Chào các bạn! Vì nhiều lý do từ nay Truyen2U chính thức đổi tên là Truyen247.Pro. Mong các bạn tiếp tục ủng hộ truy cập tên miền mới này nhé! Mãi yêu... ♥

9.








NUWAMBA, 2006.



Maryam ta gama haɗa kan kayanta, daga katifa, risho, bokiti zuwa kayan provision. Ranar tafiya kawai take jira ta iso. Ita abun har mamaki yake bata wai zata tafi jami'a.

Wayaga 'yar mitsilar Abba a jami'a.

A shekara sha shida mutane da yawa na gani tayi ƙarama ta tafi jami'a. Ciki kuwa harda Ummanta. Tunda aka fara zancen WAEC da JAMB hankalin Umma ya tashi. Ita a ganinta Maryam bata yi hankalin da zata turata makaranta wani gari ba, ko cikin garin ma hankalinta bai kwanta ba. Dama a ce tana da girman jiki ne da da sauƙi. To Maryam ɗin ce gata nan ga yanda ta ke. Ƙannenta duk sun fita girma ko Zee sai ka ce ta bata shekara ɗaya zuwa biyu.

"Anya Maryam baza ki bari sai wata shekara ki tafi ba?" Umma ta ce tana kallon akwatin da Maryam ta gama rufewa da taimakon Safiya.

Allah Ya so Baba Malam na wurin. "Wace irin magana ce Sa'adatu? Akan me za'a bari sai wata shekara bayan yarinya ta samu admission. Kina da tabbacin zata samu admission din wata shekaran ko kuma ma cin JAMB din."

Umma ta rausaya kai tana marairaice fuska. "Wai gani na yi ta yi ƙarama Baba, ni dai tsoro nake ji wallahi."

Mama ta girgiza kai. "Duka da me kika fita lokacin da kika tafi makaranta?"

"Dukda haka Mama, zamani ya chanza. Kuma ni ai day na yi, ita kuwa Zaria fa zata tafi."

"Addu'a kawai za ki yi mata. Muma haka muka ji da muka tura ki makaranta. Amma maganar a bari sai wata shekara bai taso ba."

"To Baba, Allah Ya tabbatar mana da alkhairi." Umma ta ce tana sakin ajiyar zuciya. "Kin gama haɗa kan komai de ko?"

Maryam ta gyada kai. "Eh Umma. Saura hijaban da aka bada ɗinki kawai."

"Ya kamata ki je shagon telan ai kar ya kasa cika miki alƙawari." In ji Mama.  "Anjima Firdausi sai ta raka ki kafin ta tafi gidanta."

"To Mama."

Akwatin ta ja ta kai ɗaki ta kai shi idan kayan ke ajiye. Sauran kayayyakin da ta baza a kan gado ta linke ta mayar da su cikin wardrobe. Anti Firdausi ta shigo ɗakin dauke da danta Hamza mai shekara uku.

"Yaya Maryam 'yan jami'a, ana ta shiri."

Maryam ta yi dariya ta miƙa hannu zata karɓa Hamza ya noƙe kafaɗa. "Sarkin kyuya, sai ka yi ta yi ai. Kuma Nawal zata zo babu ruwana da kai."

Nawal ɗiyar Anti Jamila ce. Ita tana Bauchi da zama. Tare aka yi bikin su ita da Anti Firdausi kuma dukan su sun gama school of nursing yanzu haka aiki su ke yi a asibitocin gwamnati.

Umma ma shekara uku kenan da samun aikinta a Nursing Home da ke nan Kaduna.

Zee ta shigo ɗakin da niyar daukan jaka tana ganin drawer din Maryam a buɗe ta yi wurin. Kafin ta ciro rigar da ta daɗe tana hari Maryam ta yi saurin tare ta.

"Kai Yaya, ke da kika siya sababbi da yawa, dan Allah ki bar mun wannan mana. Ke baki so in riƙa tunawa da ke idan kin tafi."

"Sai na bar miki riga za ki riƙa tunawa da ni Zee?" Maryam ta yi dariya.

"Dan Allah Yaya ki bar mun."

Maryam ta girgiza kai. Idan Zee ta fara nacin abu kaman tsohuwar mayya. Rigar ma fa tsawon ya yi mata kaɗan. Rigar ta ciro ta wurga mata, daidai shigowar Safiya.

"Wallahi nima sai an bani. Kai Yaya Maryam tun yaushe na ke cewa ki bani rigar nima."

Anti Firdausi ta dago kai daga inda ta ke ƙoƙarin kwantar da Hamza. "Sai kun ƙarar mata da kaya wai. Ita da zata tafi makaranta ai tafi ku buƙata."

"Kai Maman Hamza, ki bari nima a bani." Safiya ta ce, drawer din ta isa ta ciro wata baƙar riga mai adon ja. "Ni ga wanda nake so. Yaya in ɗauka?"

"Ɗauka."

Ihu ta yi ta rungumeta. "Nagode yayarmu. Allah Ya bar mana ke."

Sallamar ƙawarta Hamida ya katse Maryam. Ta kulle drawer dinta ta ce kuma kar taga hannu kowa a ciki sannan ta fita. Umma kaɗai ta rage a falon, ta samu Hamida na gaisheta.

Umma ta amsa ta tambayeta yaya ʼyan gidan. "Na yi waya da Maman ku ɗazu ma ai. Ke kin gama shirin ko."

"A'a Umma da saura."

"Gwara dai a gama lokaci nata wucewa." Umma ta miƙe ta shiga ɗaki ta bar su a falo.

"Maryamah," Hamida ta ce cike da zolaya.

Nan da nan kuwa Maryam ta ɓata rai. "Ki kiyaye ni Hamidatu."

Hamida ta yi dariya. "Hamidatu dai ba suna bane. Amma Maryamah kuwa kowa ya sani suna ne me zamab kan shi."

Maryam ta girgiza kai tana dariya. Kitchen ta tafi ta daukowa Hamida ruwa tare da meatpie din ta yi jiya.

Hamida na gani ta miƙa hannu ta ɗauke plate ɗin meatpie ɗin kafin ma Maryam ta ajiye tray ɗin. "Kin yi meatpie din kenan, shine ba ki aiko mun nawa ba ko?" A hankali ta gutsiri meatpie din tana lumshe ido. "Kai Maryam!"

Maryam ta yi murmushi tana jin ɗaɗin santin da Hamida ke yi. "Ya yi daɗi?"

"Har sai kin tambaya? Gaskiya ki ƙaro mun dan wannan ya yi mun kaɗan."

Tun kafin su fara WAEC Maryam ta ke roƙon Umma ta saka ta makarantan koyan girki. Umma ta ce sai ta fito da sakamako mai kyau tukunnan. Ranan da zata duba WAEC dinta zuciyarta kaman zata tsaga ƙirjinta ta fito.

Result din ya yi kyau har ya wuce tsammani. Ta samu A1 a subjects huɗu, B2 a subjects biyu sai C4 a sauran ukun. Ita kanta bata taɓa tunanin zata fito da result haka mai kyau ba.

Ta ko sha kyauta a makaranta da gida. Mama ta bata leshi mai ɗan karan kyau. Baba Malam ya siyan mata waya ya ce tunda makaranta zata tafi tana buƙata. Anti Jamila da Anti Firdausi ma sun haɗo mata kayan kyale-kyale na 'yan mata. Umma kuma ta biya mata kuɗin makarantan koyan girki kaman yanda ta yi mata alƙawari.

Ta je makarantan na tsawon sati shida. Ta koyi girke-girke kala daban daban. Continental da intercontinental dishes, da kuma local dishes na gida Najeriya. Sannan ga pasteries da snacks da kuma drinks.

Ko mai aka koya musu a ranan idan ta dawo gida sai ta gwada. Wasu su yi daɗi wasu kam ba su ciwuwa. Yanzu haka dai ta fi kwarewa a harkar murza flour musamman ma dai meatpie da doughnut. Shi yasa yanzu ba zaka taɓa zuwa gidan ba ka same su ajiye ba. Da ya ƙare Baba Malam da kan shi yake cewa a sake yi.

Bayan Hamida ta gama santin meatpie din ta ce Maryam ta tashi su je kasuwa.

"Me za ki siya?"

"Kayan kwalliya zan siya kin san zamu tafi ABU Zaria."

Maryam ta tuntsire da dariya tana kallon ƙawarta dake fari da idanu. "Eh lallai yan jami'a, gaskiya ne. Bari in faɗawa Umma."

"Kar dai ku daɗe," abunda Umma ta ce mata kenan.

Maryam ta sanyo hijabinta su ka tafi. A hanya sunata hira abun su. A shekarun da su ka wuce Hamida da Maryam sun zama tamkar 'yan biyu. Baka taɓa ganin ɗaya baka ga ɗayar ba. Malamai a makaranta an san su, idan ɗaya bata zo ba an riƙa tambayan ɗayar ina yan biyun ki.

Sannan zumuncin da iyayen su mata ke yi shi ya sake haɗa kan su. Baban Hamida da kan shi ya samo musu admission a ABU, duk da basu samu course din da su ka yi applying ba. Pharmacy su ka yi applying Hamida ta samu Chemistry Maryam kuma Biochemistry.

Ƙasar ce ta kamo ƙasar wa ya sanka wa ka sani, sai masu uwa a bakin murhu ne su ke samu course ɗin da su ka yi applying. A Najeriya inda ka ce lallai sai abun kake nema zaka karanta to kana tare da wahala. Shi yasa Baban Hamida ya ce kar su wani tsaya jiran Pharmacy, su karɓa wannan ɗin su fara. Albarka ake nema dan haka su yi addu'a Allah Ya sa hakan shi ne mafi alkhairi.

Sun isa kasuwar da ke nan kusa da su. Dayake ranan assabar ta ke ci, kasuwar cike take maƙil da mutane. Maryam dai ita ʼyar kallo ce, duk inda Hamida ta saka ƙafa itama nan ta ke sakawa.

Masu kaya sun baje kolin su sai siye da sayarwa ake yi. Hamida ta gama kwashen tarkacenta ta je su tafi.

"Ke baza ki siya komai ba?"

Kai Maryam ta girgiza. Su Anti Firdausi duk sun siyan mata wannan abubuwan dan haka bata da buƙatar su. Wata sarƙan beads dai ta gani da ta bata sha'awa amma bata so ta siya Umma ta yi faɗa.

"Anti Nafisa nata bani tsoron zaman hostel." In ji Hamida. "Wai ba'a sanya idan ba haka ba ʼyan ɗaki raina ka zasu yi su mayar da kai shashasha. Tana faɗa mun na ce dole in faɗa miki dan ke ce shugaban masu haƙurin duniya, duk abunda aka miki sai ki kyale. To dai jami'a ba secondary school bane, babu wanda zai kwatar miki hakƙinki. Saboda haka idan an yi miki abu ki buɗe baki rama."

Maryam ta yi dariya tana sauraronta.

Maryam da Hamida ko ta ina sun sha banban. Fatar Maryam nada duhu, Hamida fara ce. Maryam bata da tsawo, Hamida doguwa ce. Haka Maryam nada haƙuri da dauke kai Hamida kuwa sai inda ƙarfinta ya ƙare. A makaranta inda aka toni Maryam faɗa Hamida ke shigan mata.

"Kina dariya. Ba abun dariya bane. Wallahi Maryam kar mu je ki riƙa bari roomates na raina miki wayo."

"To Anti Hamida."

Hamida ta galla mata harara. "Allah sa ma dai mu samu ɗaki ɗaya kawai. Saboda na san babu wani abun arziƙi da za ki iya tabukawa."

"Ai ina da ke Hamidatu ba sai na yi komai ba."

"Ko? Za ki gane," Hamida ta gyada kai.

Maryam Allah Ya yi ta ba mai son hayaniya ba. Duk abunda zai kawo tashin hankali tana gudun shi. Wani lokaci dan a zauna lafiya ko ita ke da gaskiya sai ta kyale. Hakan ba ƙaramin ba Hamida haushi ya ke yi ba.

Hamida 'yan 'do me I do you' ne. Bata bari ta kwana sam.

A hanya su ka rabu. Hamida ta yi hanyar gida ita kuma Maryam ta nufa shagon tela ta karɓo dinkin hijabai. Ta iske baya nan.

Ta isa gida taga motar Baba Zubairu pake a kusa da motar Baba Malam. Murmushi ya mamaye fuskarta.

A shekarun da suka wuce bayan rasuwan Abba daidai da rana ɗaya Baba Zubairu bai taɓa mantawa da su ba. Saboda yanayin aikin shi bai cika zuwa ba musamman da ya aka yi mai transfer zuwa ƙasar yarbawa amma ko da yaushe aiken shi na kan hanya.
Da waya ta yawaita kuwa a wata ya kan kira sau biyu zuwa uku.

Kullum Maryam ta gan shi tunani ɗaya ke zuwa mata rai. Da Abbanta na raye da shima ya yi kaza, ko ya yi kaza. Musamman da taga Baba Zubairu da furfura. Da Abbanta na da rai da shima furfuran girma ta fara fito mai.

Falon Baba Malam ta nufa dan ta san nan Baba Zubairu ya ke. Ta same shi suna hira da Baba Malam.

Yana ganinta murmushin fuskar shi ya faɗaɗa. Da hannu ya yi mata alama da ta matso kusa da shi. "Yaya Maryam ce haka? Masha Allah."

"Ina wuni Baba," ta gaishe shi cike da ladabi da biyayya.

"Lafiya lau mutanen ABU. Kin shirya tafiya ko?" Maryam ta gyda kai tana jin yunwa. "Kin san ni da Abban ki nan mu ka je."

Maryam ta dago kai ta kalle shi tana murmushi. "Na sani Baba." Yana ɗaya daga cikin dalilan da take son makarantan.

Da dama Abba yana bata labarin yanda su ka yi karatu cikin gata. Ya ce har wanki ake yi musu a basu abinci da kuma kudin allowance. Dukda yanzu abubuwa sun lalace ba haka makarantan ta ke ba amma tana sha'awar ta yi karatu a jami'ar da Abbanta ya yi karatu.

Ba ta daɗe a falon Baba Malam ba ta koma sashen su. Su Safiya sun tafi islamiya shi yasa wurin ya yi shiru.

"Kai me kake yi baka je islamiya ba?" Maryam ta tambaya Idris da ke zaune a falon yana game a wayar Umma. Ta tabbata Umma bata san ya dauko mata waya ba.

"Na je, koroni aka yi na yi latti."

"Ya yi maka kyau." Ta cire hijabi ta zauna. "Ina Anti Firdausi?"

"Baban Hamza ya zo sun tafi."

"Kaiii, ba mu yi sallama ba. Ka je ka gaida Baba Zubairu?"

Kai ya gyada. "Da chan na ke ma."

Ɗaki ta shiga inda ta samu an yi kachacha da shi. Kai ta girgiza ta hau kimtsa wurin. Daga Safiya har Zee babu wanda zai iya sa hannu ya gyara ɗaki. Kwafa ta yi, zata tafi makaranta ai, zata ga wa zai riƙa gyara musu ɗakin.

Tsaff ta gyara wurin ta haye gado. Chan kaman an tsunguleta ta miƙe ta shiga ɗan ƙaramin kicin ɗin dake nan bangaren su. Meatpie ɗin da ta yi ta daura kan plate tare da zobo da shima ita ta haɗa. Ta maida hijabinta ta taka zuwa falon Baba Malam.

"Sannu Yaya," inji Baba Zubairu.

Maryam ta yi dariya. Yaya dai da Abba ke kiranta ya bita. Allah Ya so ta ba ɗayan sunan bane.

"Ko 'yar mitsila zan ce?"

Maryam ta zaro ido. Kaman ya san me ta ke tunani. Da sauri ta girgiza kai. "A'a Baba."

Bismillah ya yi ya ci meatpie ɗin. A hankali ya riƙa jinjina kai. "Wannan duk a cooking school din kika koya?" Ta gyada mai kai. "Masha Allah. Ya yi daɗi sosai. Sauran mu resturant ko?"

Murmushinta har kunne. "In sha Allah."

"Toh Allah Ya taimaka."

Ɗaki ta koma ta haye kan gado ta ɗauko wayarta tana latsawa. Ta yi shekara biyu da yin sauka shi yasa ita bata je islamiyar ba. Tana cikin latsa waya bata san lokacin da barci ya dauketa sai ji ta yi ana daddabata ta tashi. Cikin magagin barci ta buɗe ido taga Umma a samanta tana ce mata ta tashi.

"Tashi Baban ku zai tafi."

Bayi ta shiga ta wanke fuska ta zumbula hijabi ta yo waje. Ashe ta daɗe tana barcin, garin har ya yi duhu ga 'yan islamiya nan sun dawo. Zee na kusa da Baba Zubairu ta cika shi da surutu.

"To shikenan Zainab. Ina zuwa gida zan aiko miki."

Nan su ka yi wa Baba Zubairu sallama. Tabbas ya riƙe zumunci da har zuwa lokacin nan bai yarda su ba.

Wata envelope ya miƙawa Maryam. "Gashinan ki ƙara kudin makaranta. A maida hankali kin ji, Allah Ya bada sa'a."

"Baba da ka bar shi...." Maryam ta fara cewa ya katse ta.

"Da Abbanki ya baki za ki ƙi karɓa?" Kai ta girgiza, idonta na zafi. Baba Zubairu ya yi murmushi. "Karɓa Maryam kin ji. Allah Ya bada sa'a."

"Ameen Baba nagode," ta ce wani abu na tokare mata wuya. "Allah Ya saka da alkhairi."

Ya yi mata murmushi sannan ya gaisa da Idris da Bashir. Har saida motar shi ta ɓace kafin su shiga ciki.

Maryam ta nufa falon Mama inda Umma ta ke ta miƙa mata envelope ɗin. Kuɗi ne a ciki 'yan dubu dubu. Umma ta jinjina kai ta miƙawa Mama.

"Allah Ubangiji Ya sakawa bawan Allahn nan da alkhairi. Hakiƙa shi ɗin mai riƙe zumunci ne. Allah Ya haɗa fuskar shi da aminin shi a aljannah. Maryam ku riƙe zumunci. Kina ganin dai yanda bawan Allahn nan ke dawainiya da ku. Wanda ya fito ciki ɗaya da mahaifin ku be yi muku haka ba. Dan haka kar ku sake ku zama masu manta alkhairi. Yanzu kin girma kin yi hankali, idan an kwana biyu ki dauka waya ki kira ki gaida shi. Ba sai an ce miki ba."

"In sha Allah Mama."

"Allah Ya yi muku albarka."

"Ameen Mama."

A nan falo ta barsu Mama nata jinjina kirki da zumunci irin na Baba Zubairu. "Bawan Allah. Shi kuma tashi ƙaddaran kenan, Allah bai ba shi haihuwa ba."

Umma ta gyada kai. Kusan tare aka yu bikin su da na Zubairu. Tunda matar shi ta farko ta yi ɓari sau biyu farkon farkon auren, shikenan har yau ko batan wata bata sake ba. An je asibitin har an gaji. Kuma Allah Ya yi shi da son yara sosai. Tun marigayi na da rai bai taɓa zuwa gidan hannu biyu ba kullum sai ya riƙo musu wani abu.

Ko bayan dawowar su Kaduna ma ba'a wata be yi musu aike ba. Da so ya yi ya ɗauke dawainiyar yaran gaba ɗaya. Umma ta ƙiya kar abun ya yi yawa kuma.

Shaguna da ta bari a hannun shi nata bunƙasa. Tunda daɗewa aka yi expanding shagunan. Yanzu haka ma shirin siyan wasu shaguna da ke kusa da su ake yi dan a ƙara faɗin wurin.

Babu fashi duk wata sai ta ji alert na riba da aka samu sannan ya turo mata breakdown din komai. Umma ta sha faɗa mai ba sai ya turo breakdown ɗin ba amma ya ƙiya a cewar shi saboda a samu transparency da trust a tsakanin su.

Ita da yaranta kam ba su da abun cewa Zubairu sai godiya da fatan Allah Ya saka mai da alkhairi.








Ƙarfe ɗaya da minti talatin na dare. Gaskiya ina son ku🤭 dan haka a dage a yi voting. Amma fa ban ce a yi voting kaɗai ba a yi gaba. Comment pleaseee🥹

Toh jama'a ya muke ji game da littafin nan? Yay 👍🏼 or nay👎🏽


~Maymunatu Bukar💕 (saboda sabo Maryam na fara typing😂)

Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro