Chào các bạn! Vì nhiều lý do từ nay Truyen2U chính thức đổi tên là Truyen247.Pro. Mong các bạn tiếp tục ủng hộ truy cập tên miền mới này nhé! Mãi yêu... ♥

7.












Umma ta sanar da ASP Zubairu yanda su ka yi da Baba Malam. Ya ce In sha Allah zai tabbatar an yi komai yanda ya dace. Sannan ya tura a sanar da Musa tunda haƙƙinsa ne ya sani.

Musa sam bai ji daɗin faruwar hakan ba. Amma babu yanda ya iya. Dan shi kam duk abunda aka haɗa da hukuma yana ja da baya. Sannan ya san halin Zubairu sarai ba zai raga mai ba idan ya yi ba daidai ba. Zai saurara ya ga yanda abun zai kasance daga baya sai ya san yanda ze yi.

Ana cikin haka Inna ta kwanta rashin lafiya ya kai har saida aka kwantar da ita a asibiti. Ɗiyar Musa ta zauna da ita. Kwananta biyu aka sallameta. Musa ya kafe akan lallai sai ta koma gidan shi wai rashin kula ne ya sa ciwon ya yi tsanani haka.

Inna ta wanke shi tas ta ce kuma gidan Sa'adah zata koma. Musa ba dan yaso ba Inna ta koma.

Sai dai kwananta biyar da dawowa daga asibiti rai ya yi halinsa, ta rasu cikin barci.

An kwana da ita ba'a wayi gari da ita ba.

Inna Lillahi Wa Inna Ilahi Raji'un!

Wata uku cif tsakanin Inna da ɗanta Ahmad.

Umma ta sake shiga cikin tashin hankali ta zama abun tausayi. Mutuwar Inna ta dawo mata da mutuwar Ahmad sabuwa fil. Haka take kwana ta wuni tana kuka har sai hawayen sun ƙafe. Wancan karan Inna ke bata ƙarfin gwiwa yanzu Innar babu ita, itama ta tafi ta barta. Babu mai rarrashinta.

Umma ta koma tamkar wata zombie. Ta rame ta yi haske alamun babu isasshen jini tare da ita, idawunta duk sun faɗa.  Duk wanda ya ganta dole ya tausaya mata. Yaran suma sun yi jungum jungum.

A watanni uku sun rasa mutane biyu masu muhimmanci a rayuwarsu.

Umma har saida ta kwanta ciwo dalilin jininta da ya hau ba kaɗan ba. Wannan karan Jamila bata koma da Mama ba, dan abun ze yi wa Firdausi yawa. Itama mutuwar ta girgizata sosai domin ita ce ta fara ganin gawar Inna. Da yake tare suke kwana a ɗakin Innar.

A haka har Umma ta fita takaba. Ta cigaba da rayuwa ne ba dan tana jin daɗinta ba. A lokuta da dama idan ta ji inama a ce itama mutuwa zata ɗauketa sai ta tuna da marayun da suka dogara da ita.

Don su take koƙartawa taga komai ya daidaita. Ita suke kallo, daga wurinta su ke saka ran samun ƙarfin gwiwa. Sai dai basu san ba zata iya ba. Mai bata ƙarfin gwiwar ya tafi ya barta. Ahmad ya tafi ya barta ita kaɗai.

Umma ta sa hannu ta dafe ƙirjinta inda take jin zuciyarta na sake karyewa. Ta tawarwatse gaba ɗaya bata san ta inda zata fara gyarata ba. Ta ina zata fara? Ba zata iya ba. Ahmad ya tafi ya barta. Inna ma ta tafi ta barta.

Inna Lillahi Wa Inna Ilahi Raji'un!

Hasbunallahu Wa Ni'imal Wakil!

Da kyar Umma ta samu ta saita kanta. Tana cikin goge hawayenta Firdausi ta shigo da sauri. Umma ta kalleta ganin yanda bata cikin natsuwarta.

"Lafiya Firdausi?"

"Umma dama Baba Musa ne ya zo neman ki."

Musa? Umma ta ce a zuciya da mamaki. Me ya zo yi? "Gani nan zuwa." Bayi ta shiga ta wanke fuska sannan ta saka hijabi ta fita.

Musa na zaune hakimce a falo kai ka ce gidansa ne. Ko gaisuwar Umma bai amsa ba. "Kinga Sa'adatu ba abunda ya kawo ni ba kenan. Ki sanar da Zubairu azo a raba gadon nan tun kafin ran kowa ya baci. Wannan wani irin abu ne? Idan banda ma kin raina mun wayo me ye na wani sako Zubairu cikin zancen raba gado shi da bai da hurumi cikin lamarin. Tun wuri ki yi gaggawar sanar da shi kafin in dau mummunan mataki a kan ki wallahi."

Kullum idan Umma ta yi tunanin ta gama fahimtar waye Musa sai ya nuna mata ba haka ya ke ba, ya fi yanda take zato.

Wai har ya manta ya ke nufi ko kuwa son abun duniya ne ya rufe mai ido?

Watan Inna biyu da rasuwa wanda ke nufin watan Ahmad biyar kenan. Nan da Inna ta rasu ya ruƙa rusa kuka yana ya shiga uku gatan shi ya ƙare a duniya amma gashi zaune ko wata uku ba'ayi ba yana wani zance daban.

"Kai yanzu rabon gado ne a gaban ka Musa? Ka yi musu adalci kenan? Kaman jira kake yi a ce babu su." Umma ta ce ranta na ƙuna.

"Kin ga kada ki faɗa mun maganan banza kin ji ko. Laifi ne dan na ce a raba gado a bani kasona, naga dai haƙƙina ne ba na wani ba. Ke har kin isa ki ce mun jira na ke yi, to idan ma jiran na ke yi sai me? Na ce sai me? Akwai wani abu da za ki iya yi ne? Ni dai na faɗa miki ku yi gaggawan bani kaso na kafin ran kowa ya ɓaci. Kina wani maganan banza, mutumin da ya mutu ba ya mutu ba. Akwai wani abun yi ne? Tunda ke kin fini son su sai ki dawo da su ai. Aikin banza aikin wofi."

Allah sarki rayuwa. Yau a rashin Ahmad har Musa ya samu daman shigowa har cikin gidanta ya yi mata rashin mutunci har haka. Wayyo.

Saƙon Musa ya isa ASP Zubairu. Ka haifi ɗa ne baka haifi halinsa ba. Waye zai ce Arc. da Musa ciki ɗaya su ka fito? Ko ta ina sun sha banban. Idan Musa ya yi wani abun rasa abun cewa ASP ya ke yi. Sam bai taɓa zaton abun Musa har ya kai haka ba. Amma fa duk abunda ya ke yi har yau bai taɓa tunkarar ASP ɗin kai tsaye ba sai dai ya je ya yi zubawa Sa'adatu ruwan rashin mutunci.

Kotun muslunci ASP Zubairu ya je aka haɗa shi da ɗaya daga cikin alƙalan ya yi rabon gadon. Tun zaman farko Musa ya fara baɗa matsala. Shi a dole sai duka shaguna biyu da ke Kwari sun zama cikin kason Inna da zai gada tunda shi kaɗai ne ɗanta da ke raye. ASP ya sanar da shi babban shagon baya cikin dukiyar gado saboda kafin marigayi ya rasu ya mallakawa matarsa shagon dan haka nata ne halak malak.

In hankalin Musa ya yi dubu ya tashi dan ya gama sa rai shagunan biyu zasu dawo hannunsa. Daga nan ya tayar da rigima akan dole shagon da ya rage ya kasance cikin kason Inna da zai gada. Alƙali ya sanar da shi babu abunda za'a chanza tunda an yi rabo kaman yanda musulunci ya tsara shago ya faɗa kason Zee da Idris  kuma babu mai chanza hakan.

Da yaga haka ba zai samo mai maslahan da ya ke nema ba sai ya koma wurim Sa'adatu yana matsa mata. Babu irin rashin mutuncin da Musa be yi mata ba akan maganan gadon kaman ita ta raba.

Duk wannan hayagaga da Musa ke yi bai sa an fasa rabon gadon ba. Aka raba na kowa aka ɗamka mai. Umma aka bata nata da na yaran. Nan ma fa Musa wai bai yarda ba. A dole sai shi za'a ba na yaran ya riƙe a hannusa.

Hakan ba ƙaramin ƙullar da Umma ta yi ba. Wato Musa babu kunya babu tsoron Allah a fili ya ke bayyana manufarsa na cinye dukiyar marayu.

Mutane na da abun tsoro. Da hannunka ka riƙa cin wutan jahannama. Amma duka basu damu ba gani suke yi kaman ƙarya ne. Gani suke yi kaman idan sun ci sun ci bulus ne. Sun manta cin dukiyar marayu na ɗaya daga cikin manyan zunubai sannan Allah SWT Ya ce duk wanda ya ci dukiyar maraya wuta kawai ya ke zubawa cikinsa sannan zasu shiga cikin wata wuta mai tsanani.

Amma mutane son abun duniya ya sa sun manta da wannan. Kawai su mallaki dukiya ko ta wani hali shine babban burinsu.

Umma ta ce ko bai isa ba. Da kanta ta samu alƙalin ta yi mai bayani tunda a shari'ance Musa ya fi chanchanta a ba kason yaran a matsayinsa na ƙanin ubansu amma tunda ba shi da amana sai aka ɗamka mata na yaran.

Rashin mutunci Musa na yau daban na gobe daban. Dole ASP Zubairu ya taka mai burki.

Da ransa ASP Zubairu ya yiwa kansa alƙawari ba zai bari wani ya cutar da iyalan Ahmad ba ko da kuwa mutumin ɗan uwansa ne. Saboda Ahmad ya wuce amini a wurinsa ya zama ɗan uwa. Da ana zaɓen ɗan uwa ai da Ahmad ba zai zaɓa Musa ba. Musan da ya kamata ya zama gatan marayun da Ahmad ya tafi ya bari shine ke neman jefa su wani hali.

Mutum da ɗan uwanshi amma hassada da son abun duniya sun rufe mai ido da kunnuwa bai ji bai gani.

Wannan ne yasa Umma ta samu sauƙin fitinar Musa. Ta koma aiki dukda ba daɗin shi ta ke ji ba. Kullum ta fita hankalinta ba a kwance ba musamman idan tana night duty.

Wata rana ta dawo daga aiki da mislin ƙarfe ɗaya na rana ta samu an balle kofar gidan. Faɗan irin tashin hankalin da ta shiga ba zai misaltu ba. Barayin ba su iya balle ƙofar falon ba amma ƙofar kicin sun cireta daga jikin gini sun ajiyeta gefe. Rabin kayan abincin da ke kicin ɗin an kwashe. Gas cooker kuma an fara janyota amma ba su iya fita da ita ba dan gata nan a tsakar kicin ɗin. Cylinder ɗin gas kuwa gudu uku duka an ɗauke su. Jamila da Firdausi sun je kasuwa suma dawowa su ka yi su ka samu Umma cikin tashin hankali.

Ranan Umma bata iya runtsawa ba. Kwana ta yi cike da tsoro da fargaba. Washegari 'yan unguwa babu wanda yaga lokacin da abun ya faru.

Haka suka cigaba da zama cikin fargaba sai dai daga ranan hakan bai sake faruwa ba.

Umma ta yi ƙoƙarin ganin ta cigaba da tafiyar da rayuwarta da na 'ya'yanta daidai gwargwado. Sai dai abun yana nema ya gagareta. Tafiyar da gida ba ƙaramin abu bane ba, ba ka taɓa sanin wahalar abu sai ka yi da kan ka. Danma Allah Ya taimaketa ƙannenta na nan suna taimaka mata. Sai dai idan su ka tafi bata san ya zata yi ba.

Idan an kwana biyu ASP Zubairu na leƙowa ya duba lafiyarsu. Abokanan Ahmad su kan leƙosu a kai a kai sai dai hakan bai dore ba na kwana biyu ne kawai. Ya zamana idan ba ASP ba babu wani kuma da ke zuwa duba su.

Ya rage daga Sa'adatu sai marayunta suka cigaba da rayuwarsu cike da kewar jigonsu da ya yi musu nisa. Tsakanin su da shi sai addu'a sai kuma tuna dumbun memories ɗin da ya tafi ya bari.




***

Dawowar Umma daga asibiti kenan a matuƙar gajiye. Jamila da Firdausi ta samu a tsakar gida suna hira. Suna ganinta su ka fara mata sannu da zuwa Jamila ta karɓa jakarta.

"Sannu da zuwa Umma," inji Firdausi. "Bari in kawo miki abinci."

Umma ta girgiza kai tana daga mata hannu. "Bar abincin nan Firdaus. Idan akwai ruwan zafi dai ki kawo mun in sha shayi."

Abinci yanzu bai dameta ba. Dan ba zata iya zama da yunwa ba shi yasa ma take ci amma ba dan tana marmari ba ko tana jin daɗin ɗanɗanon ba.

Firdausi ta kawo mata flask ɗin ruwan zafi da kayan shayi da kuma kofi. Umma ta yi mata godiya.

Zaman ƙannenta a nan ya gyara alaƙar su sosai duk da dama chan ba wai ɓaci ta yi ba. Akwai tazarar shekaru tsakanin su wanda ya sanya babu sabo chan tsakanin su. Jamila na da shekaru ashirin, Firdausi kuma na da sha takwas. Allah Ya yi wa mahaifiyarsu rasuwa tun suna yara, Jamila na da shekara huɗu ta rasu. Mama mahaifiyar Umma ita ta riƙe su. Idan ba an faɗa ma ba ko ka sani ba za ka taɓa cewa 'ya'yan kishiya ne Mama ke riƙo ba. Dan ita ba haka ta ɗauke su ba. Matsayin su ɗaya da tilon 'yar ta Sa'adatu.

Baba Malam ya auri Gwaggo mahaifiyar su Firdausi a lokacin Sa'adatu nada shekara sha biyar. Sai Gwaggo ta zama tamkar yayarta. Yanda su ke zaune ba zaka taɓa cewa matar mahaifinta ce ba.

Sun zauna cikin kwanciyan hankali har Allah Ya karɓa ran Gwaggo. Jamila da Firdausi su ka koma hannun Mama. 'Yan uwan Gwaggo sun zo a basu yaran Baba Malam ya hana. Amma suna zuwa wurin danginta a kai a kai.

Yanzu Jamila da Firdausi sun yi jarabawar school of nursing amma basu samu ba. Umma ta ce musu ko poly ne su fara amma sun nuna sun fi son nursing ɗin.

"Umma kayan miya sun ƙare," cewar Jamila tana zama kan kujera.

Umma ta gyada mata kai. "Anjima sai ku siyo. Akwai wani abu da ya kare ko ya kusan ƙarewa?"

Jamila ta girgiza kai. Umma ta saki ajiyar zuciya. Gabanta har faɗuwa ya ke yi idan aka ce babu wani abu a gidan. Ɗaki ta shiga ta duba yawan kuɗin da ta ke da shi a hannu.

A lokaci irin haka kewar Ahmad ɗinta ke mamayeta. Da bata san duka wannan lissafin ba sai dai ta faɗa abunda ta ke buƙata washegari a kawo mata fiye da yanda ta ce ma.

Ajiyar zuciya ta saki tana yi mai addu'a a zuciya. A kwana a tashi har ya yi wata da watanni da barin duniya amma kullum ji ta ke yi kaman yau ya tafi ya barta.

Mutane da yawa na ce mata zata saba. Jin su kawai ta ke yi. Ta yaya zuciyarta za ta saba rayuwa ba tare da masoyinta ba? Abun kaman da wuya.

Kuɗin ta cire daidai yanda zai isa ta ba su Jamila su siyo abunda ake buƙata. Dayake su ma yanzu sun zama ʼyan gari. Umma har bata son tunawa za su tafi. Dan da su a gidan shi yasa abubuwa basu chaɓe mata ba. Idan su ka tafi bata san ta inda zata fara ba.

Bayan Jamila da Firdausi sun fita sai gidan ya yi shiru. A lokuta irin haka ne Umma Sa'adatu ke jin matsananciyar kewar sahibinta Ahmad.

"Allah Ya yi maka rahama Ahmad ɗina. Allah Ya haɗa fuskokin mu a aljannatul firdaus."

Takardu ta fito ta yi aiki domin ta dauke hankalinta daga tunanin da ta faɗa. Ta yi nisa a aikinta yaran su ka yi sallama sun dawo daga makaranta. Bashir ya rugo da gudu ya ɗane kanta.

Umma na dariya ta ce ya dagata kar ya karya mata cinya sannan ta amsa gaisuwar sauran. Kaman yanda su ka saba kowannen su ya je ya chanza kaya. Kasancewa alhamis ce babu islamiya sai su ka saka kayan gida.

Maryam ta zubo musu abinci a plate ɗaya su duka.

Babu daɗewa Firdausi da Jamila suma su ka dawo su ka yada zango a tsakar gidan.

Haka rayuwa ta cigaba da tafiya a wannan gidan, yau daɗi gobe babu. Umma Sa'adatu ta tsaya tsayin daka sannan ta dage dan ganin ta tafiyar da rayuwarta da na yaranta akan turba mai kyau.

Umma ta roki iyayenta alfarma da a bar mata Firdausi a wurinta ko ba komai zata debe mata kewa sannan duba da yanayin aikinta dole ta samu wanda zai riƙa zama da yaran idan tana night duty.

Baba Malam ya yi shawara da Mama kafin ya amince. Umma ta ji daɗin wannan karamci da iyayenta su ka yi mata. Jamila kaɗai ta koma Kaduna itama tana ji inama ta zauna sai dai babu yanda za'a yi a bar su Mama su kadai.

Firdausi yanzu ta zama ʼyar gida. Yaran suma suna jin daɗin zamanta a gidan.

Wata rana Umma ta tafi asibiti night Firdausi da yaran na zaune a falo suna kallo su ka ji kaman an taɓa kofa. Firdausi ta kalla Maryam dan su biyu kadai su ka ji.

Ƙaran da su ke sake ji wannan karan da ƙarfi ya sa suka firgita. Firdausi ta maza ta ce su shiga cikin ɗakin Umma ta maida ƙofar ta rufe da mukulli. Bashir ya firgita ya fara kuka Firdausi ta rufe mai baki jikinta na karkarwa.

Gidan a rufe yake dan haka ko sun balla ƙofar ne suka shigo ko kuma sun hauro ta katanga.

Kici-kicin buɗe ƙofar falon ake ta ƙoƙarin yi. Firdausi ta tsure ga yara suna ta kuka. Ko wani addu'a ya zo mata karantawa ta ke yi dan wata ƙila har addu'o'in shiga bayi da na saka kaya ta karanto.

Anfi awa ɗaya ana ƙoƙarin buɗe kofar Allah be basu sa'a ba. Ba su yi magana ba amma daga ji ba mutum ɗaya ne ba. Daga ƙarshe dai su ka ji shiru babu motsi alamun sun tafi.

Daren nan barci barawo ne kaɗai ya iya sace su. Umma na dawowa da safe Firdausi ta fashe da kuka. Sai a sannan ta samu daman zubar da hawaye dan ta firgita ba kaɗan ba.

Hankalin Umma ya kai kololuwar tashi. Kamar wancan karan babu wanda ya ga shigarsu ko fitarsu. Umma Sa'adatu ta tsinci kanta cikin tsaka mai wuya, ta rasa wa zata kaiwa kukanta.

Satin gaba ɗaya bata koma wurin aiki ba. Har ta fara tunanin ko ta ajiye aikin ne. Amma aikin nan shine rufin asirin su idan ta ajiye shi taya zata kula da marayunta.

Cikin ikon Allah da ta sanar da abokan aikinta abunda ya faru da yawa a cikin su suka ce za su riƙa karɓan night duty ɗinta.

Umma bata taɓa zaton wanna karamci daga wurinsu ba. Amfanin zama da mutane lafiya kenan. Sai ya zamana ta dena night duty gaba ɗaya.

Ba'ayi wata da faruwan abun ba aka sake haurowa. Shima kaman wancan ba su samu damar buɗe ƙofar ba. Faɗin tashin hankalin da Umma ta tsinci kanta abu mai wuya ne.

Gidan ya zama harin barayi da dama tunda an san babu namiji a gidan sannan mai gidan ya rasu dan haka ana musu kallon suna cikin kuɗin gado da aka raba.

Da ASP Zubairu ya ji labari ya yi faɗa ba kaɗan ba akan rashin sanar da shi da ba'ayi ba.

"Sa'adatu ki ƙaddara ni ƙanin Ahmad ne. Kar ki ji nauyin tunkarata da komai. Babu abunda bazan iyawa jinin Ahmad ba. Ahmad ya yi mun abunda har in bar duniya ba zan taɓa mantawa da shi ba. Dan Allah ki bari in bada gudunmawata wurin kula da marayun da ya bari."

ʼYan sanda biyu ASP ya sa tsaron gidan, ɗaya da rana idan sun tafi makaranta ɗaya kuma da dare. Tunda gidan babu ɗakin mai gadi a waje ya ke patrol ɗinsa.

Wannan ne ya sa aka samu saukin abun. Amma dukda haka Umma bata koma night ba.

Ranan assabar tana kicin ta jiyo hayaniya tana fitowa ta ci karo da Musa yana balbalin bala'i.

"Wallahi ko ki shiga ki dauko mun takardun nan ko kuma ki kuka da kan ki. Babu yanda za'ayi in gama wahala da shagunan nan sannan a ce wai naki ne wallahi ba ki isa ba."

Tunda ASP ya ja mai kunne bata sake saka Musa a idonta ba. Har ga Allah ita ta manta da shi ma, abubuwan dake damunta sun yi mata yawa.

"Musa ka yi wa Allah ka rabu da mu. Wannan wani irin matsifa ne dan Allah."

"Matsifa? Ba za ki san masifa sai na gamu da ke tukun. Wallahi tallahi kin ji na rantse miki Sa'adatu abunda na yi a baya kaɗan ne, wanda zan yi nan gaba sai kin yi da na sani ba kaɗan ba. Shi yasa idan kina son zaman lafiya ki shiga ki ɗauko mun takardun shagunan biyu gaba ɗaya."

"Kenan kai ka riƙa turo mutane gidan nan da dare Musa?"

Umma ta yi tambayan cike da mamaki da kuma dumbin fargaba. Wannan wa ce irin jaraba ce?

Musa ya yi wata shu'umar murmushi ya juya ya fita ba tare da ya bata amsa ba. Ƙafafuwanta kasa daukanta su ka yi ta zube a ƙasa zufa na keto mata sannan ta fashe da kuka.

Firdausi ta nufo wurin da sauri, a kan idanunta komai ya faru.

"Ya zan yi da mutumin nan Firdausi? Ba zai barni ba sai ya samu abunda ya ke so. Ko kawai in ba shi takardun?"

Umma ta yi magana cikin matsanancin kuka. Wayyo Ahmad! Ahmad ya tafi ya barsu har Musa ke iya yi musu haka.

"A'a Umma, kada ki bashi takardun."

"Toh ya zan yi Firdausi? Ina tsoron ya illata ni ko ya illata ku."

"Ki faɗawa Baba da Baba Zubairu su za su san abun yi."

Ummi ta gyada kai. Ita zaman garin gaba ɗaya ma ya isheta. Banda matsanancin kewar mijinta da ta ke yi da kuma Inna ga Musa na nema ya zautar da ita.

Waya ta ce Firdausi ta ɗauko mata. Daga chan gefe inda ake samun network ta tsaya ta kira lambar landline ɗin gidansu tana addu'a Allah Ya sa akwai wani a kusa.

Jamila ce ta dauka Umma ta bari su ka gaisa sama-sama ta ce mata ina Baba.

"Yana ɗaki yanzu ya dawo."

"Yi sauri ki yi mai magana."

Umma Sa'adatu na jin muryar mahaifinta ta sake fashewa da wani kukan. Baba Malam hankalinsa ya tashi da kyar ya samu ta bar kukan.

"Sa'adatu mene ne? Me ya faru? Wani abun kike so?"

"Baba so na ke yi in dawo gida. Bazan iya zama a nan ba, na gaji da zama a nan." Umma ta amsa tana shashsheƙa.

"Gida kike so ki dawo Sa'adatu? Toh shikenan, bari kuka kin ji. Idan kina so ma gobe ku taho."

Baba ya ce ba tare da ya nemi jin dalilinta ba. Ɗiyar ta sa na matuƙar ba shi tausayi. Mutuwar miji ba ƙaramin abu bane. Ga kuma surukarta da itama Allah Ya dau ranta. Dan ma Sa'adatun akwai dauriya da tawakkali. Shima hankalinsa zai fi kwanciya idan ita da yaran su ka dawo kusa da shi.










~Maymunatu Bukar💕

Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro