
Chapter 10
Tsaki anna tayi tace ai sai ki tashi ki dauro alwala kiyi sallah nasan kin kwantane babu addua,jikin yasmin sanyaye ta sauko daga kan gadon ta shiga toilet tayi alwala sannan ta dawo ta shimfida dadduma tayi sallah raka,ah 2 tare da adduoi sannan ta koma ta kwanta zuciyarta naci gaba da bugawa saboda ta tsorata sosai,karfe 6 anna ta tashi yasmin tayi sallah bayan ta iddar da nata sallar,yasmin na iddar da sallah ta koma ta kwanta saboda jiya batayi wani bacci sosaiba,sai karfe 12 na rana yasmin ta tashi daga bacci,bathroom ta shiga tayi wanka tayi brush ta fito,lotion kadan ta shafa ba tare data saka ko powder ba ta saka wani simple gown ash colour wanda yai matukar yi mata kyau,dankwalin rigar tayiwa daurin turban sannan ta dawo gefen gado ta zauna tasan anna tana chan tana aiki a apartment dinsu first lady,tea flask ta janyo ta hada tea sannan ta koma kitchen ta bude food flask wanda anna ta saba ajiye mata abincinta a ciki,plantain ne da chips da omelette ciki,ta ci abincin sosai saboda yau ta tashi late kuma akwai yunwa a cikinta sosai,flat slippers dinta ta saka bayan tayi plugging wayanta a charge ta nufi apartment din first lady kamar yanda ta saba taya anna aiki,direct kitchen ta wuce ta samu anna tana yanka avocado zatayi avocado salad,cikin tsokana yasmin ta kalli anna tace anna ba dai har kin gama aikin nan ba?ba tare data kalli yasmin ba tace toh idan ma ban gamaba ke zan jira ki duba fa ki gani karfe 1 na rana kike fitowa nufinki jiranki zan zauna yi?dariya yasmin tayi tace anna kenan sarkin mita toh nidai kiyi hakuri don nasan yau idan kika fara mita kowa seyasan ban tashi da wuriba,,bayan ta tayata sun hada avocado salad dinne anna tace yawwa yasmin jeki palour din baqi ki gyara sannan kije bangaren rahma ki gyara don yau nayi sake aikin ya hademin dayawa,okay kawai yasmin tace ta nufi guest palour ta gyara sosai ta zuba turaren wuta a burner tare da feshe dakin da fresheners masu kamshi,apartment din rahma ta nufa bata tarar da kowa a dakin ba da alama rahma ta fita unguwane,ta fara share-share da goge-goge,tana cikin wankin toilet ne rahma ta turo kofa ta shigo tare da freinds dinta,jikin yasmin sanyaye ta fito daga toilet din bayan ta gama wankewa ta tsuguna ta gaishe dasu fadila da zahra,tunda ta fito fadila da zahra ke kallonta kamar sun samu tv,bayan ta gaishesu ne ta fice daga dakin gabanta na dukan 3-3,cikin mamaki fadila ta kalli rahma tace hey monkey kina nufin wannan itace yarinyar da kike fadamin?murmushi rahma tayi tace eh itace,ajiyar zuciya zahra tayi tace lord!!!she's damn beautiful,gyara zama fadila tayi tace yanzu kina nufin wannan yarinyar dana gani yar aikice?murmushi rahma tai tace gashinan ai kinga sheda,dariya tayi tace gaskiya i trust you kawata ba armaan ba ko baban armaan ne yaga wannan yarinyar he will definitely fall for her.....a tare suka kwashe da dariya,fadila ce ta kalli su zahra tace kuna tunanin armaan zezo gidan nan kuwa?i don't think so nima abinda nake ta tunani kenan zahra ta fada a takaice,murmushi rahma tayi tace nima nasan armaan kunyar abinda ya aikata mun bazai taba barinsa shigowa cikin gidan nanba nasan tabbas anjima zai kira yasmin yace sedai su hadu a wani wajen
Tun karfe 3 su rahma ke faman shirya yasmin saboda zuwan armaan malik,sosai suka shiryata wannan karon,skin tight blue cocktail dress tasa wanda yai matukar karbar jikinta sannan ta dora black turkish kimono,sosai yasmin tayi kyau,zahra na cikin yi mata styling na hair dinta wayanta ya fara kara,it was armaan malik suka fada a tare,jikinta sanyaye ta daga wayar bayan sun sata a hands free tace hey,shima hey din kawai yace bayan yayi shiru na 30 seconds yace you didn't send the address,da sauri ta dafe bakinta tace ohh I'm sorry,murmushi yayi kamar tana ganinsa yace it's okay say it now,ajiyar zuciya ta danyi kadan sannan tace Aso rock presidential villa,murmushi ya sakeyi yace Alright i will be there be jira ta sake maganaba ya kashe wayan
Cikin mamaki gaba daya suka kalli junansu suka ce heck!!!how dare him!!!da gaske armaan zezo cikin gidan nan?cije lip din kasa rahma tayi tace i don't think so har yanzu banyi believing armaan zai iya shigowa cikin gidannan ba da niyyar wai yazo neman wata ya mace
Yana ajiye wayar yasmin ya kira mubarak,ringing daya yayi mubarak ya dauki wayar yace asap,alluring kawai yace a takaice sannan yace inaso yanzu kaje villa ka samomin duk wani information akan yasmin hayat,okay kawai mubarak yace sannan ya kashe waya,,,,,bayan dukkanin securities sun gama bincike akan mubarak suka bashi izinin shiga gidan,cikin ladabi ya mikawa mutumin daya gani tsaye yana bawa shukoki ruwa sukai musabaha sannan suka dan matsa gefe saboda inda suke tsaye ya jike da ruwa,bayan sun sake gaisawane mubarak ya kalli mallam jauro ya mika masa rapper kudi na 50k sannan yace inaso zanyi maka wata tambayane akan iyalan gidan mr president,sosai mallam jauro yake murmushi yace karka damu yaro yi tambayarka insha Allah zan baka amsa,good mubarak ya fada a hankali sannan yace yaran mr president su nawane?dariya mallam jauro yayi yace haba yaro yar wannan tambayarce ta kawoka abinda zaka iya samun amsarta cikin jaridu da gidan radio ai kowa yasan shugaban kasa matarsa daya tilo sannan yaransa guda 2 ne kawai daga rahma sai yusuf amma shi yusuf ba a kasar nan yake zauneba yana California achan yake aiki kuma yana dadewa bezoba,a takaice dai rahma hayat ita kadaice yarinyarsa a cikin gidan nan,girgiza kai mubarak yayi yace kuma kana nufin babu wata yarinya da shugaban kasa ke riko har take amfani da sunansa?murmushi mallam jauro yayi yace gaskiya babu hasalima ma,aikatan gidan nan duk manyane babu wata yarinya sai yarinyata guda daya kuma dama na fada maka ni shukoki nake bawa ruwa a gidannan ita kuma matata yar aikice a gidan ita da yarinyar tawa duk aiki suke a gidan,da sauri mubarak ya kalli mallam jauro yace okay kenan maryam din da nake gani itace yarinyarka?girgiza kai mallam jauro yayi yace a'ah maryam ai babbar macece ita wannan yarinyace karama sunanta yasmin......bayan sunyi sallama tun kafin ya karasa gida ya kira armaan ya tabbatar masa da cewar yasmin yar aikice a gidan
Tsaye yake jikin mirror sanye da shirt sea blue da black trouser bayan yayi styling hair dinsa sosai yake shinning,ga kamshin perfume dinsa me kyau sai diamond wrist watch din dake hannunsa,mubarak ne ya turo kofa ya shiga dakin cikin mamaki yace where in the hell are you going?dariya armaan yayi yace gurin yasmin mana,tsaki mubarak yayi yace wait wai kai duk abinda na fada maka beyi makaba kenan me zakayi da yar aiki kuma armaan?me zakayi da yarinya makaryaciya wacce bata ji kunyar idonka ba tace maka ita yar shugaban kasace?karka manta kaje ka yaudari rahma yar shugaban kasa ranar bikinku kace ka fasa kuma yanzu kana nufin zakaje kace kanason yar aiki a cikin gidan tayaya hakan zai yiwu?me zakaci da yarinya yar aiki kuma makaryaciya?shiru armaan yayi kadan tare da lumshe idonsa yace I'm in love with her seriously,and i love her the way she is.....
Thank you for reading my story!!!
Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro