3.
KANO
YUNI, 2002.
Rana ake kwallawa ba kaɗan ba. Duk zafin ranan Maryam bata jin ta saboda ta yi wa Umma laifi. Bayan sun taso daga makaranta Bilkisu Kabir ta ja ta gidan su, niyarta ta yi minti ɗaya ta fito amma ta na shiga ta iske Umman Bilkisu na dafa abincin suna da za a yi a nan layin su. A taƙaice dai da ita aka gama komai.
Gashi har an kira sallar ƙarfe huɗu. Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un! Yau zata chasu ne kawai. Ko abincin da Umman Bilkisu ta bata bata ɗauko ba.
Gudu ta ke yi amma kaman ana janta baya har yanzu bata iso ba. A ƙofar gida ta ci karo da su Zee za su tafi islamiya.
"Yaya? Ina kika je? Umma na ta neman ki, har Habun gidan Malam ta aika ya je makarantan ku ya dubo ki." in ji Safiya tana kallon yanda yayarta ke cira idanu.
"Ina Umma?" Ta tambaya tana haki.
"Tana ciki tana jiran ki." Zee ta amsa ta.
Wani irin juyi cikinta ya yi. Yau ta shiga uku.
Bata ma san lokacin da su Zee su ka tafi ba. Takalman ta ta cire ta riƙe a hannu. A hankali ta tura ƙofar gidan ta leƙa. Babu kowa a tsakar gida. Saɗab saɗab kaman sabuwar ɓarauniya ta fara takawa, har ta kusa ƙofar falo Umma ta kira sunanta. A zabure ta yarda takalman ta juya.
Umma na tsaye ƙofar kicin ta rungume hannu tana kallonta. Tunda ta leƙo Umma ta ganta. Dariya ma ta bata, yanzun ma idanunta har sun cika da ƙwalla.
"Daga ina ki ke?"
"Umma dan Allah ki yi haƙuri...."
"Ni ba haƙuri na ce ki bani ba, daga ina ki ke?"
"Gidan su Bilkisu."
"Wa kika tambaya?"
"Ban tambayi kowa ba. Dan Allah ki yi haƙuri Umma wallahi ba zan sake ba."
"Zo nan," Umma ta ce fuskarta babu alamun wasa.
Da kyar Maryam ta iya haɗiyan miyau. Shikenan tata ta ƙare. Idan akwai abunda ta tsana shine a taɓa lafiyar jikinta. Shi yasa ko a makaranta bata taɓa yarda ta yi laifin da zai kai a yi duka.
Tun kafin ta kai gaban Umma ta fara kuka. "Umma dan Allah ki yi haƙuri wallahi ba zan ƙara ba. Dan Allah Umma."
Umma dai ta haɗe fuska amma dariya ce ke cinta. Maryam sai tsoro kaman farar kura. Ta na isowa gabanta Umma ta kamo kunnenta ta ɗan murda kaɗan.
"Gobe ki ka sake sai na miki duka. Je ki ci abinci ki zo ki shirya ki tafi islamiya."
Maryam ta riƙe kunnenta da ke raɗaɗi. "Umma na yi latti wallahi da dorina mai baki biyu a ke duka."
"Kin san ana dukan lattin kika tafi yawo. Maganin ki kenan, gobe ma kya sake tafiya yawo ai. Maza ki wuce ki shirya."
Ta san babu yanda za ta yi dole ta tafi islamiya. Ko abincin bata tsaya ta ci ba ta tafi. Ta ko iske har an tare ƴan latti a ƙofar makaranta. Yau dai ta bani. Ba zata sake biyawa ko ina ba daga yau. Ana tashi makaranta zata wuce gida.
Malamin da ya ganta cikin ƴan latti ba ƙaramin mamaki ya yi ba dan ya san ba halinta bane. "Maryam Ahmad ya aka yi ki ka yi latti yau?"
Ta ɗukar da kai tana wasa da yatsunta. "Bani hannun ki."
Hannunta na hagu ta miƙa mai tana karkarwa. Da ya ɗaga bulalar sai ta kauce. Haka ta yi ta yi da kyar ya mata guda biyu a maimakon biyar ya ce ta tafi tunda bata saba latti ba.
Maryam dai ta so ta daure amma tana zama kan benchi sai kuka. Da yake sune ƙananun aji dan smally ma ake ce mata a benchin gaba ta ke zama. Ido duk ya yi ja, gashi daman ta yi kuka a gida kafin ta taho.
Karatun ranan rai ba ɗaɗi ta yi shi. Da aka tashi ma ko jiran su Zee bata yi ba. Duk da haka kusan tare su ka isa gida. Sun iske Abba ya dawo daga wurin aiki.
Tun dawowar Inna ya fara neman transfer a dawo da shi Kano sai watan da ya wuce ya samu transfer ɗin.
"Ah ah, Yaya Maryam me ya same ki naga kaman kin yi kuka."
"Abba yawo ta tafi bata dawo ba sai ƙarfe huɗu," Zee ta ce tana komawa kusa da shi. "Kuma a islamiya a ka yi mata dukan latti."
Maryam ta makawa Zee harara. "To, gulmammiya wa ya tambaye ki."
"Maryam!" Umma ta kira ta da ɗan ƙarfi. "In ƙara ji kina kiran ƴan uwanki da sunayen banzan nan."
"Matso nan Yaya," Abba ya ce yana miƙa mata hannu. "Ina kika je?"
Maryam ta ji tsoro, bata miƙa mai hannunta ba daga inda ta ke a zaune ta amsa shi. "Gidan su ƙawata Bilkisu na je. Abba ka yi haƙuri wallahi ba zan sake ba."
"Good. Idan za ki je wani wuri ki tabbata kin sanar da Umma ko ni, bana son in sake ji kin maimaita abunda ki ka yi yau."
"In sha Allah Abba ka yi haƙuri," ta juya ta kalli Umma. "Umma ke ma ki yi haƙuri."
Umma ta daga mata kai, Abba ya ce. "Shikenan ya wuce. Wa zai sha ice cream?" Duka suka daga hannu. "To ku je ku chanza kaya, idan na dawo masallaci sai muje a siyo."
Bayan sun fita Umma ta kalle shi. "Tuwon da na yi fa wa zai cinye?"
Abba ya kwashe da dariya. "Ki ci kayan ki, mun ƙoshi."
Umma ta gyada kai. "Shi za ku ci gobe da safe kuwa."
Abba ya yi ta mata dariya yanda ta yi da fuska. Dawowar shi Kano ba ƙaramin cigaba ya kawo a zaman su ba, sun sake fahimtar juna fiye da baya, wanda ba su taɓa zaton akwai sauran abun fahimta tsakanin su ba sai yanzu.
Bayan sallar maghriba Abba ya sa su Maryam a mota su ka fita aka bar Umma da Inna kaɗai a gida. Umma ta haɗa abinci ta kai wa Inna a ɗaki.
"Sannu Sa'adatu," Inna ta ce da murmushi a fuskarta.
Ta chanza sosai tun dawowarta gidan, har ƴar ƙiɓa ta yi fatarta ta murje. Yawan rashin lafiyar ya ragu sosai Alhamdulillahi. Umma na bata duk kulawar da ta ke buƙata, abinci ma ba ko wanne ta ke ci ba sai masu amfani a jikinta.
Inna na cin abinci suna hira da Umma. Akwai kyakyawwar fahimta tsakanin Umma da surukarta, ta ɗauke ta tamkar uwar da ta haifeta itama Inna ta ɗauke ta tamkar ʼyar cikinta.
Umma na nan har barci ya ɗauke Inna. Dama ta yi shirin barcinta kafin ta zauna cin abinci. Umma ta gyara mata kwanciya sannan ta tattare kayan ta kai kicin. Itama ba jin cin tuwon ta ke yi ba dama saboda Baban Maryam ta yi kuma ya tafi ya barta da abunta. A fridge ta saka dan kada ya lalace. Ta san gobe da safe shi da kan shi zai ce a kawo mai ɗumame.
Ɗaki ta koma ta fito da takardun da ya kamata ta duba kafin ta je aiki gobe. Tunda aka chanza CMD a asibitin da take aiki komai ya taɓarɓare. Mutane sam ba su tsoron Allah kwata kwata, abun tsoro ya ke bata. Magani da kayan tallafi da gwamnati ta ke kawowa marasa lafiya shi su ke rabawa tsakanin su hankali kwance kaman sun manta Allah zai tambaye su. Son abun duniya ya rufe musu ido.
Son abun duniyan ne ya sa Musa ya tunkare ta da zancen wani fili ta kaiwa Ahmad ya siya. Tun ba yau ba Arc ya ke zancen siyan fili ya fara gini, ya ce gidan da su ke ciki yana nema ya yi musu ƙadan.
Ko ƙadan Umma bata kawo wani abu a ranta ba duk da ta yi mamaki me ya sa Musa ya kawo mata tallar be kai wa ɗan uwanshi kai tsaye ba. Ta samu amsarta wata rana ta je gaishe da Inna ta shiga gidan Musa inda ta ji shi yana hira matar shi. Tazo shiga falon kenan ta jiyo shi, sai ta dakata.
Umma ba ƙaramin firgita ta yi ba. Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un! A ce ka fito ciki ɗaya da mutum amma kana cutar shi kuma kana bari wasu su cuce shi. Ina duniyar nan zata mu?
Filin na ʼyan damfara ne da aka haɗa baki da shi idan ya kawo mai siya za a bashi kaso mai tsoka a ciki. Dalilin shi na samun Umma kuwa dan kada a zarge shi kuma daga gefe zai riƙa ziga ɗan uwan shi akan lallai da haɗin bakin ita Sa'adatu aka cuce shi.
"Ina so in kawar da ita gefe guda, ta zamana bata iya taɓuka abun arziƙi a kan dukiyar shi, dan komai Yaya ze yi sai ya yi shawara da ita," Musa ya ce da takaici. "Ta bi ta yi wani kane-kane ta kulle mun ko wace ƙofa. Kuɗin magani ma da na likita bana iya ƙarawa sosai saboda Ahmad ya kama ya kai Inna asibitin da take aiki. Kin ga kuwa idan na yi ƙari mai yawa zai tambayeta daganan asiri na ya tonu."
Gwiwa a sake Umma ta koma gida. Ta rasa inda zata saka kanta. Lokacin Arc. ya yi tafiya. Ko ya dawo ma bata san ta ina zata fara faɗa mai ba.
Washegari sai ga Musa ya dawo da zancen filin. Umma ta yi mai tas! Ta ce kuma duk wani sharri da ya ke nufin su da shi Allah Ya mayar kan shi. A lokacin ne a ka yi walƙiya Umma taga ainihin waye Musa.
Wani irin dariya ya bushe da ita. Fuskar shi ta chanza ta zama abun tsoro. Umma ta firgita ta fara ja da baya.
"Sa'adatu kenan. Kina tunanin Yaya zai yarda da zancen ki?" Ya sake wata irin dariya mara daɗin ji. "To ki faɗa mai mu gani. Na yi miki alƙawari muddun ki ka buɗe baki kika sanar da shi ba za ki so abunda zai biyo baya ba."
Wannan ne lokacin farko da Maryam ta iske ta tana kuka. Na biyun kuwa ya sake dawowa ne ya sake jan kunnenta, dan har ikirarin illata yaranta ya yi, kuma ya nuna mata wuƙa. Ta firgita sosai ta kasa tsaida kukanta har Maryam ta same ta a haka.
Tun lokacin Umma ke tunanin ta ya zata bullowa abun. Sai gashi Arc ya fara gano gaskiya da kan shi. Wannan ne ya sa hankalinta ya fara kwanciya, yanzu idan ta faɗa mai zai fi saurin yarda. Amma har yanzu ta kasa gano hanyar da ya kamata ta bi ta sanar da shi kada lokaci ya ƙure. Dan ta san tabbas Musa na chan na wani sabon shirin yanda zai cutar mata da miji.
Tunda Inna ta dawo gidan Musa bai sa ke zuwa ya sameta ba. Sau biyu dai yana zuwa da sunan duba Inna, idan sun haɗa ido yana mata wani irin kallo mai ban tsoro.
Umma ta yi zurfi cikin tunaninta bata ji shigowar shi ba sai da ya taɓa ta. Da sauri ta ja baya cikin tsoro sai da taga shine ta sauke ajiyar zuciya.
Arc. Ahmad ya kalleta, "Lafiya Sa'adah? Ko akwai wani abu da ke damun ki."
"A'a, babu komai," ta ce tana girgiza kai. "Aiki ne ya ɗauke mun hankali. Sannu da dawowa. Ina yaran?"
"Yauwa," ya amsa yana gyara zama a ƙasa inda ta baje takardu. Ɗaya ya dauko ya duba. "Yaran sun tafi sun kwanta. An sha tsalle tsalle duk an gaji."
"In kawo maka tuwon?" Umma ta tambaya murya cike da zolaya.
Abba ya yi dariya. "Maman Maryam idan ban ci tuwon nan ba anya zan kwana lafiya kuwa? A yi mun haƙuri sai da safe, kinga sai in ci in haɗa da kunu idan zan samu."
"Kai da gidanka, zaka samu mana."
"Wane ni? Komai ai saida izinin gimbiya," miƙewa ya yi ya fara haɗa kan takardun. "Yanzu dai Gimbiya Sa'adah kike ba Nurse Sa'adah ba dan haka a ajiye takardun nan a gefe a kula da ni."
Ya tattare takardun gaba ɗaya ya adana mata su sannan ya miƙa mata hannu. Umma na murmushi ta saka hannunta cikin na shi ya miƙar da ita. Hannun shi ya rataya a wuyanta ya ja su zuwa gado.
***
Jiki a sanyaye Arc. Ahmad ya dawo gida. Umma na ganin shi ta san babu lafiya. Yaran sun tafi islamiya Inna kuma na barci. Ɗaki ya nufa ba tare da ya ce mata komai. Da sauri ta bi shi gabanta na faɗuwa.
"Baban Maryam lafiya? Me ya faru?"
Bai ce komai ba sai kai da yake girgizawa, idanunshi sun kaɗa sun yi ja jawur. Umma hankalinta ya tashi sosai. A ƙasa ta zauna shi kuma yana kan kujera. Hannun shi ta kamo jikinta na karkarwa ɗan bata taɓa ganin shi cikin wannan yanayin ba.
"Ahmad mene ne? Kana tsorata ni." Muryarta rawa ta ke alamun ƙiris ya rage ta fara kuka.
Arc. Ahmad ya yi wani murmushi mai cike da ciwo. Hannun shi ya zare daga nata ya miƙe tsaye. Itama da sauri ta miƙe.
"Baban Maryam..." Umma ta sake kira.
Ya juya mata baya, baya so ta gan shi a haka zuciya a raunane. Bayan an yi mai dukkan bayanan da ya nema komai ya ɗauke mai, ya ji kawai so yake yi ya gan shi a gida. Sai da ya shigo ne ya ji dama bai taho nan ba saida ya saita kan shi.
Umma ta sha gaban shi. Ta rasa abunda zata yi kawai ta fashe da kuka. Arc hankalin shi ya ƙara tashi ya fara rarrashin ta. Ganin haka Umma ta yi ƙoƙarin saita kanta.
"Me ya faru?" Ta sake tambaya.
Arc ya sake girgiza kai. Har yanzu ya kasa yarda da abunda aka sanar da shi. "Duniyar nan babu amana."
Jin haka Umma ta fahimci me ye matsalar. Sai tausayin shi ya kamata. Idan ita ce ɗaya daga cikin ƙannenta biyu su ka mata haka bata san ya zata ji ba. Bare shi da su biyu kaɗai su ka rage ga mahaifiyar su ba isasshen lafiya gare ta ba, sauran ʼyan uwan dama su da babu duk ɗaya.
"Musa. Sa'adah Musa fa. A ce da musu za a haɗa baki a cutar da ni, saboda son abun duniya." Kai Arc ya girgiza zuciyar shi na tafarfasa.
Umma ta kamo hannun shi ta zaunar da shi kan kujera. Kaman yanda ta yi ɗazu ta zauna a ƙasa hannun shi cikin nata.
"Kin san abokina Zubairu ai, police dinnan," Umma ta gyada kai. "Shi na samu na ce ina so ayi mun bincike mai zurfi a kan Musa, tun lokacin da na gano halin da Inna ke ciki hankalina bai kwanta. Abun ya yi muni Sa'adah..." ya girgiza kai. "Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un! Kai! Kai!"
Ko a mafarki Arc. Ahmad bai taɓa tunanin Musa ze yi mai haka ba. Ko kowa zai yi mai haka bai zata harda Musa a ciki ba.
"Gona da ake ta samun asara kwanakin baya ashe duk shine. A ce an ɗauko kaya ʼyan fashi sun tare motar duka da sa hannun Musa. Me ye ban yi wa Musa ba? Ba wai ina mai gori ba ne, ko ɗaya, kawai ina so in sani idan akwai inda na gaza har ya yi mun haka."
"Babu ta inda ka gaza," Umma ta ce hawaye na bin fuskarta. "Babu inda ka gaza Ahmad. Kawai Musa ya kasance maha'inci mai son kan shi, mai rama alkhairi da sharri. Ko ɗaya kada ka yi tunanin kana da laifi, ko me zaka yi mai ba zai taɓa godewa ba saboda ya sa hassada da ƙeta a ran shi. Ba laifin ka bane."
Arc Ahmad ya kalleta cikin ido. "Me yasa ba ki faɗa mun ba?"
Ƙasa Umma ta yi da kanta. "Ka yi haƙuri. Na rasa ta inda zan fara tunkarar ka da zancen."
"Ban ji daɗi ba sam. Ashe har akwai abunda za ki ji nauyi ko tsoron sanar da ni, kenan ba mu zama ɗaya ba."
Da sauri Umma ta dago tana girgiza kai. "Ba haka bane. Ka yi haƙuri."
Umma ta faɗa mai abunda da ya faru ba tare da ta ɓoye komai ba. Ran Arc. Ahmad ya ƙara baci fiye da da.
"Musa ya shigo gidan ya ce zai illata mun ke da yarana ki kasa buɗe baki ki faɗa mun? Da sai yaushe za ki faɗa mun to? Sai ya illata ku tukun?"
Umma ta sadda kai ƙasa. Sai yanzu ta ke ganin kuskurenta. "Na yi kuskure. Ka yi haƙuri ka yafe mun."
Kanta ya ɗago. "A kan ki da Maryam, Safiya, Idris, Zainab da Bashir, zan yi faɗa da kowa. Kune rayuwata ba zan taɓa yarda wani ya wulaƙanta ku ko ya cutar da ku ba, matuƙar ina raye."
Arc. Ahmad ya cewa Umma yana so ya runtsa. Ta tashi ta bar ɗakin amma ba a son ranta ba. Ta san yana cikin wani hali kuma yana ɓoye mata dan karta tada hankalinta.
Arwala Arc. Ahmad ya yi bayan fitar Umma ya kai kukan shi wurin wanda Shi kaɗai zai iya share mai hawaye ya magance mai matsalolin shi. Ya daɗe kan abin sallah.
Bayan ya idar ya zauna tunanin yanda zai yi da Musa dan ba zai bar shi hakana nan ba. Da akan shi abun ya tsaya da da sauƙi amma har ya iya tako ƙafa ya shigo mai gida sannan ya yi barazanar cutar da matar shi da ʼyaʼya ya kasance dole ya gane kuren shi.
•
•
•
•
•
~Maymunatu Bukar💕
Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro