27.
OKTOBA 2010.
Yau da faduwar gaba Umma Sa'adatu ta tashi. Ko wurin aiki bata samu nutsuwar yin aikinta da kyau ba. Tana dai maimaita 'Hasbunallahu Wa Ni'imal Wakeel'
Lokacin tashinta bai yi ba ta tattara ta tafi. Har ta kusa gida ta karkata kan motarta ta yi hanyar gidan Fatima (Maman Hamida).
"Wai wai wai. Shi yasa na ke ta ganin hadari ashe kifin rijiya ce ta fito yau." Cewar Maman Hamida cike da zolaya.
Umma ta harare ta tana zama kan kujera. "Daɗi na da ke sharri wallahi Fatima. Ke da kike magana ina kike zuwa? Gwara ni ina fita aiki ma."
"Ai ni gidana ne ofis ɗina." Fatima ta yi dariya. "Sannu da zuwa. Daga wurin aiki?"
"Wallahi kuwa. Har na kusa gida na juyo nan. Yau tunda safe na ke jin faɗuwar gaba na rasa dalili. A hanyata ta komawa gida abun ya tsananta shi yasa ma na taho nan."
"Subhanallahi. Allah dai Ya sa lafiya."
"Ameen."
Fatima ta cika gaban Umma da abinci da snacks. Dama da tsohuwar yunwarta ta taho dan haka ta ci abincin sosai. Tana ci suna hira.
"Amma dai Baban su Hamida baya nan ko?"
"Baya nan, ya yi tafiya. Mai ya sa kika ce haka?"
"Haba no wonder. Da yana nan da kin tashi ya fi a irga. Na lura shifa Oga baya son ki yi nesa da shi."
Fatima ta kwashe da dariya harda riƙe ciki. "Kin rama. Lallai Sa'adatu irin wannan sharri haka."
"Babu zancen sharri. Shi yasa ban fiye son zuwa gidanki ba."
"Sharri kala kala. Dama kallon da ki ke yi mana kenan."
"Ke ma kin san gaskiya na faɗa."
"Toh ya za mu yi. Soyayyah bata tsufa sai dai matsoya su tsufa."
Umma ta jinjina kai tana dariya. "Eh lallai. Tabbas hakane."
"Kin gani. Ke ma kin ƙi bada haɗin kai a samu wanda zai riƙa lasa miki zumar."
"Bari dan Allah. Na gudu ban tsira ba kar ki koma Mama."
"Har yanzu tana kan bakarta?"
"Ai babu abunda ya chanza sai wanda ya yi gaba ma. Na kasa gane dalilinta. Ko da ina budurwa bata matsa mun haka ba."
"Tunda kika ga haka tana da dalilinta. Ke dai kawai ki yi ta addu'a."
"Addu'a ai kullum cikin yinta na ke yi. Sai dai in ƙara dagewa."
Tun ranan da ta sanar da Baba Malam decision ɗinta ta ke isthikarah cikin dare. Daidai da rana ɗaya bata taɓa tsallakewa ba. Ta miƙa wuya ta barwa Allah zaɓi. Domin duk abunda Ya hukunta daidai ne.
Komawarta Islamiya ba ƙaramin () ya yi ba. Tabbas ilimi rahama ne. A ajin su na Seerah malamar ke sanar da su duka matan fiyayyen halitta zawrawa ne banda Nana Aisha (Allah Ya yarda da ita). Hakan ya sa ta ji wani sanyi da nutsuwa. Mutuwar miji ba sabon abu bane kuma idan ka dogara da Allah sai Ya baka fiye da wanda ka rasa. Umm Salamah bint Abi Umayyah(RA) yanda ya zo a hadisi ta yi addu'ar Allah Ya bata wanda ya fi Abu Salamah bayan rasuwarsa sai Allah Ya bata Manzon tsira amincin Allah su tabbata a gareshi.
Allahu Akbar!
Sannin hakan ba ƙaramin ƙarfin gwiwa ya bata ba. Ta ƙara dammararta na addu'ar mafi alkhairi, ta barwa Allah zaɓi.
Ta daɗe suna hira da Fatima har lokacin tashinta na asali ya yi. Sai da ta yi sallar la'asar ta kama hanya. Isowarta gida ya yi daidai ta fita wasu dattijai su huɗu. Bata kawo komai kanta ba ta shiga. A gareji ta haɗu da ƙannen Baba da ʼyan uwansa su uku. Ta yi mamakin ganin su dan bata ji Baba na cewa za su zo ba. Bayan sun gaisa su ke ce mata tafiya za su yi, fitowar su kenan. Sai dai kafin su tafi ɗaya ke ce mata Allah Ya sanya alkhairi.
Addu'ar ta ɗaure mata kai. Wani abun ta samu a ke mata fatan alkhairi? Bata fahimci zancensa ba ta watsar dan ita ta faɗuwar gaban da ke damunta ta ke yi.
Cikin gida ta iske Firdausi ta zo da yaranta. Suna ganin Umma su ka rungumeta. Mintin ta biyu su ka gaisa kafin ta shiga ciki. Dayake cikinta a cike ya ke bata nemi abinci ba.
Aikin da bata samu damar yi a ofis ba ta fiddo duk da ya kamata a ce ta kwanta ne ta huta. Sai dai zamanta haka nan zai sa ta yi ta tunane tunane da basu da amfani. Shiyasa ta ɗauko abunda zai ɗauke mata hankali.
Ba ta yi nisa da aikinta ba Firdausi ta leko kai ta faɗa mata Baba na kiranta a falonsa. Ba tare da ta yi dogon tunani ba ta nufi falonsa sai dai ganinsa zaune tare da Mama ya sa ƙirjinta amsawa.
Kiran menene a ka yi mata?
Bayan ta gaishe su ta zauna bayan ʼyan daƙiku Baba ya yi gyaran murya. "Mama Sa'adatu," ya kira Mama da sunan da bai ciki amfani da shi ba. "Ke ce shaida wata ɗaya da ya gabata mun zauna kamar haka da Sa'adatu ta bani izinin in aurar da ita ga duk wanda na so in har na gamsu da dabi'unsa."
Ai yana faɗan haka gaban Umma ya yanke ya faɗi. Ashe faɗuwar gabam ɗazu nafila ce.
"Tabba haka ne," Mama ta ce. "Ni ce shaida. Da bakinta ta furta wannan kalaman. Haka a ka yi. Babu wani baren zance a nan."
"Toh Alhamdulillahi." Baba Malam ya jinjina kai. "A yau ni a matsayina na mahaifin Sa'adatu na ɗaura mata aure."
Umma Sa'adatu ta tsinta kanta cikin yanayin da babu kalaman da za zata iya bayani da su. Na ɗaura mata aure kawai ke kai kawo cikin kanta.
Cikin amincin Allah abu na farko da laɓbanta su ka furta shi ne. "Ya Hayyu Ya Qayyum!" chan ƙasan maƙoshinta.
Mama kuwa sai hamdalah ta ke yi tana godewa Ubangiji da ya nuna mata ranar da ta daɗe tana jiran zuwanta. Burinta ya cika.
"Alhamdulillah! Alhamdulillah! Ba ka faɗa mana da wa a ka ɗaura ba."
Baba Malam sai ta ya ɗauki wasu ʼyan mintuna kafin ya faɗa sunan da Umma Sa'adatu kwata-kwata ko a mafarki bata taɓa kawo wa a ranta ba.
"Da CSP Zubairu ne. Yanzu wakilan shi su ka fita."
Tunda Baba ya kira Zubairu komai ya kwance Umma ta daina fahimtar komai. Wani yuu ta ke ji a kunnuwanta kaman ƙarar rediyo.
"Sa'adatu." Muryar Baba ta yi nasarae dawo da ita hayyacinta. "Bayan na zauna da ke babu daɗewa Zubairu ya same ni da ƙudurinsa a kan ki. Ban amince kai tsaye ba sai da na yi binciken da ya kamata a kansa duk da na san sa, amma maganar aure ba wasa. Saboda hukuncin da ki ka ɗauka ya sa na hanashi zuwa wurinki duk da ya so ya yi jayayya na nuna masa babu damuwa. Bayan na gamsu da binciken da na yi a kansa shine a yau na ɗaura miki aure."
"Kai Alhamdulillahi! Alhamdulillahi!" Mama ta sake maimaitawa cike da farin ciki. "Ba ki ce komai ba."
Sa'adatu ta dago fuska da hawaye ke kwarara. Ta kalla mahaifinta sannan ta kalla mahaifiyarta. Wata natsuwa da ƙarfin gwiwa da bata san daga ina su ke ba ta samu. Ta tsinci kanta da cewa, "Allah Ya tabbatar mana da alkhairinSa."
Mama ta yi ƙayataccen murmushi ta na ta saka mata albarka. "Malam ba ka ji daɗin da na ke ji ba. Wannan haɗin ya yi. Idan akwai wanda zai riƙe yarinyar nan da ʼyaʼyanta bai wuce Zubairu ba. Yaron kirki, yaron arziƙi. Mutum mwi dattako. A da ma ya yi bare yanzu da a ka ƙulla tsaftattaciyar alaƙa a gaban Allah SWT. Banda ko tantama zai riƙe amana."
Umma dai ba zata iya cewa ga yanayin da ta ke ciki ba. Ta san ta nemi zaɓin Allah, kuma Ya zaɓa mata bata da jayayya. Sai dai ƙasan ranta ta kasa tantace asalin mai ta ke ji game da al'amarin. Gaba ɗaya jikinta ya dauke.
"Tashi ki shiga ciki Sa'adatu. Allah Ya ba ku zaman lafiya."
Jiki a sanyaye, gwiwa a sake Umma Sa'adatu ta taka zuwa dakinta. Bata tsaya ko ina ba sai kan sallayarta. Da arwalarta dan haka ta kabbara sallah.
A sujada idan bawa ya fi kusanci da Mahaliccinsa ta fashe da kuka tana cewa "Ya Allah ba ka kuskure. Komai Ka yi daidai ne. Na karɓa zabin Ka hannu bibbiyu. Ya Rabbi, Ya Ubangijina Kada ka barni da wayona ko dubarata. Ni mai rauni ce, mai nema a wurinKa Ya Rahman. Ya Allah Kai ka ce mu roƙa za Ka amsa, Ya Allah... Ya Rabbi..."
Ta daɗe a wannan yanayi har sai ta ji nauyin da ke ƙirjinta ya tafi gaba ɗaya. Wayarta ta lalubo ta kira aminiyarta Fatima wanda bata da tamkarta.
"Hajjaju ya kika isa?" Cewar Fatima.
Umma ta kasa cewa komai sai kuka da ta fashe da shi.
Hankalin Fatima ya yi matuƙar ta shi. "Lafiya? Mai ya faru? Wani abu ya samu yaran ko su Baba? Me ya faru? Sa'adatu ki faɗa mun me ya faru!"
Umma na shashasheƙa ta faɗa mata abunda ya faru.
Fatima ta yi jum na minti kaɗan. "Wanene? Be yi mi ki bane? Ba kya so? Sai da na ce miki kin yi wauta da kika barwa Baba zabi. Wa aka aura miki?"
"Fatima CSP Zubairu. Zubairu abokin marigayi."
"Wai!" Fatima ta sauke ajiyar zuciya. "Na sha da wani abokin Baba Malam a ka haɗa ki ai. Haɗin bai yi miki ba? Ba kya so?"
"Ban isa in ce bana so ba tunda da bakina na ba Baba zaɓi. Aikin gama ya gama tunda an ɗaura amma Fatima na rasa ya na ke ji. Abokin marigayi ne fa..."
"Bari in katse mi ki zance indai wannan ne dan Allah kar ki ɗaga hankalinki. Na san za ki ji kamar kin ci amanar marigaya. Amma abu ne da Allah Ya hallarta, ba haramun bane kar ki bari shaiɗan ya ci galaba a kan ki. Wa ke rasuwa ƙani ya auri matar balle aboki. Kina ta addu'a, kina ta neman zabin Allah. Gashi Allah Ya bayyana mi ki zabinSa gare ki. Zabin Allah shine daidai a rayuwar dan Adam. Da Allah Ya bar mu da wayonmu da tuni mun taɓe. Saboda haka Sa'adatu yanda kika dage da addu'a ki cigaba da yi. Allah Ya baku zaman lafiya. Allah Ya haɗa kannku, Ya baku ikon sauke nauyi da haƙƙin da ya rataya a wuyan ku. Allah Ya baku zaman lafiya mai ɗaurewa. Gobe in sha Allahu da sassafe za ki ganni. Dan Allah kar ki bari shaiɗan ya ci galaba a kan ki ya sa ki tunanin kin ci amanar marigayi."
Magana da Fatima ya kwantar mata da hankali kwarai dan chan ƙasan ranta ji ta ke ta zama maci amana. Ta aura Zubairu aminin mijinta. Amma tunawa da ta yi ta kwana ta yini tana neman zabin Allah sai a hankali ta riƙa samun natsuwa.
Bata dai tashi daga kan abun sallar ba haka Mama ta shigo ta sameta. Mama ta kalleta ta ruƙo mata hannu, ta rungumeta.
"Alhamdulillahi. Ina matuƙar farin ciki. Zubairu mutumin arziƙi ne kin sani ba sai na faɗa miki ba. Sannan Allah ba zai taɓa zaɓar miki abunda zai cutar da ke ba matuƙar kina da yaƙini matuƙar kin yi tawakkali. Saboda haka kada ki damu, ki kwantar da hankalinki. Allah Ya yi miki albarka. Allah Ya baku zaman lafiya. Na san na takura ki da batun auren nan saidai nan gaba na ke duba miki Sa'adatu. Zama hakanan babu daɗi. Kina da buƙatar wanda zai kula da ke. Nauyin ya yi miki yawa ke ce nan ke ce chan. So na ke yi in ganki kema wani ya kula da ke fiye da yanda Malam ke kula da ke. Ba a san gawar fari ba amma ni da mahaifinki kullum tsufa mu ke yi. Sauran ʼyan uwanki na gidajensu ke na ke ta tunani. Idan mu ka tafi mu ka bar ki ke da yaran nan wa zai kullan mana da ke? Shiyasa kika ga inata matsawa."
Allah sarki uwa! Komai ta yi daga so ne. Ba dan ƙiyayya ko musgunawa ba.
Umma Sa'adatu ta kifa kanta a cinyar Mama tamkar ƙaramar yarinya hawaye na gangarowa. "Na gode Mama. Na gode."
"Allah Ya yi miki albarka."
Misalin ƙarfe tara da rabi na dare wayar Umma ta yi ƙara. Ganin sunan CSP Zubairu a fuskar wayar ya sa gabanta faɗuwa. Hannuta na rawa har wayar na neman subucewa ta amsa kiran.
Sai dai ta kasa cewa komai sai shi da ya yi sallama ta amsa. Daganan duka su ka yi shiru.
A ranta tana ayyanawa yanzu wannan shine mijinta! Allah Ya wajabta haƙƙoƙi da wajibai da ya zama dole ta sauke su garesa a matsayin mijinta. Aljannarta na ƙarƙashin ƙafarsa yanzu. Take jikinta ya yi matuƙar sanyi tana jinjina girmar al'amarin.
"Sa'adatu."
Kiran sunan har tsakar kanta dan bai taɓa kiranta haka ba. Sai dai ya ce 'Maman Maryam'.
"Kin amince? Are you okay with it? Da na samu Baba na so ya bari in nema amincewar ki ya ce ba haka ba. Ki aje batun biyayya a gefe Sa'adatu ki faɗa mun are you okay with this? Kin amince? Kada ki ji nauyin faɗa mun abunda ke ran ki."
Umma ta zuƙa lumfashi ta sauke a hankali. Maganganun Mama da na Fatima da addu'o'in da ta taɗe tana yi su ka dawo mata. A hankali ta furta, "eh."
Daga ɗayan bangaren Zubairu ya sauke nannauyar ajiyar zuciya har ta na iya jiyowa. "Alhamdulillah! Na gode. Allah Ya bani ikon faranta miki rai, Allah Ya bani ikon riƙe amana. In sha Allah ba za ki taɓa nadamar amincewa ba. Na gode."
Kalamansa sun yi mata daɗi sannan sun ƙara saka ta samun natsuwa.
"Sai da safe amaryar Zubair."
Daganan ya kashe wayar ya barta da dumbin kunya.
A daren nan bacci barawo ne kawai ya iya sasheta.
Ta farka washegari ba tare da damuwa ko tsoron ranar da ta gabata ba, sai dai kuma fargabar abin da wannan sabon babi na rayuwarta zai ƙunsa ya maye gurbinsu.
Kamar yanda Fatima ta yi alƙawari da safe sai gata. "Amarya. Amarya." Tana shigowa ta rangaɗa guɗa.
Umma ta girgiza kai. Jin guɗar ya sa Mama ta fito aiko ta taya Fatima. Umma Sa'adatu kaman zata nutse ƙasa dan kunya. Wai harda Mama a ke guɗa, kai jama'a!
Mama na fita bayan sun gaisa Fatima ta ciro leda. "Ni matsalata ɗaya da auren nan da ya zo babu notice. Ban shirya ƙawata ba."
"Ke dallah chan." Umma ta ture ta.
"Da gaske na ke yi. Gyara ki zan yi tsab! Ko sabuwar budurwa albarka."
Umma ta girgiza kai jin shirmen da ƙawarta ke faɗa. Fatima ta hau ciro kayan da ke cikin ledar tana ta bayani yanda Umma za ta yi amfani da su.
"Wai a yaushe duk kika samo wannan?" Ta ce da mamaki tana kallonta.
Fatima ta kashe mata ido. "Daga cikin kayana na diban miki. Kin san ni ba dai baya ba wurin gyara. In har ki ka yi amfani da kayan nan ko? Ke da kan ki za ki nemi ƙari."
Saboda fitina irin ta Fatima sai da ta saka ta wanka da ruwan lalle da magarya haɗe da turaren miski. "Kullum safe da dare za ki riƙa wanka da shi. Yaushe ne tarewan?"
Nan fa ɗaya. Ita wannan tunanin sam bai zo kanta ba ma. "Allahu a'alam. Sai na ji daga gareshi."
Daga nan Fatima ke tambayarta ko yaran sun sani. Cike da damuwa Umma ta ce ba su sani ba. "Ban san ya za su ɗauki zancen ba."
"Kaman yaya? Ya wuce su yi murna? Ba baƙo bane ai, sun san shi kuma akwai kyakyawar alaƙa a tsakanin su."
"A da da yake matsayin aminin mahaifinsu ba. Yanzu kuma da matsayinsa ya chanza ban sa ya za su ɗauke shi ba."
Fatima ta kwantar mata da hankali. A nan ta yini sai yamma ta tafi. Bayan sallar la'asar Baba ya shigo falon Umma ya miƙa mata brown envelope. "Ga sadakin nan dubu ɗari."
Umma ta zaro ido cike da mamakin yawan kuɗin.
A hanyar Baba na fita ya barta a daburce da kalamansa na ƙarashe. "Ki shirya anjima mijinki zai zo."
***
Bayan sallar isha'i Mama ta yi dubara ta kora yaran tare da Baba Malam wai su tafi ziyara. Ya rage daga ita sai Umma a gidan.
Tun ɗazu Umma ta haɗa kan ʼyan snacks ɗinta. Ta yi kewar Maryam, da tana nan ta san ita zata yi komai. Falon ta gyara ta kunna turaren wuta. Bayan ta idar ta salla ta samu kanta da yin wanka da haɗin Fatima. Cikin kayanta ta ciro atamfa dinkin riga da zani ta saka. Kallar kayan ya haska fatarta. Tana zaune bakin gado cike da fargabar haɗuwa da shi a karo ma farko tunda matsayinsa ya chanza a rayuwarta.
Sallamarsa ya haddasa wa zuciyarta matsanancin bugo. Tana ji suna gaisawa da Mama. Daga nan Mama ta ce bari ta kirata.
Mama na buɗe kofar idonta ya sauka kan hijabin da ke gefenta. Take ta haɗe rai. "Dauko mayafi."
"Mama?" Ta ce a daburce.
Mama bata amsa ta ba ta ɗauke hijabin ta nemo gyalen da ya hau da kayan. Ita dai tana ganin ikon Allah wurin Mama. Sam ta daina nuna mata ʼyar kunyar nan da ta ke yi da.
Daga nan ta fita abunta ta bar Umma da faɗuwar gaba. Bayan wasu ʼyan minti ta saita kanta ta dauki mayafin ta yafa har kai.
Duk taku ɗaya tana jiyo ƙarar bugun zuciyarta a kunne har ta isa falon. Ƙamshin turarensa ya haɗu da turaren wutan ya bada wani ni'imtaccen ƙamshi.
Kafin ya ɗago Umma ta kalle sa. Sanye ke da shadda ɗinki babbar riga kalar sasarin samaniya sai sheƙi ta ke yi ta haska fatarsa da ke wankan tarwaɗa. Ga hula da ke ƙyali a kan sa.
A hankali ta taka zuwa kujerar da ta fi kusanci da ita. Wanda kuma ta kasance mafi nisa daga wanda ya ke a zaune.
Umma Sa'adatu ta kasa ɗaga kanta sama har su ka gama gaisawa.
"Sa'adatu."
Yanayin da ya kira sunanta dole ta ɗaga kai. Suna haɗa ido ta yi saurin ɗaukewa.
"Na dade ina neman zabin Allah kafin na zo wurin Baba da batun neman aurenki. Na so kwarai a ce mun fahimci juna kafin wannan lokacin sai dai haka Allah Ya tsara. Ni da ke mun rasa abokan rayuwarsu da mu ka yi zaton za mu kasancr tare har abada. Sai dai Allah ba Ya barin wani da wani ya ji daɗi. Lokaci na yi ko sakwan ɗaya ba za ka ƙara ba. Dukkan mu lokaci mu ke jira. Buƙata ta ba mu maye gurbin wanda su ka tafi su ka barmu bane. Bana tunanin har mu bar duniya zamu iya kwana mu wuni ba tare da yi musu addu'a ba. Duk da mutawa ba ta da rana duka mutuwar farat ɗaya su ka yi. Ahmad ya tafi bai dawo ba, Ladidi kuma mun rabu lafiya na dawo na iske rai ya yi halinsa.
Abunda na ke koƙarin in ce Sa'adatu shine mu taru mu ƙarasa saura a abinda ya rage a rayuwarmu cikin aminci. Ni da ke duka babu yaro a ciki. Mu taru mu riƙe yaran da na ɗauke su tamkar ʼyaʼyan cikina. In sha Allah za ki same ni mai kula da riƙe amana. Mu gina rayuwar mu cikin farin ciki da aminci."
Maganganunsa sun yi tasiri sosai a kai a kan Umma Sa'adatu. Duk wucewar daƙiƙa na sake tabbatar mata ba ta yi kuskuren amincewa ba. Kai ta ɗaga su ka haɗa ido a mutumin da ya kasance bata da tamkar shi a yanzu. Matsayinsa ya fi na kowa a rayuwarta sannan haƙƙinsa da ya rataya a wuyarta ya fi na kowa nauyi.
A hankali ta ɗaga kai. "Allah Ya bamu ikon rike amanar juna sannan Ya tabbatar mana da alkhairinSa a kodayaushe."
Murmushi ya yi har tana jiyo sautin. "Ameen Amaryar Zubair."
Sunan da ya kirata da shi kenan jiya ya barta da matsinanciyar kunya. Miƙewa tsaye ta yi. "Bari in kawo maka ruwa."
Tana shiga kicin ta sauke nannauyar ajiyar zuciya. Tray ɗin da ta shirya tun ɗazu ta dauka ta fita. A gabansa ta ajiye ta tsiyaya zoɓon ta miƙa masa. Karɓa ya yi yatsunsa na shafar nata. "Na gode."
Wurin zamanta ta koma tana wasa da yatsunta.
"Akwai wani abu da kike buƙata ko ki ke so ki yi?"
Umma ta girgiza kai. "Babu ko ɗaya."
"Haba Hajjaju a taimaka ko walima a yi, hakan yana da kyau."
"Toh. Duk yanda ka ce haka za a yi."
"Amma banda kai amarya. Ni zan zo in dauketa da kai na."
Mutumin nan so ya ke yi ta nutse dagaske kenan.
"Kuma ke mu ke jira ki buɗe mana gida." Umma ta ɗago kai ta kallesa da mamaki. Zubair ya ɗaga mata gira. "Eh. Kin taɓa gani an shiga gida ba tare da rabbaitul bait ba?"
Umma idan ta fahimci abunda ya ke so ya faɗa mata, tun sannan ya yanke hukunci kenan?
Kai ta saukar ƙasa. Shi ya yi ta jan hirar ba tare da ya matsa mata ba. Goma saura ya miƙe zai tafi. Har mota ta raka shi. Ya shiga ya bar ƙofa a buɗe ƙafarsa ɗaya a waje.
"Na gode sosai Sa'adatu. Words cannot express my gratitude."
Godiyarsa ta fara yawa kuma. "Dan Allah ka bar gode mun hakanan."
Zubair ya yi dariya. "Toh Amarya duk yanda ki ka ce. Ni zan koma. Sai da safe."
A daren Umma da murmushi a maƙale fuskarta ta yi bacci.
•
•
•
•
•
Oldies love🤭😍
Assalamu alaikum Jama'a! To ya ku ka ji babin nan?🤭
Na so in update uku amma bai yiyu ba. Sha wannan babin is extra loooong so it should count as three😆
Baƙon da mu ke ta jira ya iso🥹🤲🏽💕
*اَللّٰهُمَّ بَلِّغْنَا رَمَضَانَ*
Ya Allah ka sa mu ci moriyar watan nan mai alfarma, Ka sa muna cikin bayan da za Ka ʼyanta daga wuta. May we all witness Ramadan and may it be transformative for us. May all the good akhlaqs we develop stay with us for the rest of our lives, and may the sins we abandon stay away forever
Ameen🤲🏽💕
Dan Allah kar mu yi sakaci ko sakwan ɗaya ya wuce mu a watar nan ba tare da mu amfana da shi ba.
Daga ƙarshe ina roƙon kowa ya saka ni a addu'a🥹🤲🏽💕 dan Allah ku saka Maymunatu Bukar a addu'a kun ji.
Ma'asalam
Sai mun haɗu bayan sallah in muna da rai da lafiya.
~Maymunatu Bukar💕
Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro