Chào các bạn! Vì nhiều lý do từ nay Truyen2U chính thức đổi tên là Truyen247.Pro. Mong các bạn tiếp tục ủng hộ truy cập tên miền mới này nhé! Mãi yêu... ♥

25.




Hankalin Maryam ya tashi sosai da ta ji abunda ya faru. Ba ta iya zama ba sai ta je gida. A matsayinta na babba ta samu Idris ta mai fada sosai sannan ta koma nasiha.

Ta ƙi jinin shaye-shaye. Ko taba taga mutum na sha tana jin wani irin bacin rai. Taya da kanga za ka sha abunda zai ɓata maka rayuwa.

Ƙwaya da kayan maye na ɗaya daga cikin abubuwan da su ke saurin ruguza rayuwar mutum. Kuma an fi samun haka cikin maza.

"Idris ka rufawa kan ka asiri wallahi wannan ba hanya me bullewa ba ce. Ni ganau ce ba jiyau ba akan illar ƙwaya. Wani dan ajin mu tun aji ɗaya ya ke jan first class. Abu ne me wuya a ABU musamman biochem amma haka yaron nan har mu ka zo final year. Kwasam ya faɗa shaye shaye. Ya daina zuwa aji, ko test ɗaya be yi ba. A haka har mu ka fara jarabawar wancan semestet ɗin. To be zuwa aji be san komai da a ka yi ba dole ya shigo da satar amsa. Cikin rashin sa'a invigilators su ka yi ram da shi. Dama neman yanda za su kada shi su ke yi sai gashi ya kawo kan shi da kan shi. Wallahi a take a ka cike mai form sai kora. Ko ɗaga ƙafa ba su yi mai. Shikenan fa duk ƙoƙarin da ya yi a baya ya tashi a banza.

Idris mu riƙe maraicin mu dan Allah mu bi duniya a sannu. Wallahi babu komai cikinta sai ƙyale ƙyale. Ba mu kyautawa kan mu ba idan mu ka bi hanyar da ba daidai ba. Ba mu kyautawa Abba. Sannan uwa uba ba mu lyautawa Umma ba. Kana ganin irin faɗi tashin da ta ke yi a kan mu. Shin mun kyauta mata idan mu ka saka mata ta hanyar da bata ɗace ba.

Kuma kar ka manta kai ne babba namiji Idi. Nan gaba kai za ka maye mana gurbin Abba. Shaye-shaye wallahi ba abun yi bane. Ko ka tuba tabon nan ba zai taɓa barinka ba har ʼyaʼya da jikoki. Kafin ma a kai kan ʼyaʼya ko kafin ka yi aure sai ya taso ko da kuwa ka tuba. Balle malam bahaushe be iya mantuwa ba. Har mu sai ya shafa Idi."

Idris ya yi kuka sosai ya yi mata alƙawari ba zai taɓa faɗawa hanyar nan ba. Maryam ta rungume ƙaninta tana kuka itama. Dole su riƙe maraicinsu. Yanzu sai a ce dan baya da uba ne. Kallon da a ke musu kenan ʼyaʼyan mace babu uban da ke tsawatarwa. Mutanen mu na manta cewa uwa ita ke da kaso mafi tsoka a tarbiyar yara. Yara nawa ne da ubanin na su amma su ka lalace.

Sai Monday da sassafe ta koma makaranta. Safiya, Zee da Bashir ba su san me ya faru ba. Baba Malam ya ce kar a sanar da su. Ko su Anti Jamila ma ba su sani ba.

Idris ya tsorata sosai sannan duk nasihun da a ka mai sun zauna daram a kansa. Ya karɓa hukuncinsa hannu bibbiyu. Idan ya tuna da hawayen Umma sai ya ga kaman an yi mai sassauci. Ko sannu bata sake haɗa shi da yaran ba har su ka gama NECO kowa ya kama hanyar shi.

***

Ƙarfe biyar na yamma a garin Kano ta yi wa Khalid. Ya daɗe be je gida ba dalilin sauyi da a ka samu na ma'aikata wurin aikin su. Yana da buƙatar ya zauna da Mama da Ya Ramlah batun maganar Maryam.

Babban burin shi a yanzu bai wuce Maryam ta zama matarsa ta sunnah ba.

Ya ci sa'a Ya Ramlah ta gudo weekend da yaranta wai mijinta ya yi tafiya. Ya ji daɗin hakan dan a lokaci ɗaya ya ke son yi musu magana.

"Ammar kawo mun ruwa." Ya ce da yaron da ya zama saurayi yanzu. Girman mutum ba wuya duka yaushe yaron ke mai kyuya yanzu har ya girma.

Mama ta ji daɗin ganin Khalid dan itama da maganar da ta ke so su yi mai muhimmanci.

Washegari da safe Khalid ya shigo falon Mama ɗauke da sallama. Bayan gama cin abinci ya tanƙwashe ƙafa yana kallon su.

"Akwai yarinyar da mu ka sasanta da ita. Mun fahimci juna sosai har ta bani dama in turo magabatana."

Ya Ramlah ta kalli Mama da wani abu a fuskarta da Khalid be fahimce na menene ba. Mama bata kalli Ya Ramlah ba duk da tana jin nauyin kallonta.

Shiru ba su ce komai ba har tsoro ya darsu a zuciyar Khalid. Me yasa su ka yi shiru kaman ya yi magana da wani yare daban.

"Mama..."

"Khalid tun yaushe ka ke tare da wannan yarinyar? Ya sunanta? Ya a ka yi ba mu santa ba?"

Be san dalili ba amma sai ya ji ba zai iya faɗa mata tun yaushe ya kamu da son Maryam ba. Yanda su ke yi be gamsar da shi ba. "Shekara ɗaya muna tare yanzu. A ABU na haɗu da ita."

Sai a sannannYa Ramlah ta yi magana. "Shekara ɗaya har ya isa ka santa har ka tabbatar ita ka ke son ƙarashe rayuwarka da ita."

Gira ya daga mata. Ta manta haɗuwarta da Baban Ammar da wata uku a ka saka musu rana kenan. Kaman ko ta san me ya ke tunani, "wancan daban."

Au Allah? Be de ce mata uffam ba sai ita da ta cigaba da ƙoƙarin kare kanta.

"Akwai ʼyar gidan abokin aikin Abbanka Musa da na ga ta dace da kai har na faɗawa iyayenta za ka zo ku sasanta."

Maganar Mama ta isa kunnuwan sa kamar saukar aradu. Da sauri ya kalleta mamaki ƙarara a fuskarsa. "Mama?"

"Eh Khalid. Ka ji abunda na ce. Saboda haka ka je yau ku gaisa."

"Ta ya zan ce miki akwai wanda mu ka daidaita sannan ki ce in je wurin wata mu gaisa?"

"Rashin kunya za ka mata Khalid saboda mace." Ya Ramlah ta hayyayaƙo kaman ya yi wani gagarumin lefi.

Menene rashin kunya a cikin zancen da ya yi? Musa abokin kasuwancin Alhaji ne da su ka haɗu ba da dadewa ba. Har yaushe Mama ta san su ita ba hudɗa ta ke yi da kowa ba. A take alamar tambaya ta hau kan zancen.

Ze gano bakin zaren.

Washegari ya shirya domin zuwa gidan Musa kaman yanda Mama ta buƙata. Har ƙasan ransa ba son zuwa ya ke yi ba. Amma ta dage ta haƙiƙance wanda ya ƙara tabbatar mai akwai me zugata daga gefe. Tarihin gidan kaf babu wanda a ka taɓa cewa ga wata su je su sasanta. Me yasa sai a kan shi?

Baya da wani aboki a garim Kano dan haka shi kaɗai ya je. Mintin shi biyar a waje wata budurwa ta fito sanye da atamfa da gyale kan ƙafaɗarta ko arziƙin rataya be samu ba. Fuskar ta sha kwalliya jan bakin ja kaman gyalenta. Kayan jikinta kuwa kaman da allura a ka ɗinka su.

Wannan ce Mama ke cewa sun dace? Wannan ɗin?

"Ya MK! Sannu da zuwa! Bismillah mu shiga ciki."

Khalid ya bita ciki su ka shiga wani falo daga waje daga gani na maigidan ne.

"Ina zuwa," ta ce sannan ta fita. Bayan wasu yan mintina ta dawo dauke da tray ta ajiye kan teburin da ke gaban shi.

Ta koma zata rufe ƙofar falon ya yi saurin dakatar da ita. "Da kin bar ƙofar a buɗe."

"Wai dan kar a dame mu."

"Ba damuwa."

Kafaɗa ta daga amma duk da haka saida ta dan sakayata. Kujerar da ke gefensan ta zauna shi yana kujerar mutum ɗaya da ke falon.

"Sannunka da zuwa Ya MK. Ina ta kallon hanya tunda a ka ce zaka zo sai yau."

Khalid ya jinjina kai. Ta san abunda a ke ciki kenan. Wanene ya kirata ya faɗa mata ze zo?

"Naja'atu ko?"

"Ya MK," ta ce da wata shagwabar da Khalid bai san daga ina ta fito ba. Kuma ma waye ya faɗa mata a na kiransa MK. "Ka kira Naj, dan Allah. Naja'atu sai ka ce wata ʼyar ƙauye."

Ikon Allah! Allah Ya kawo shi shi kam.

"Ya makaranta? Ya kowa da kowa?"

"Duk suna lafiya. Mama ta tafi biki da kun gaisa, Abba kuma yana kasuwa."

"Wani course ki ke studying?" Ya tambaya dan shi be san me ze ce mata ba.

ʼYar dariya ta yi tana rufe baki. "Mama bata faɗa maka bana makaranta ba?"

"Ba kya makaranta? Ba ki da lafiya ne?"

"You're so funny."

Maganar ta bashi haushi. Menene abun ban dariya cikin maganar da ya yi?

"Kawai banda ra'ayin karatun ne. Na fara BUK naga ina! Ba zan iya ba. Wahalar ta yi yawa kan kwalin da baya da wani amfani a ƙasarnan yanzu. Business kawai zan fara tunda dan me a ke karatun? Ba dan a samu aiki a yi kuɗi ba? Bare yanzu ma sai ka gama makarantar ba ka samu aikin ba. Kaga ka sha wahala a banza."

Ikon Allah! Tabbas Allah Ya kawo ka MK. Ya faɗa a rai. Ya rasa abunda ze ce. Gyaran murya ya yi, "wani business din kike yi?"

"Ban fara ba tukun ai. Ina dai tunani. Suma businesses din ne wahala wallahi. Neman wanda zai kawo mun kuɗi a sauƙaƙe na ke yi."

Idan ya hasaso da kyau, shekarunta ba za su wuce ashirin ba. Sa'aninta na ajin ƙarshe a jami'a ita tana zaune a gida saboda bata son ta sha wahala. Iyayenta na kallonta kuma su ka kyaleta. Lallai!

Duk kalmar da ke fita daga bakinta na sake tabbatarwa da MK sam basu dace ba. Ko da kuwa babu Maryam wannan yarinyar ba zata taɓa jan ra'ayinsa ba har ya ji yana sonta.

"Muna ta magana a kaina, ya aiki? An ce mun kana aiki a Jigawa."

Yana son ya san wanene ya ke faɗa mata abubuwa a kansa. Daga gani ba yanzu ta sani ba shi kuwa sai jiya ya san da zamanta.

"Eh haka ne. Na samu hutu ne na zo gida."

"Hakan yana da kyau. Idan mun yi aure Jigawar za mu zauna kenan?"

Khalid ya yi turus yana kallonta. Dariya ta yi cike da borin kunya ta maza ta chanza maganar.

Ita ta yi ta zancen shi de sai ta ya gyada kai ko ya fada wasu yan kalmomi ta cigaba. Agogon da ke hannusa ya kalla. Ya kamata ya kama hanya amma kafin ya tafi dole ya faɗa mata gaskiya.

"Naja'atu."

"Kai Ya MK! Call me Naj please!"

Share shirmenta ya yi. "Na san an faɗa miki dalilin zuwa na. Ban san da wannan shirin ba sai jiya. To tell you the truth ina da wanda na ke so kuma magana ta yi nisa saboda haka ina me baki haƙuri amma wannan abun ba ze yiyu ba."

"An daura mu ku aure?"

"Mene?"

"Ya MK tunda ba a daura aure ba ai shikenan. Kai ko da auren ma ni banga wata matsala ba. Kai dai ka bani chance sai na ture wancan daga zuciyarka."

Khalid bai san sanda ya fashe da dariya ba. "Ban iya boye boye ba. Ba zan bata mi ki lokaci ba alhali na san gaskiyar lamarin. Ina miki fatan alkhairi Allah Ya haɗa ki da wanda zai so ki kamar yanda na ke son budurwata. Sai anjima."

Bai jira amsarta ba ya fita. Yana isa gida ya samu Ya Ramlah a ɗaki tana kwance tana latsa waya. Tana ganin shi ta miƙe zaune. "Khalid har ka dawo? Ya ya ku ka yi da ita?"

"Tun wuri ku faɗawa Alhaji hanyar nan ba mai bullewa ba ce gwara ya nemo mafita. Banga dalilin kawo ni cikin maganar da ban san da ita ba."

"Ya a ka yi ka sani?" Ya Ramlah ta ce da mamaki.

Khalid ya yi dariya cike da takaici. "Na sha faɗa miki duk gidan babu wanda ya san halin Alhaji kaman ni."

Cikin surutan Naja'atu ya gano babanta na bin Alhaji kuɗi. Duba da dabi'un yarinyar babu mamaki iyayenta na neman yanda za su aurar da ita su huta. Babu shakka Alhaji ya bada shawar haɗin dan a kawar da zancen bashi.

Duka wannan hasashe ya ke yi amma zai gano gaskiyar zancen nan ba da daɗewa ba.

"Khalid mana..."

Ya kalla yayarsa cike da mamaki. Magiya ta ke yi mai ya yarda? Wannan wani irin son kai da zuciya ne. Shikenan kullum duk wata matsalar mahaifinsu a kan sa zata ƙare?

"Ya Ramlah kenan. Annabi ya ce ka so wa dan uwanka abunda ka ke so ma kan ka. I'm not even hurt kin yarda I'm disappointed. Gidan nan ina sha banda kamar ke amma kullum kina nuna mun ba ki da banbanci da sauran. Da ni na kasance a wurinki sai inda ƙarfi na ya ƙare wurin ganin ba a tauye miki haƙƙi ba amma sadly you can't do the same for me. Kullum sai da ki ce in yi haƙuri, in yi hakuri. Haka maganar aikina you couldn't stand up for me. Ko so ɗaya ba ki ce komai ba. Amma ba komai."

Ya juya zai fita ta riƙo mai riga. "Dan Allah Khalid. Wallahi Musa ya ce idan bai yarda ba kotu zai kai shi kuma Abba bai da kuɗin da ze biya."

Ta tabbata bashin ya ci kenan.

Khalid ya juya a fusace ransa na ƙuna. Yau da Alhaji ya kasance uba na gari da babu abunda zai hana ya taimake shi.

"Da sani na ya ci bashin? Ko ni na yi amfani da kuɗin? Duk yaran da ke gidan me yasa sai ni?"

Ba sai an faɗa ba saboda yana da abun yi ne. Karatun da babu wanda ya san yanda a ka yi ya gama shi. Tun aji ɗaya Alhaji bai sake biya mai kuɗin makaranta ba. Tutorials da yi wa mutane project ne su ka riƙe shi har ya gama. Tun yana level 2 ya ke wa ʼyan final year project. Nas kaɗai ya san da haka. Bai faɗawa Mama da Ya Ramlah ba dan ya san babu amfani.

Alhaji be san karatun nada amfani ba sai yanzu? Aikin da a ka so hana shi shima yanzu a ke neman a ƙaru da shi.

"Ku sani babu wanda zai sa in auri yarinyan chan da bata san ciwon kanta ba. Idan aure ne shi ya aureta mana, ba yau yafara auren sa'anin yaransa ba ai."

"Khalid!"

"Kar ki yi mun ihu Ya Ramlah! I have had enough! Na gaji! Na gaji da rayuwar gidan nan! Wace irin rayuwa ce kullum abu ƙara tabarbarewa ya ke yi. Ba zan zaman muku scapegoat ba. Ba zan ɓata rayuwata sabo in faranta muku ba when no one is willing to do the same for me!"

A matuƙar fusace ya bar wurin ransa na tafarfasa yana ƙuna. Wace irin rayuwa ce wannan? Da sauri ya miƙe zaune daga kwanciyar da ya yi saboda lumfashinsa da ya ke neman ɗaukewa.

Ya rasa inda ze saka ransa ya ji sanyi. Kaman ya fashe da kuka. Wace irin rayuwa ce wannan? Iyayensa na raye amma jinsa ya ke tamkar maraya. ʼYan uwansa sun fi goma amma ji ya ke tamkar shi kaɗai ya zo duniya.

Jakarsa ya buɗe ya ciro ƙaramar jaka inda maganin shi ya ke da likita ya rubata mai kwanakin baya da ya yi mura. Akwai wanda ya ke saka shi barci. So ya ke yi ya manta duk abunda ya faru yau ko da na wani lokaci kaɗan ne.


***

"Hello Babe? Kina ina ne?" Khalid ya tambaya riƙe da wayarsa yana kallon dalibai da ke kawo cikin makaranta.

"Ina lab amma yanzu zan gudu na gaji wallahi."

"Maryam," ya yi dariya. "Kullum cikin guduwa ki ke yi. Wani lab din? Na Biochem ko micro?"

"Micro. Na gama ai. Na yi serial dilution zan bari su yi incubating."

Suna magana ya taka daga inda ya ke gaban Biochem zuwa Micro. Babu tazara nan da nan ya iso.

Yana tashi yau da safe ya ce zai tafi. Duk sanda ya fara kewar gida yana zuwa za a tuna mai dalilin da yasa baya zuwa. Mama ta yi ta faɗa. Sam Khalid yanzu bai gane mahaifiyarsa. Ta chanza gaba ɗaya. Kaman an ɗauko wata an ajiye a wurin.

Ya Ramlah ba ta ce komai ba sai addu'ar Allah Ya kiyaye. A yanda ransa ya ɓace da ta yi magana sai sun yi faɗa.

Mutumin da ya haɗa husumar har ya taho be gan shi ba. Yana isa tasha ya tsinta kansa da shiga motar Zaria. Ganin Maryam ne kaɗai ze fidda shi daga bakin cikin da ya ke ciki.

Yana tsaye ta fito sanye da labcoat wayarta a kunne tunda har yanzu magana su ke yi.

"Jakarnan ta yi miki nauyi ai."

Da sauri ta waiga har ta gansa tsaye jikin wata mota. Take wani kyakyawan murmushi ya mamaye illahirin fuskarta. Murnar ganin shi da ta yi kaɗai ya isa ya wanke duk wani bacin rai da ya taho shi.

"Kai da ka ke Kano!"

Dariya ya yi, "na yi missing baby na dole in taho."

Murmushi ta yi ta dauke kai. Yana son kunyarta. Wani lokaci da gangan ya ke yi dan kawai yaga kayataccen murmushin nan.

Hannu ya sa ya karɓa jakar su ka jera suna tafiya tana faɗa mai yanda ta ke ciki da labwork ɗinta.

Mutane da yawa sun tsaida shi dan a gaisa.

"MTN ba, everywhere you go."

Khalid ya fashe da dariya. "Toh ya zan yi. Mutane ai rahama ne."

"Tabbas amma na ka yi yawa, ba mu taku biyu sai wani ya tsaida ka."

Tana rufe baki wani dan department din su kuwa ya kira sunan shi.

"Ka gani ko," ta ce tana dariya bayan sun yi gaba.

A gaban hostel ya jirata ta je ta chanzo kaya. Bata daɗe ba ta dawo.

"Ina za mu je? Frizzlers ko pepsi?" Ya tambaya.

"Mu je pepsi na kwana biyu ban ci shinkafar su da hadadden salad ɗinnan ba."

Khalid bai bar Zaria ba saida Maryam ta wanke masa zuciya tas ba tare da ta sani ba. A haka kuma a ke nema a kawo mai wata cikin rayuwa bayan ga wanda ke faranta mai rai.

Ina! Hakan ba ze yiyu ba!







When I start a book na san inda zamu amma ban san hanya ba. Kaman zani Daura ne, ban san ta Kano zan bi ba ko ta Katsina😂

Toh dai ga mu nan. Har ga Allah ni kaina I didn't see this coming🙆🏻‍♀️ mu cigaba da bin hanyar nan ko mu bi wata?😂

And my sincere apologies for taking so long. Ku yi haƙuri.

Also, this is for the sister I met yesterday at Deensisters🫶🏽💕

~Maymunatu Bukar💕

Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro