4.
Washegari Arc. Ahmad ya gama yanke hukunci da ya dace ya ɗauka. Ya nemi izinin fashi daga ofis dan haka bayan ya sauke yaran daga makaranta ya dawo ya samu Inna.
Yana jin daɗi kullum ya ganta akwai cigaba, ta chanza gaba ɗaya kaman ba ita ba. Ashe dama rabin ciwon nata rashin kula ne.
Sun yi hira sosai da Inna kafin ya yi gyaran murya. "Inna akwai maganan da na ke so mu yi."
"To, Allah Ya sa lafiya."
Abba dai bai ce komai ba. Tun daga kan rashin kaita asibiti har zuwa kan abunda Musa ya yi wa Sa'adah duka ya faɗa mata bai ɓoye komai ba.
"Amma Musa ya ci amanar zumunci," Inna ta ce tana girgiza kai. "Musa bai kyauta ba. Allah ne gatan shi, sai kai amma da abunda zai saka maka kenan? In har ya iya maka haka kenan da mahaifin ku na raye zai mai haka kenan. Kai amma ban ji daɗi ba. Ka kirawo mun shi, ina son ganin ku gaba ɗaya."
"To Inna." Abba ya amsa a sanyaye. Da niyar shi ya samu Musa hukuma ta raba su. Sa'adah ce ta ce Inna na da rai bai kamata ya tsallaketa ya tafi kotu kai tsaye ba. Ya fara samun Inna tukun alabashi daga baya idan ya kama sai a je wurin hukumar.
Yaro ya aika unguwar su Musu a kira shi. Bayan sallar azahar sai ga shi. Da ba dan Inna ta ce a kira shi ba da babu abunda zai sa Musa ya tako ƙafa ya shigo mai gida.
Musa na shigowa ya sha jinin jikinsa ganin irin kallon da Ahmad ke yi mai, sannan bai tarbe shi da fara'a kaman yanda ya saba ba.
"Ina wuni Yaya?" Musa ya ce yana ƙaƙalo murmushi.
Ahmad ko kallon shi be yi ba ya miƙe ya shiga ciki. Musa ya haɗiyi miyau da kyar. Babu daɗewa Ahmad ya dawo tare da Inna. Itama Inna sama sama ta amsa gaisuwar shi.
"Musa?" Inna ta kira sunan shi murya a dake.
"Na'am Inna."
"Bayan mahaifin ku ya kwanta rashin lafiya wa ya biya maka kuɗin makaranta har ka gama?"
Musa ya kalli Inna sannan ya kalli Ahmad. Murya chan ƙasa ya ce, "Yaya."
Kai Inna ta gyada. "Bayan ka gama makaranta ya samo maka aiki ko be samo maka ba?"
"Ya samo mun."
"Me ya samu aikin? Shi kake yi yanzu?"
"A'a ba shi na ke yi ba."
"Me ya faru ka bar aikin?"
"Laifi na yi aka sallame ni."
"Bayan nan mai ya faru?"
Musa ya kalli mahaifiyar shi yana jin wani irin ɓacin rai. "Na cewa Yaya ni kasuwanci na ke so in yi ba aikin gwamnati ba." Ya bata amsa. Jin ta yi shiru tana kallon shi, ya cigaba, "ya bani jari na bude shago a kantin kwari."
"Aure fa?"
"Shi ya yi mun lefe, ya biya sadaki sannan ya bani gida."
Inna ta girgiza kai. "Ashe baka manta duka wannan ba? Amma ka iya shure duka alkhairin da ya maka ka saka mai ta hanya mafi muni. Ka bani kunya Musa. Bayan cin amanar shi da ka yi har iyalin shi ka ce zaka illata."
"Munafuka, Sa'adatu ce ta zo ta faɗ—"
"Musa!" Abba ya daka mai tsawa. "Ka da ka sake ka aibunta mun mata. Zan ɗauki mummunan mataki a kan ka."
"Yaya ita ta zo ta haɗa muku ƙarya da gaskiya, kai babu ma gaskiya a zancenta. Ta ya zan yi maka haka Yaya? Kai ma ka san ba zai taɓa yiwuwa ba."
Arc. Ahmad ya kalle shi cike da takaici. "Jami'an tsaro na saka su ka yi mun bincike."
Jin an kira jami'an tsaro Musa ya san ƙaryar shi ta ƙare.
Inna ta fashe da kuka, tana cewa, "ka ci amanar zumunci Musa, ka ci amanar zumunci."
Da sauri Abba ya nufa wurinta, Musa kuma ya zube a ƙasa. "Inna dan Allah..."
"Yi mun shiru mutumin banza kawai. A nan zan yanke muku hukunci tunda na isa da ku, ni na haife ku ba ku kuka haifeni ba. Daga yau duk wata dukiyar Ahmad da ka san tana hannunka ka tattara ka maido mai abun shi. Sannan maganar kasuwanci ba zata sake shiga tsakanin ku ba, kowa ya je ya nemi na shi shi kaɗai tunda abun haka ne. In ya ji zai iya yafe maka dukiyar da ka cinye da wanda ka yi mai asara to Alhamdulillah, idan kuma ba zai iya yafe maka ba sai ku je alƙali ya raba ku."
Inna na gama magana ta shiga ciki. A ɗaki ta yi kukan takaicin halin Musa Umma na bata baki. Tun suna yara Inna ke yawan cewa Ahmad ya bar Musa ya san zafin nema ba komai ya ɗauka ya bashi ba. A lokacin Ahmad murmushi kawai ya ke yi, ya ce idan bai yi wa Musa ba wa zai wa? Ga irin ranar da ta ke gudu nan ta zo.
A falo Musa na kan gwiwowin shi yana roƙon gafara. "Yaya ka yi haƙuri wallahi sharrin shaiɗan ne. Yaya ka gafarce ni."
"Miƙe tsaye," da sauri Musa ya tashi. Arc. Ahmad ya kalle shi. Ɗan uwansa ne wannan da suka fito ciki ɗaya, ko ya ce ze yi mai wani abu ma son da ya ke mai ba zai bari ba.
"Da niyata hukuma ce za ta raba mu. Ko baka dawo mun da ƙudin ba sai ka kwana bayan kanta saboda abunda ka yi wa Sa'adah."
Musa ya zaro ido, zufa na keto mai. Ya shiga uku! A barshi da cika baki da barazanar iska amma matsoraci ne lamba ɗaya.
Ya buɗe baki zai yi magana Ahmad ya dakatar da shi. "Sa'adar da ka ke son cuta ita ta yi ta bani haƙurin tun jiya. Ta ce kada in biye maka in bari duniya ta san abunda mu ke ciki. Ka je Musa na barka da Allah, Shi zai ƙwatar mun hakƙina. Kai ba ƙaramin yaro bane bare a ce baka san abunda ya dace ba. Duniya ce dai ko? Ka je gata nan ta ishi kowa riga da wando. Wanda bai zo ba ma jiran shi ta ke yi. Ni na san darajar zumunci a musulunci, na kuma san hukuncin wanda ya yanke shi. Amma ka sani abubuwa ba za su taɓa komawa yanda su ke a da ba har abada. Kuma ina gargaɗin ka ko da wasa ka sake tunkarar iyalina da makamancin abunda ka yi, wallahi, wallahi, wallahi ba za ka ji da daɗi ba. Ka tashi ka bar mun gida."
Da sauri harda tuntuɓe Musa ya bar gidan. Tunda dai babu maganar dawowa da kuɗi sannan babu zancen jami'an tsaro da kwana bayan kanta ai shikenan. Duk wani jawabi da ya yi ya bi iska tunda ya tsira da ran shi da mutuncin shi.
Ahmad ya zauna ya dafe kai. Mikewa ya yi ya shiga ɗakin Inna. Umma na ganin shi ta miƙe zata fita. Hannunta ya riƙo ya dawo da ita. A gefen Inna ya zauna.
"Inna dan Allah ya isa haka."
"Dole in yi kuka," ta girgiza kai. "Ba tarbiyar da na ba Musa ba kenan, ban ba shi wannan tarbiyar ba."
"Ki yi haƙuri Inna, hawayen ki musiba ce a gare shi."
Da ƙyar aka samu Inna ta daina kuka. Magani Umma ta kawo mata na ciwon kai, a ciki ta haɗa da na barci. Babu daɗewa barci ya ɗauke Inna. A hankali su ka rufo mata ƙofa su ka nufi ɗakin su.
Kan kujera Arc. Ahmad ya zauna idon shi a rufe. Umma ta tausaya mai sosai. Sam babu daɗi a ce na kusa da kai ne ke cutar ka. Kusa dashi ta zauna ta sarƙe yatsunsu wuri ɗaya tare da ɗaura kanta a kafaɗar shi. Arc. ya gyara zama ya maida kan Umma zuwan ƙirjin shi.
Sun daɗe a haka kafin Arc ya sa yatsun shi a haɓar Umma ya ɗago kanta. A hankali ya sumbaci goshinta.
"Nagode."
Umma ta rungume shi. "Babu godiya tsakanin mu."
***
Ƙoƙarin buɗe tukunyar da ke kan wuta ta ke yi zafin ya sa ta yarda murfin da sauri. Allah Ya so tukunyar bata faɗi ba.
Bayan ta gama yarfe hannu cikin ciwo ta kyalla ido ta hango tsumman goge na kicin ɗin. Saida ta linka shi sosai yanda ba zata ji zafi ba.
"Maryam!" Umma ta kwalo mata kira. "Wai baki duba ba?"
"Gashinan zan duba," ta faɗa da ƙarfi dan Umma ta jiyo ta.
Talge ne Umma ta ce ta dubo ko ya fara bararraka. Ya fara kuwa dan har wani tsalle ya ke yi. Maryam kawai ta ji sha'awar tana so ta tuƙa tuwon.
Za ko ki burge Umma! Wata zuciyar ta ce mata.
Murmushi ta yi harda tafawa. Ta je ta ɗauko muciya da garin semovita sannan ta janyo kujera yanda zata ga cikin tukunyar da kyau. Dama bata maida murfin tukunyan ba. Da yake lefty ce da hannun hagu ta riƙe muciyar tana deɓo garin da hannunta na dama.
Da kaɗan kaɗan ta ke zuba garin tana juyawa a hankali. Tana yi abun na burgeta, irin ita ɗinnan! Tana so taga tana girki komai na tafiya daidai. Dan ma Umma bata son bata da ita zata riƙa dafa abincin gidan nan kullum.
Ta maida hankalinta kan tuƙin tuwon daga sama ta ji muryar Idi. "Kai! Wa ya sa ki? Se na faɗawa Umma. Umma! Umma! "
Da ƙarfin shi ya yi maganan hakan ya firgita ta sosai. Garin juyawa kujerar ta gurɗe Maryam ta faɗi muciyar da ke ɗauke da talge mai tsananin zafi ta biyo ta sai kan hannunta na dama.
Wani irin ihu ta kwala ta riƙe wurin da ɗayan hannun.
Abba ne ya fara shigowa da gudu Umma na biye da shi. Daukarta ya yi yama rasa mai ya kamata ya yi. Umma ta ce ya sauketa gaban famfo. Hannun ta saka ƙasan ruwan.
Maryam na ta kuka. Abba ya ɗauko mukullin mota yana nema ya ɗauketa Umma ta hana shi. Duk ya ruɗe bai lura taimakon gaggawa ta ke bata ba.
Sauran 'yan uwan duk sun yi tsaye a gefe suna kallon 'yar uwar su jiki a sanyaye, musamman Idris da a kan idonsa ta faɗi. Bashir ma ganin tana kuka ya sa shima ya fara. Inna ta fito jin hayaniya.
Umma ta ce Safiya ta ɗauko mata first aid box a ɗaki. Bayan Umma ta kashe famfon Abba ya ɗauki Maryam da ke kuka har yanzu ya kaita falo.
Umma ta shigo falon ɗauke da ruwa mai ɗumi. Wani roba ta ciro daga first aid box ɗin ta ɗiɓa ruwan dumin kaɗan ta haɗa abun ya yi kumfa. Handgloves ta saka sannan ta ciro auduga.
"Umma mene ne wannan?" Maryam ta tambaya cike da tsoro tana ƙoƙarin miƙewa.
"Sabulun wanke ciwo ne, babu abunda zai miki."
Maryam ta zare ido. Sabulu fa! Ai sai ta nema hanyan waje. Abba ya yi saurin ruƙota. A kan cinyar shi ya ɗaurata ya riƙe ta gam har Umma ta gama wanke ciwon ta yi mata dressing.
An dai sha ihu da haure-haure. Fuska ta yi shanana da hawaye harda su majina.
Umma ta kalleta yanda ta yi wuri-wuri. Babu zafi fa ko kaɗan. Bata ma tsaya ta ji ko da zafi ko babu ba kawai ta sa a ranta akwai. "Kar ki sauke hannun."
Maryam sai ajiyar zuciya ta ke yi. Kanta ta tura ƙirjin mahaifinta har lokacin tana kuka. Shi ya riƙe mata hannun bai damu da majinar ma da aka goge mai a riga ba. Ɗaki ya kaita sannan ya sa pillow ya yi supporting hannun. Daɗinta ma ciwon ba a bayan hannun bane zata iya aje shi ba tare da ta fama ciwon ba.
Umma ta shigo ɗakin da robar ruwa da ledar magani a hannu. "Karɓa ki sha," ta miƙa mata. Maryam ta yamutse fuska. Umma ta ce. "Idan ba ki sha ba sai dai a kira ayi miki allura. Zaɓi ya rage na ki."
Da sauri ta karɓa tana sake yamutsa fuska. A nan su ka barta ta huta. Su Safiya kuma Umma ta ce kada wanda ya shiga ya dameta. Inna ta leƙa barci har ya dauketa.
Umma na maida kayan da ta yi amfani wurin su tambayan Abba ya sa ta juyawa.
"Me ya sa kika sa ta tuƙa tuwo fisabilillahi?"
Ashe ran shi a ɓace ya ke tun dazu dannewa kawai ya ke yi. Kukan Maryam har yanzu yawo yake a kunnensa.
"Ni ban saka ta ta tuƙa mun tuwo ba. Ka santa da karambani, daga na ce ta duba idan ya fara tafarfasa kawai ta fara tuƙawa. Ni ban saka ta ba."
"Duba tukunyan ma ai bai kamata a sata ba. Duka Maryam ɗin nawa ta ke. Da yanzu duka tukunyar ta faɗo mata fa."
Umma ta fahimci harda tsoro ke sa shi faɗa dan haka ta ja bakinta ta yi shiru har ya gama.
"Ka yi haƙuri," ta ce bayan ya gama.
Tuwon da ba a ci ranan ba kenan.
Kwanan Maryam goma tana jiya. Shagwaɓa dai an sha ta. Tana yi Abbanta na biye mata. Duk abunda ta ce tana so shi ake mata.
Umma na bata kulawar da ya kamata. Ciwon ya ƙame ya bushe. Kullum aka zo dressing sai an yi daga da Maryam.
Ranan nan da ta ba Umma haushi har dungurinta ta yi. "Za ki zo haihuwa dan ƙaniyarki, zan ga yanda za ki yi. Yarinya sai shegen raki."
Daga ƙarshe dai Abba ya gama mata dressing din ranan.
Babbar ƙawarta Bilkisu Kabir ta zo dubata. Sun shar hira sosai kafin Bilkisu ta tafi.
Da dare duka a taru a falo ana hira. Ba a yi abincin dare ba Abba ya dawo da gurasa da lemun kwalba.
Yaran nata ba mahaifin su labarin abunda ya faru a makaranta yau.
"Abba an sa ni a drama!" In ji Zee. "Idan na girma ina son zama 'yar film."
Idi ne ya fara kwashewa da dariya. Zee sarkin tsiwa ta maka mai harara.
"Ba dai film ba Zainab," Abba ya ce. "Ki dai nemo wani abun da kike so ki zama."
"To zan zama nurse kaman Umma!" Ta ce da ƙarfi.
"Nurse Zainab Ahmad. Masha Allah! Allah Ya taimaka. To in dai kina son zama nurse kaman Umma sai kin dage da karatu."
"To Abba."
Abba ya yi murmushi ya shafa mata kai. "Kai kuma fa?" Ya tambaya Idris. "Kai me kake so ka zama?"
"Me ƙera abubuwa."
"Wasu irin abubuwa?"
"Mota da jirgi."
"Engineer kenan."
"Eh shi!" Idi ya yi dariya.
Abba ya koma kan Safiya itama ya tambayeta. Buden bakinta ta ce, "Ni dai Abba har yanzu ban sani ba, sai na yi tunani."
Umma ta yi dariya ta girgiza kai. "Sai ki dage ki yi ta tunanin ai."
"To Yaya Maryam fa? Ke mai za ki zama idan kin girma?"
Maryam ta yi shiru na ɗan wani lokaci. Murmushi ta yi, "Abba ni resturant na ke so in buɗe, wurin cin abinci."
"Ba ki dandara talgen da ya zubo mi ki ba kenan," Abba ya tsokaneta. "Chef Maryam. Allah Ya bada sa'a. Wani suna za ki saka?"
"Baban Maryam," Umma ta yi dariya. "Ina ta san wani suna za ta saka, ko kin sani Maryam?"
Maryam ta girgiza kai.
"In baki suna kina so?" Abba ya tambayeta. "Amma fa na baki sai kin biya ni."
"Ina so Abba. Kuma idan na buɗe resturant ɗin zan biya ka."
"Kowa ya yi sheda Yaya zata biya ni idan ta buɗe resturant."
Kowa ya ce ya shaida.
Abba ya yi shiru ya na bubbuga haɓar shi alamun yana tunani. Maryam ta ƙagu ta ji sunan.
"In faɗa?"
"Eh!" Duka suka ce da ƙarfi.
"Yaya kaɗai zan faɗawa, matso kusa." A kunne ya raɗa mata. Ta yi dariya ya mika mata hannu su ka tafa.
"Abba muma a faɗa mana," Zee ta ce tana tura baki.
"Ki bari sai Yaya ta buɗe za ki sani."
Abba ya ɗauka Bashir ya ɗaura shi kan cinya. "Malam Bashir dai footsteps ɗina zai bi, architect zai zama. Sa'adah lokacin retire din mu ya kusa fa. Muna da chef, engineer, nurse, architect da kuma Hajiya Safiya. Kin ga sai mu ja gefe mu zauna."
"Shikenan mun huta."
"Allah Ya yi muku albarka gaba ɗaya. Kowa sai ya dage. Make Abba proud."
•
•
•
•
~Maymunatu Bukar💕
Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro