Chào các bạn! Vì nhiều lý do từ nay Truyen2U chính thức đổi tên là Truyen247.Pro. Mong các bạn tiếp tục ủng hộ truy cập tên miền mới này nhé! Mãi yêu... ♥

5.









KANO
DISAMBA 2002.



Sanyin ƙarshen shekara ya iso. Ko ina hazo ne da hunturu. Bishiyoyi sun bushe, iska nata kaɗawa, ga ƙura. A gidan Arc. Ahmad an sa ledoji an toshe tagogi saboda a samu sauƙin sanyi. Sanyin wannan shekaran mai tsanani ne.

Maryam bata taɓa jin bata so ta je makaranta ba sai yau. Tunanin taɓa ruwa na nema ya sata kuka. Ko kaɗan bata so ta fito daga cikin bargonta mai ɗumi.

"Maryam ko dai ba ki da lafiya ne?" Umma ta tambaya da ta shigo ta ganta a kwance.

"A'a, Umma."

"To tashi kar ku yi latti."

Maryam ta ɗago kai ta kalli agogon da ke maƙale jikin bango. Da bargon nannade jikinta ta taka zuwa bayin. A nan ta bar shi tana fitowa ta ɗauka ta ƙara nade jikinta. Shafa mai ma cikin bargon ta yi.

Abun karyawa na jiran su a falo. Ita ta fara fitowa ta samu Abba na cin abinci. Tunda Abba ya dawo Kano da aiki tare su ke cin abincin safe da na dare. Hakan ba ƙaramin daɗi ya ke mata ba. Kuma tunda ya dawo shi ke kaisu makaranta. Su Zee ake fara ajiye 'yan firamare ita ce ƙarshe.

Kamar kullum Safiya ce ƙarshen shigowa mota. Abincin ma bata gama ci ba Umma ta kora ta bayan ta ƙara mata wanda ta rage cikin kular abincinta.

"Hajiya Safiya kenan," inji Abba yana tayar da mota.

Safiya ta ji kunya harda rufe fuska da hannunta.

"Ka matsa!" Zee ta faɗa da ƙarfi tana mutsu-mutsu.

"Duka nan be ishe ki ba? Ke giwa ce?" Idris ya ce fuska a kumbure.

Ta cikin madubi Maryam ke kallon su, ita tana zaune a gaba su kuma suna baya. Bashir na gefen Safiya, Zee da Idris a ɗayan gefen.

"Abba ka ga Idi na ce mun giwa!"

"Idris kada in sake ji. Ke kuma ki zauna ɗam."

Daga nan kuma motar ta yi shiru har aka isa makarantan su. Ya rage daga Abba sai Maryam a motan. Wannan lokacin na yi mata daɗi saboda hira su ke yi sosai da Abba. Wani lokacin ita zata cika shi da surutu yana sauraron ta wani lokaci kuma shi ya ke bata labari.

Yanzu ma labarin yarintan su su duka ya ke bata. Kaman kar a iso makarantan su ta ke ji.

"Mun iso," Abba ya ce yana tsayawa a bakin gate ɗin makaranta. Maryam ta turo baki. Abba ya mata dariya. "In kin dawo zan cigaba da baki."

Jakarta ya miƙa mata ta buɗe kofa ta fita. Tana ta ɗaga mai hannu har saida ta daina ganin motar.

Assembly ta samu za a yi. Da sauri ta shiga layin 'yan js2 A. A baya ta tsaya wurin ƙawayenta ana surutu, malamin na ganinta ya ce maza ta wuce gaba. Su Bilkisu na ta yi mata dariya. Ita ce ta farko a layin.

Arc. Ahmad wurin aiki ya nufa bayan ya ajiye yaran a makaranta. Kusan ko da yaushe shine farkon zuwa a ma'aikatar. Dan wani lokaci ko ma su shara ma yana riga su zuwa. Abokan aikin shi na yawan yi mai tsiya wai ko madam ke koro shi. Sai dai ya musu dariya yana mamakin su. Ga lokacin da aka yi yarjejeniya da kai za ka zo aika amma sai ka yi zaman ka sai wurin ƙarfe goma ko sha ɗaya kuma ƙarshen wata ka karɓa albashi hankali kwance.

Ko share ofis din na shi ba a yi ba. Da kan shi ya sa tsintsiya ya kakkabe wurin ya jiƙo tsumma ya goge ƙurar. Daga nan kuma ya fara aiki. Sallar azahar ce kaɗai ta tayar da shi daga kujerar da ya zauna. Bayan ya dawo ba shi ya sake motsawa ba sai da lokacin tashi ya yi.

Agogo ya kalla. Ƙarfe uku da rabi. Ko ya tafi a hanya la'asar zata iske shi. Jira ya yi aka kira sallah ya yi sannan ya hau hanya.

Kasuwa ya nufa inda zai je ya duba ya ake ciki a shagunan shi. Musa ya koya mai darasi. Tunda ya karɓa shagunan ya ke zuwa dubawa a kai a kai sabanin da da sai ya yi wata da watanni bai leƙa ba. Ɗan uwanshi ma ya yi iya son ran shi inaga bare.

Abubuwa nata tafi yanda ya kamata cikin amincin Allah. Bunƙasa da cigaba da shagunan ba su samu a baya ba sun samu yanzu.

Ya daɗe a kasuwar sai wurin ƙarfe biyar ya baro wurin. Yano ƙoƙarin rufe ƙofar motan ya ji tsayuwar mutum a gefe, daga kan da zai yi ya ga Musa.

Tsakanin shi da Musa tun wancan lokacin sai in ya zo duba Inna. Tunda abun ya faru ya fara zuwa duba Inna a kai a kai wani lokaci har sau biyu a rana. Abba ya taka mai burki, bai isa ya hana shi zuwa duba mahaifiyar shi ba amma ya tabbata duk sanda zai zo Arc yana gida idan ba haka ba ya jira a waje ko ya sake dawowa. Amma Arc bai yarda ba Musa ya shigan mai gidan bayanan ba.

"Yaya ina wuni. Yanzu Saminu ya ke ce mun ka zo."

"Lafiya lau."

Musa ya gyara hular da ke kansa. "Har zaka tafi?"

"Eh, kar dare ya mun a nan."

"To, to shikenan," ya gyada kai. "Sai da safe. Ka gaida Inna."

Arc. Ahmad ya amsa da to ya ja mota ya tafi. A hanya yana tunanin yanda alaƙar shi da Musa ta ke yanzu. Shi mutum ne da idan ya yarda da kai ya yarda kenan. Amma muddin ka ɓata rawar ka da tsalle ka yi abun da ya sa trust ɗin da ke tsakani ya ruguje to shikenan, da wuya ya iya sake yarɗa da kai.

Har ya kusa kaiwa gida ya karkata kan motar ya nufa gidan amininsa ASP Zubairu. Tare su ka yi karatun sakandire. Yaro ya aika ya yi mai sallama da mai gidan.

Arc. Ahmad na tsaye jikin mota ya fito. "Ɗan sanda abokin kowa," ya ce yana miƙewa. Hannu ya miƙa mai su ka gaisa.

"Bismillah mana Arc, mu shiga ciki."

"Ka yi haƙuri na zo babu sanarwa."

"Haba Ahmad, wace irin magana ce kake yi haka."

Falo su ka isa matar gidan ta kawo musu ruwa. Bayan an sake gaisawa Arc ya yi gyara murya.

"Dama magana mai muhimmanci na ke so mu yi. Tun lokacin da abunnan da Musa ya faru na fara tattara kan duk wasu takardu masu muhimmanci. Na samu lauya na, duk abubuwan da ake buƙata da wanda ya kamata a yi an kammala. Original ɗin zan adana su amma ina so kaima ka riƙe wasu copies ɗin."

Arc. Ahmad ya yi mai dukkan bayanin da ya kamata.

ASP Zubairu ya lumfasa sannan ya karɓa takardun. "In sha Allah zan adana maka su."

"Sa'adah zan ba original ɗin ko da amfanin su ya taso."

ASP Zubairu ya sake jinjina kai. Daga nan aminan biyu su ka yi 'yar hira kafin Arc. Ahmad ya kama hanyan komawa gida.

Ya isa ya iske Inna da yaran a tsakar gida wai tana ba su tatsuniya. Zee da Safiya sai kyalkyala dariya su ke. Farin ciki da annashuwa su ka mamaye shi ganin su a haka. Alhamdulillahi, shi kam baya da bukatar komai a duniya, yana roƙon Allah Ya cigaba da rufa musu asiri, Ya ba shi ikon cigaba da kula da su yanda ya kamata.

Yaran suna ganin shi su ka rugo da gudu ana mai oyoyo. A nan tsakar gida ya ce a kawo mai abinci shima ya zauna ya saurari tatsuniyar Inna.

Da daddare bayan an gama shirin barci da ɗauko jaka mai dauke da takardun ya ba Umma.

Umma ta fito da takardun ɗaya bayan ɗaya tana karantawa. "Baban Maryam me zan yi da wannan?"

"Ajiye su za ki yi a wurin ki."

"To," ta gyada kai. Wani akwati ta janyo ƙasan gado. A nan take adana duk wata takarda mai muhimmaci da ga kan birth certificates din yara zuwa kan takardunta na makaranta. Chan ƙasa ta tura takardun sannan ta yi bismillah ta rufe akwatin ta maida shi wurin shi.

"Shago ɗaya na maida shi sunan ki."

Da sauri ta juyo ta kalli mijinta da ke rubutu kaman ba shi ya yi magana yanzu ba. "Me ka ce?"

Arc ya ɗago kai ya kalle ta. "Daga wannan watan ribar ɗayan shagon hannunki zai dawo."

Hawaye ne suka taru a idanun Umma tana mamakin wannan bawan Allah. "Baban Maryam..." ta fara cewa sai ta yi shiru. To me zata ce?

Arc. ya yi murmushi ya miƙe ya kamo hannunta ya zaunar da ita kan kujera. "Ba sai kin ce komai ba Sa'adah na. Kin chanchanci fiye da haka."

Bayan Arc. Ahmad ya gama bautar ƙasa neman aiki ya kai shi garin Kaduna. A nan ya haɗu da Sa'adar shi. Kafin ya hau hanya ya ji kaman akwai wani gagarumin alamari da zai faru da shi ashe zai haɗu da masoyiyarsa ne a wannan tafiya. Bai samu aikin da ya je nema amma ya samu fiye da aikin. Ya samu abokiyar rayuwa mai son sa da ƙaunarsa, mai kula da shi da hakƙinsa da ya rataya a wuyanta. Ya samu uwar 'ya'yansa wacce ta basu tarbiyar da ta dace.

An ɗaura musu aure ba ya da tsayayyen aiki yana dai buga buga ya samo abunda zai riƙeta da shi. Ko sau ɗaya bata taɓa korafi akan rashin wadatarsa a lokacin ba. Wani lokaci idan komai ya tsaya mai cak da albashinta ake kula da gidan. Haka har Allah ya buɗa mai.

Dan haka idan be yi wa Sa'adah ba wa zai wa? Ta chanchanci fiye da haka.

Goshin su ya haɗa wuri ɗaya yana jin sonta na ƙara yawa a zuciyarsa. A hankali ya share hawayen da ke zubowa daga idanunta.

"Idan kina mun godiya, ina ji kaman ba ki san matsayin da kike da shi a zuciyata ba. Ina son ki sosai Sa'adah. A kan ki zan iya yin komai."

Umma ta runtse ido tana murmushi ga hawaye na gangarowa fuskarta. Alhamdulillah da miji irin Ahmad. Da tazo magana sai kalaman su bace mata dan haka ta haɗe bakunan su wuri guda tana fatan ta haka fahimci irin tsantsar son shi da ta ke yi itama.

***

Maryam ta kalla Idris da Zee ta kalla kwabin da su ka zubar mata. Wani baƙin ciki ne ya shaƙe mata wuya bata san lokacin da ta fashe da kuka ba.

Zee ta zaro ido hankali tashe, Idris shima duk ya ruɗe. "Yaya ki yi haƙuri. Bari mu kwashe miki."

Harara ta galla mata tana share hawayen da takaici ya saka ta yi. "Dallah ku fita ku bani wuri!"

Maryam bata da hayaniya bata da faɗa amma ta yi fushi sai Allah. Umma kan ce halin Abban su ta ɗauko.

Da sauri Zee da Idi su ka bar kicin ɗin. Ƙasa ta kalla inda kwabin ya ke malale duk ya bata kicin ɗin. Wainar flour za ta yi dama da kyar ta samu Umma ta barta. Wai ta gama kwabawa kafin ta ɗauko tanda su ka shigo kicin ɗin garin rawan kai su ka barar da shi.

Har ta ɗauko tsintsiya ta ajiye. Ɗakin su ta nufa. "Wuce ku je ku goge wurin." Ta ce babu alamun wasa.

Tarbiyar Abba da Umma ne girmama na gaba da kai duk da ƙarancin shekaru da ke tsakanin su. A gidan ma Idris da Zee ne kawai ke yawan faɗan saƙo da saƙo.

Da ƙunƙuni su ka tafi kicin ɗin. A ƙasa ta zauna har yanzu haushi na cinta. Allah Ya sani ta saka ran cin wainar flour, ga shi flour ɗin da ta rage kenan.

Hakanan tana ji tana gani ta haƙura. Takarɗunta ta ɗauko ta fara homework ɗin da aka bata.

"Yaya tun yau za ki yi homework ɗin," inji Safiya da shigowarta kenan. "ki bari sai gobe mana. Gobe fa assabar ko kin manta."

"Ban manta ba Hajiya Safiya," ta kirata da sunan da ya bita tun ranan da ta cewa Abba zata yi tunanin abunda ta ke so ta zama idan ta girma. "Gwara in yi yau kawai, kin ga na huta."

"Hmm mmm, ni dai sai ranan lahadi da dare."

"Ko Monday da safe ba." Maryam ta girgiza kai. Ta san halin ƙanwarta wata ƙila sai a makaranta ma zata yi ko ta kwafa.

"Tunda an kusa fara jarabawa be kamata a riƙa bada homework ba."

"Allah Ya shirye ki Safiya."

Safiya ta yi dariya. "Ina wainar flour ko har kin cinye?"

"Ina fa na yi ma ba su Idi sun zubar da kwabin ba kuma flour ta ƙare."

"Idan Abba ya dawo daga masallaci sai mu je mu karɓa kuɗi mu siyo shagon buzu, nima ina so in ci."

"To," Maryam ta gyada kai.

Abba ya dawo masallaci wurin ƙarfe biyu. Kaman yanda ya ke al'ada a gidan duk juma'a tuwon shinkafa a ke yi da miyar agushi lafiyayya da taji nama da kifi. Sai kuma kunun aya ko zobo mai sanyi. A falo gaba ɗaya aka taru aka ci abincin.

Bayan an gama Safiya da Zee su ka kwashe kwanuka Bashir na taya su. Idi kuma ya ɗauko tsumma ya goge ledar ya fitar da ita waje ta sha iska.

"ʼYar mitsilan Abba me ya same ki kike bata rai." Abba ya tambayeta.

Maryam ta turo baki ta faɗa mai abunda ya faru. Hannu ya sa cikin aljihu ya ciro kuɗi ya miƙa mata. "Gashi ki siyo flour, a yi da yawa yanda kowa zai ƙoshi."

"To Abba. Mungode," ta ce da fara'a. Da sauri ta fita ta nunawa Safiya. Tare su ka je su ka siyo komai sannan aka shiga kicin a ka hau aiki.

Abba ya shiga ɗaki ya ce bari ya ɗan runtsa. Barci bai dauke shi ba wayarsa ta yi ƙara. Ganin sunan shugaban ma'aikatar da ya ke aiki ya saka shi dagawa da sauri. Sai ba a ji da kyau. Dole se da ya fita akwai wani tudu a cikin unguwar, nan a ke samun network me kyau.

Mintin su sama da talatin suna waya. Bayan sun yi sallama Abba ya kalli wayar yana mamaki shin dagaske ne ko mafarki. Kaman ya ruga da gudu ya isa gida ya sanar da Sa'adah ya ke ji.

Da saurinsa ya isa gida. Ɗakin Inna ya fara nufa ya sanar da ita abun alherin da ya same shi.

"Alhamdulillah! Alhamdulillah. Muna yi wa Allah godiya da rahamarSa a gare mu. Allah Ya taimaka, Ya ida nufi. Allah Ya yi maka albarka."

"Ameen Inna, ameen."

Inna ta yi mai addu'a mai tsawo.

A hankali ya daga labule. Sa'adah na tsaye hankalinta na kan kayan da ta ke jerawa cikin akwati. Ba tare da ya bari ta ji shigowarsa ba ya taka a hankali ya isa wurinta ya daga ta sama.

"Inna lillahi wa inna ilahi raji'un!" Umma ta ce da ƙarfi tana kokarin juyawa ta ga waye. "Ahmad!"

Arc. Ahmad ya yi dariya ya ajiyeta a hankali. Umma ta harare shi hannuwanta dafe da ƙirjinta. "So kake yi zuciyata ta buga."

Arc ya sake yin dariya. "MD din mu ne ya kirani. List din ma'aikatan da za su tafi Kuwait ƙaro karatu ya fito....akwai sunana a ciki."

"Alhamdulillah!" Umma ta maƙale mai wuya cikin murna. "Alhamdulillah."

Arc ya rungumeta sosai, ya cigaba da cewa, "gobe zan ce Abuja in Allah Ya yarda, an nemi wanda sunayen su ya fito a list. Tafiyan zata kasance farkon shekara bayan new year In Sha Allah."

"Kai Masha Allah. Allah Ya taimaka."

"Ameen," ya amsa yana janye jikinsa daga nata. "Yau juma'a, dan Allah a dafa abinci a rabawa mabuƙata."

Umma ta gyada kai. "Yanzu kuwa." Sake rungume shi ta yi jin daɗi kafin ta nufa kicin. Sau biyu yana applying be samu ba sai yanzu.

A kicin ta iske duka yaran suna wainar flour. Daɗinta dai ba a hargitsa mata wurin ba. Duk da tasan dama Maryam ba zata yarda su bata ba.

Tuwo ta yanke shawarar ta ƙara yi. Tunda abincin da yawa ta aika Idi ya kira wata yarinya nan makwabtan su da ke zuwa taya Umman aiki wani lokacin.

Tare da Maryam a ka yi aikin a ka gama. Akwai makarantan almajirai nan kusa da su, nan aka fara kaiwa. Sannan aka rabawa makwabta da aka san mabuƙata ne. Abba ya dauki wasu ya kai asibiti.

Da dare ya faɗawa yaran. Suna ta murna dukda ba wai sun fahimci abunda ya ke nufi ba sosai.

"Abba a jirgi zaka ko a mota?" Zee ta tambaya.

Me Idi ze yi idan ba dariya ba. "Ke wurin da ze je da nisa fa, taya ze je a mota?" Harda girgiza kai irin abun ya bashi takaici.

Zee ta kalli Abba dan bata yarda da maganan yayanta ba. "Wai haka Abba?" Abba ya gyada kai. "To Abba ni ban taɓa hawa jirgi ba."

"Kar ki damu Zainabu Abu, za ki hau wata rana In Sha Allah."

"Abba dame dame a ke saidawa a Kuwait ɗin?" Inji Safiya.

"Ana saida komai da komai."

"Ni zan yi maka list ɗin tsaraban da na ke so."

Kowa ya yi dariya ita kuwa Hajiya Safiya ta haɗe fuska.

"Abba idan ka tafi zaka daɗe baka dawo ba?"

Maryam ce da wannan tambayan. Ita tun ɗazu abunda ke damunta kenan.

"Ba kya so in daɗe ne ʼYar mitsilan Abba?"

Sunan dariya ya ke bata. Wai ʼyar mitsila. Ko da yake ita ʼyar mitsilan ce. Kai ta gyada. Tafi kowa farin ciki da Abba ya dawo aiki a Kano. Tana jin daɗin ganinsa kullum, su ci abinci tare, ya kai su makaranta, ya taya su homework. Duka wannan na mata daɗi. Bata so ya yi nesa da su. Gidan ya fi daɗi idan Abba yana nan.

"Kar ki damu, kafin ki ce me har na dawo. Kuma za mu riƙa yin waya mu gaisa kin ji."

Da murmushi ta ce, "to Abba."

Safiya ta je ta ɗauko takarda da biro aka hau rubutu list. Abba na dariya ya ce basu san dalibi ze zama ba ai baya da kuɗi.

"Abba makaranta kuma? Kai baka girma da makaranta ba?" Zee ta ce da dukkan gaskiyarta.

"Abule ai ba a girma wurin neman ilimi."

Zee ta kalle shi. "Inna yaushe zata tafi makaranta to?"

Me za a yi idan ba dariya ba. Inna ta yi mata daƙuwa. "Ja'irar yarinya."

Washegari da sassafe Arc. Ahmad ya shirya zai ɗauki hanyar birnin tarayya. Umma ta rako shi jikin mota, har ya tada ya kashe. "Sa'adah taso yaran nan mu yi sallama."

"Da ka rabu da su ka yi tafiyarka kawai."

Arc ya girgiza kai. "Babu daɗi su tashi basu ganni ba."

"Baban Maryam kana da son yara, gobe fa zaka dawo."

"Kin ga laifi na?"

Shi dai bai yarda ba saida ya shiga ciki ya tado su gaba ɗaya harda dan auta Bashir. Ɗaya bayan ɗaya ya rungume su ya ce musu sai ya dawo. Ya shiga ya sake yi wa Inna sallama ya fito.

Yaran tare da Umma su ka raka shi mota. Ya bude kofar zai shiga sai kuma ya tsaya. Umma zata tambaye shi ko ya yi mantuwa ne ta ji ya rungumeta.

"Sai na dawo." Ya ce daidai kunnenta.

"Allah Ya dawo mana da kai lafiya."

Sake rungume yaran ya yi lokaci ɗaya, sannan ya sumbace su a goshi. "Allah Ya yi muku albarka."

"Abba sai ka dawo." Duka su ka ce a tare.

Ya yi dariya sannan ya shiga mota. Idi ya buɗe get ɗin gidan. Waje su ka fita suna ta daga mai hannu har saida motar ta ba ce daga ganinsu.

"To, mu koma ciki." Umma ta ce tana dafa kafaɗar Maryam. Har yanzu gari be gama waye ba dan haka ta maida kwado ta rufe gidan.

Ranan Umma kyuyan girki ta ke ji. Akwai tuwo Inna ta ce a dumama mata shi, sauran ʼyan gidan kuma su ka ci taliyar Hausa. Ta fito daga bayi inda tayo arwalan sallan azahar ta ji gabanta ya faɗi har saida ta dafa ƙirjinta.

"Hasbunallahu wa ni'imal wakeel." Ta yi ta nanatawa.

Amma har ta idar da sallah firgicin nan bai barta ba. Tunda tana kan abun sallah sai ta sake kabbara ta yi nafila raka'a biyu. Tana cikin zikiri aka yi sallama. Kafin ta fito Idris ya shigo da gudu.

"Umma ga Baba Zubairu ya zo."

"To, ce mai gani nan zuwa."

Littafin Hisnul Muslim dinta ta ajiye ta fita. Ta same shi zaune a falo. A kujerar zaman mutum ɗaya da ke kusa da kofar ɗakinta ta zauna su ka gaisa.

"Ko bai faɗa maka ze yi tafiya ba?"

ASP Zubairu ya gyada kai amma be ce komai ba. Sai a lokacin Umma ta lura da yanayinsa. Bugun zuciyarta ya tsananta, jikinta ya fara rawa.

"Zubairu lafiya?"

Ya dago kai ya kalleta. Kafin ya yi magana Umma ta fara girgiza kai hawaye na gangarowa fuskarta.

"Sa'adatu sai dai mu yi haƙuri. Allah Ya yi wa Ahmad rasuwa sanadin hatsarin mota."









~Maymunatu Bukar💕

Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro