Chào các bạn! Vì nhiều lý do từ nay Truyen2U chính thức đổi tên là Truyen247.Pro. Mong các bạn tiếp tục ủng hộ truy cập tên miền mới này nhé! Mãi yêu... ♥

24.





Saboda tsabar kallon computer idanunta har ruwa su ke yi. Kyaftawa ta yi saboda ta fara ganin dishi-dishi. Ta kai awa huɗu a zaune ko motsi bata yi ba. Wuyarta ta ƙage, bayants ya riƙe. Dole ta nema ko aboniki ne ta shafa, ta san ba zata rasa shi ba cikin akwatin taimakon gaggawa da ke gida.

Turo ƙofar ofis ɗinta a ka yi wata ma'aikaciyar asibiti ta shigo ɗauke da wasu files ɗin.

Umma ta girgiza kai. "Laurat ba dai wasu ki ka ƙaro mun ba. Wancan ko rabi ban yi ba fa."

Laurat ta yi dariya. "Yi haƙuri ma, amma dakwai saura ma ban gama sorting ɗin su bane."

Umma ta jinjina kai. Lallai bature ya yi gaskiya da ya ce 'with more power comes more responsibility' Watanta shida da samun muƙamin Head Nurse a maternity unit. Nos ɗin da ta sauka sam ba ta yi aikinta ba. Har yau Umma Sa'adatu bata daura sabon aiki ba saboda gyara da wancan ya ke buƙata. Musamman records ɗin marasa lafiya. Dalilin da Laurat ke ajiye mata tulin files kenan.

"Sauran ki bar su sai gobe Laurat," Umma ta ce tana kallo agogo. Huɗu ta kusa, yau a kan lokaci ta ke so ta koma gida.

"Yes Ma." Laurat ta amsa sannan ta fice.

Umma ta lumfasa sannan ta koma kan aikinta. Ƙarfe huɗu kamar yanda ta yi niya ta miƙe daga kan kujerarta. Banɗakin da ke cikin ofis ɗinta ta shiga ta yi arwala. Bayan ta idar da Sallah ta sanya babban hijabinta ta sabi jakarta ta yi gaba.

Wurin ajiye motar da a ka tanada musamman dan HN ta ajiye motarta. Key ta danna motar ta yi ƙara tare da yin haske. A kujerar me zaman banza ta ajiye jakarta sannan ta tayar da motar.

Bata haɗu da cunkoso ba da ta fito daga asibitin. Cikin loƙaci ƙalilan ta isa gida.

Idris da abokansa ta iske suna kwallo a layi. Yana ganin motarta ya ruga ciki ya buɗe get din. Umma ta danna kan motar ciki ta ajiyeta kusa ta tsohuwar motarta wanda a yanzu ta zama ta Baba Malam.

Idris na haki duk ya jike da zufa ya buɗe mata ƙofa. "Sannu da zuwa Umma."

"Malam Idi kenan. Sana'ar ce a ke yi."

Ya yi dariya ya amsa jakarta. Tsawon yaron har tsoro ya ke bata. Shekara sha shida amma tsawonsa kaman falwaya. Ya fi kowa tsawo a gidan, ita da Maryam dama ba a magana dan tun tuni ya fara hango tsakiyar kan su.

Gidan shiru babu kowa a tsakar gidan. "Ina su Mama?"

"Duk suna ciki," Idris ya bata amsa.

Kamar yanda al'adarta ta ke, saida ta je ta gaida iyayenta sannan ta nufi nata sasahen. A falo ta samu Zee da Bashir suna kallo. A gurguje ta shirya zata je walimar wata ƙawarta da suka koyar tare a makarantar yaran lokacin. Itama bazawara ce Allah Ya kawo mata mijin aure.

A hanya Maman Hamida ta kirata tana tambaya idan ta fito ita ta daɗe ta isa. Minti talatin Umma Sa'adatu ta nema wuri ta ajiye motarta.

Gidan cike ya ke da jama'a. Sashin mata biyu ne a gidan, Umma ta isa sashen mahaifiyar ƙawarta inda a ke bikin tarewarta.

Ita da Rakiya sun yi koyarwa tare a makarantar su Maryam shekarun da su ka wuce. Ko bayan barinta aiki, ƙawancen su na nan.

A tsakar gida ta samu Maman Hamida da sauran matan da a ke gaisawar mutunci da su. Kusa da Maman Hamida ta zauna sanna a ka gaisa.

"Anty Nos, kin samu kin iso." Ɗaya daga cikin matan me suna Ladidi ta ce.

Umma ta yi murmushi. "Wallahi. Da kyar na ƙwato kaina, na san Rakiya ba zata kyale ni ba idan ban halarci taron nan ba."

Hakane kuwa." Muryar amarya Rakiya ta fara bayyana kafin ita.

Ta ci ado cikin leshi kore da sha aikin sirfani. Rakiya bazawara ce da Allah Ya yi wa mijinta rasuwa shekara huɗu da su ka wuce. Umma Sa'adatu ta tayata kuka a lokacin da mai gidanta ya rasu dan ita kaɗai cikin ƙawayen na su ta san zafin rashin abokin zama.

Nan a ka sake sabuwar gaisuwa sannan a ka hau tsokanar Rakiya ana ce mata amarya ta sha ƙamshi. Ta yi fari da idanu tana ta murmushi.

"Saura ke Sa'adatu. Mijin Rakiya ya kamata ya haɗa ki da abokansa zaurawa." Cewar Ladidi.

Nan kowa ya nuna goyan bayan maganar Ladidi. Umma dai dariya kawai ta yi. Aure ba shi bane a gabanta.

"Shekara kusan goma ba ki gaji da zama a haka ba Sa'adatu. Dan Allah ki daure ke ma ki yi auren nan kin ji. Zaman haka babu daɗi."

"Allah Ya tabbatar." Umma ta ce tana son katse maganar dan kar ta yi tsawo.

Ba yau ta fara jin zancen nan ba. Har ta haddace abunda su ke cewa, kar ma Mama ta ji labari. Akwai ranan da ta ce mata ga ƙasa nan ta ƙera Ahmad ya dawo. Maganar ta yi mata ciwo, kwana ta yi tana kuka. Ta san Ahmad ba zai taɓa dawowa ba, ita ba jahila ba ce da zata ƙi karɓan ƙaddararta ba.

Sun kasa fahimtar maza ba su gabanta. Duk cikin wanda su ke sallama da ita babu wani da ta ke jin zata iya rayuwa da shi. Ita ta san ko ta ƙara aure ba zai taɓa samunta dari bisa dari ba dan wani bangare na zuciyarta da ruhinta yana tare da Ahmad har abada.

"Kun ga ku kyale mun ƙawa. Komai ai na Allah ne. Allah me lokaci." In ji Maman Hamida.

Kamar yanda ʼyaʼyan su su ke aminai haka ya ke tsakaninsu. Maman Hamida ta san yanda Umma ta ƙi jinin maganar aure.

Daga nan a ka bar zancen a ka dauko wani. Suna nan har ƙarfe biyar da rabi inda yan uwan Rakiya maza su ka kaita dakinta. Ana daukar amarya taro ya watse. Umma na sahun gaba a wanda su ka fara tafiya.

A bakin motarta su ka yi sallama da Maman Hamida. Cike da zolaya ta kalli Umma. "Ko dai bazawarin zan nemo miki dagaske?"

Umma ta kwashe da dariya. "Allah Ya yaye miki Fatima. Ni kinga tafiya ta."

Maman Hamida ta yi dariya, "ki gaida mun su Baba Malam da yarana. Kwana biyu ban shigo ba."

"Za su ji."

A hanyarta ta komawa gida maganar su Ladidi na yi ta mata yawo a kai. Ganin maganar na neman saka mata ciwon kai ta yi saurin ƙawar da zancen daga ranta.

Da dare tana aikin duba filea wayar Safiyya ta shigo. Bayan sun gama gaisawa Safiyya ta fara yar murya. Umma ta san cewa za ta yi kuɗinta ya ƙare. Ta rasa me ta ke yi da kuɗi. Sam babu tattali a lamarinta. Bini-bini Umma kuɗi na ya ƙare. Maryam ko har mancewa ta ke yi da ita sai idan ta tuna da kanta ta tura mata.

"Umma kina ji na?"

"Ina jin ki Safiyya. Kuɗin ne ya ƙare?"

"Umma ya a ka yi kika sani?"

Umma ta girgiza kai. Safiyya kenan, dukkan su babu wanda bata san halinshi ba. "Ki dan saurara dan babu kuɗi a hannuna."

"To Allah Ya kawo su da wuri masu albarka."

Umma ta yi dariya. "Da ya ke kina so dole ki ce da wuri ai. Ina yayar ki?"

"Tana da test gobe ta tafi aji."

"Allah Ya taimaka. Ke me yasa ba ki je ajin ba?"

"A ɗaki na ke karatun."

"To, a dai dage. Ki san abunda ya kai ki. Banda biyewa ƙawaye Safiyya."

Tarin ƙawayen yarinyan na damunta musamman yanzu da ta tafi jami'a inda za ta haɗu da ko wani irin mutane.

Tarbiyar yaranta abu ne ta ke takatsatsan sosai a kai. Ita ce uwarsu ita ce ubansu dole ne ta dage ta tashi tsaye kan su musamman yanzu da zamani ke zuwa da sauye-sauye da ba al'adar mu ba da ke bada gudunmawa wurin lalacewar tarbiya.

A kullum addu'arta Allah Ya shirya mata su, sannan Ya taimake ta wurin basu ingantaciyar tarbiya. Ba wayo, dabara ko iyawarka ke shirya yaro ba, Allah ne.


***

Yau ma files ɗin ta duba a wurin aiki. Ta rasa me tsohuwar HN ɗin ta yi. Mutanen mu na son muƙami amma ba mu son yin aikin da muƙamin ya ke zuwa da shi. Kaso sittin cikin ɗari na aikin da ya kamata ta yi duk ba ta yi ba. Sai ma rubuta request ɗin kayan aikin da ba a buƙata da ta yi sosai. Gashi dai a rubuce kayan aiki sun iso ta saka hannu amma babu su a ma'ajiya babu alamar su.

Najeriya muna da sauran aiki. Kullum cikin zagin shuwagabanni mu ke amma mu ʼyan ƙasa ba mu ganin laifin abubuwan da mu ke yi.

Da sauri wata nos ta faɗo mata ofis. "Ma, an kawo wata emergency nos on call ba su nan."

"Ba su nan?" Umma ta tambaya cike da mamaki tana kallon agogo da ke maƙale jikin bango.

"Yes, Ma. Babu ko ɗaya, ʼyan night duty kuma sun tafi."

Ga irin abunda ta ke cewa. Ba shuwagabanni kaɗai ke da sa hannu wurin gurbacewar ƙasa ba, kowa yana da kamasho.

"Mu je, mu je." Umma ta ce tana miƙewa.

Aikinta na matsayin Head Nurse ya fi karkata kan aikin ofis ba ta cika yin duty ba sai idan an samu a ka si irin haka.

Ta samu matar da a ka kawo cikin mawuyacin halin naƙuda. Tun shekaran jiya ta fara naƙudar duk ta galabaita. Ba su kawota asibiti ba saida abu ya yi tsanani. Da wani abu ze sameta yanzu sai a ce laifin ma'aikatan asibiti ne bayan sun barta a gida suna neman lahanta ta tare da ɗan da ke cikinta.

Nan da nan a ka bata taimakon gaggawa. Likitar tana gani ta ce dole a yi mata CS dan ta galabaita bata da ƙarfin pushing.

Nan a ke yinta danginta sun ƙi saka hannu a yi mata aiki. Umma ta yi musu bayani iya bayani sun ƙi sauraronta bare su fahimce ta. Gasu dai kaman mutanen kwarai masu hankali a tsaye amma jahilai ne na ƙin ƙarawa. Wasu dalilan na su na ƙin yarda sun ƙonawa Umma rai. Ashe har yanzu akwai masu irin tunanin wai CS kashe mutum kawai ya ke yi?

"To bayin Allah sai dai ku ɗauketa ku kaita wani asibitin ko ku koma inda ku ka fito. Mun faɗa mu ku abunda ta ke buƙata kun ƙi fahimta. Ga ʼyar ku chan ba mu taɓata. Zan saka a kawo wheelchair a kai ta mota."

Jin haka ya sa wani namiji a cikinsu wanda ta ke tunanin shine mijin ya saka hannu. An yi aiki lafiya a ka ciro yarinya. Sai da a ka yi wa uwar ƙarin ruwa da jini.

Bayan an gama wannan Umma ta baro ɗakin tiyata inda ta ci karo da noses din da ya kamata a ce sun zo wurin aiki awa shida da su ka wuce. Suna ganinta ta fito su ka sha jinin jikin su.

"Ku same ni a ofis." Abunda kawai ta ce musu kenan.

Bayan ta kimtsa ta sha ruwa ta hau su da faɗa. Kowa ya santa bata wasa da aiki. Tana da sauƙin kai da faran-faran amma muddin ka saɓa doka za ku bata. Saida ta yi musu tatas kafin ta ce su barta mata ofis sannan su jira query ɗin su.

Wayarta ta yi ƙara tana dubawa ta ga principal ɗin makarantan yara. Ko me yasa principal ke kiranta? Allah dai Ya sa lafiya. Ta amsa sun gaisa tana jira ya ce mata ɗaya daga cikin yaran ba lafiya amma sai ya ce mata a na buƙata yanzu yanzu ta zo makaranta.

Ya barta tana ta tunani har ta isa makarantar. A ƙofar ofis din ta ga Idris da sauran yara a jera sun sa gwiwowi a ƙasa. Take gwiwarta ta yi sanyi. Ta iske maza huɗu a ofis din bayan principal ɗin.

"Barka da zuwa Maman Idris," Principal ɗin ya ce da turanci. "Dama ke mu ke jira. Ga wuri ki zauna."

Zuciya na dukan uku uku Umma ta zauna. Duka sauran yaran iyayensu maza a ka kira, wani laifi su ka yi haka? Ko satar amsa ce tunda sun fara NECO?

Da Principal ya fara bayani Umma taso a ce mata satar amsar ce ba abunda ya ke faɗa ba. Ta kasa magana sai sauran iyayen ke ta bayani, ɗaya ya ce ƙarya a ke wa yaronsa.

"Kar ka ce haka Sir." Principal ɗin ya ce cikin laluma. "Ni da kaina na kama su. Kuma yaronka an sha kawo mun ƙaransa....."

Principal ya yi bayanin a halin da ya kama su a bayan azuzuwa. Ko wani uba ya tofa albarkacin bakinsa banda Umma da gaba ɗaya jikinta ya yi sanyi kaman an tsomata cikin ruwan ƙanƙara.

Umma bata motsa ba, ba ta ce komai ba har kowa ya bar ofis ɗin ya rage daga ita sai Principal.

"Maman Idris ba ki ce komai ba."

Umma sai ta buɗe baki sai ta maida ta rufe. "Ka ce ba yau ne karon farko ba?"

"No Ma. Idris ba a taɓa kama shi da laifin nan ba. Asali ma yaran ba abokansa bane kwanan nan ne na fara ganin su tare."

"Yaran halin ne kenan? To da ka gansu tare me yasa baka raba su ba ko ka kirani?"

Principal ya yi ƙasa da kai. "Eh toh. Ban yi tunanin wannan ba."

"Amma na ce maka ka sa mun ido kan yarana ko? Daga shi har kan Bashir ko me ka gani ka faɗa mun. Da ka faɗa wata kila da haka be faru ba."

"Hakane Maman Idris. Ki yi haƙuri."

"Yanzu me ye hukunci da za a mai? Ni ban yarda da abunda sauran iyayen su ka ce ba. Laifi ne dole a hukunta su, ko da shi kaɗai ne su idan ba su yarda a hukunta yaran su ba."

"Tunda suna jarabawa sai ranan da su ke da paper su ke zuwa. Hukuncinsa zai riƙa zuwa kullum ya karba punishment."

"Hakan ya yi."

Umma ta miƙe ta fita, Principal na binta a baya. "Tashi ka bi mamanka Idris."

Tsit ka ke ji har su ka shiga mota. Hannu na rawa ta murɗa mukullin, yana karkarwa ta ɗaura saman sitiyari.

"Umma...."

"Ka yi mun shiru Idris! Ka yi mun shiru!"

Idanunta yaji su ke yi saboda kwallar da ta tarun mata a ido. Cikin rahamar ubangiji su ka isa gida lafiya dan bata ganin gabanta da kyau.

A tsakar gida su ka iske Baba Malam da Mama tsaye da CSP Zubairu. Mama ta fara ganin su, da fara'arta ta fara magana sai dai ganin idanun Umma sun yi ja ga Idris a gefe fuska a tsorace ya sa ta ce, "Sa'adatu lafiya?"

Kiris dama ya rage. Sai kawai Umma ta fashe da kuka. Idris ganin mahaifiyarsa na kuka saboda dalilinshi ya sa shima ya fara kukan.

"Subhanallahi." CSP Zubair ya ce yana kama Idris.

Mama ta kamo Umma su ka shiga falon Baba Malam. Suna ta tambayar me ya faru amma an kasa samun wanda zai bada amsa.

"To kun sa mu gaba kuna kuka. Ku faɗa mana me ya faru mana." Baba Malam ya ce cikin faɗa.

Umma na shasheƙan kuka ta ce. "Sigari a ka kama shi yana sha a makaranta. Sannan an samu ƙwayoyi cikin jakunan su. Na shiga uku na lalace ni Sa'adatu! Wayyo Allah!"

Falon ya dauka salati su ka juya suna kallon Idris wanda da nasani da nadama sun gama lullube shi. Shi da ko zufa baya son ganin Umma na yi yau gashi a dalilinsa tana zubda hawaye haka.

Baba Zubairu ya ce ya dawo kusa da shi. Da ze iya maida hannun agogo baya da ya yi. Kusa da Baba Zubairu ya koma.

"Sa'adatu ki bar kuka dan Allah." Mama ta ce.

"Me zan yi idan ban yi kuka ba Mama. Shaye-shaye fa! Shaye-shaye!"

"Wallahi Umma yau ne kawai..."

"Ka yi mun shiru! Ba ka kyauta mun ba Idris. Ba tarbiyar da na baka kenan ba. Ba tarbiyar da na baka kenan ba. Allah ne shaidana.... Inna lillahi wa inna ilahi raji'un."

"Umma dan Allah ki yi haƙuri ki daina  kuka. Umma dan Allah."

"Maman Maryam ki yu haƙuri. Hawayenki masifi ne a gare shi. Ki daina kuka." Baba Zubairu ya ce.

Umma ta girgiza kai wasu hawayen na gangarowa. Ba su san ya take ji a zuciyarta ba. Ƙuna ta ke yi kaman an zuba mata garwashi. Me zata cewa Ubangiji? Ta kasa riƙe amanar marayun da ya barta da su. Wayyo Allah! Wayyo Allah!

Da kyar Umma ta saita kanta. Baba Malam ya yi gyaran murya. "Idris. Abunda Umman ka ta ce hakane?"

Idris ido a ƙasa ya daga kai.

Baba Malam ya yi ajiyar zuciya. "Faɗa mun me ya faru."

"Wallahi wallahi Baba Malam ban taɓa shan komai ba. Ɗayan ma yau ne kawai." Sai ya fashe da kuka. Baba Zubairu ya dafa mai kafaɗa. "Kar ka ji komai Idris. Faɗa abunda ya faru."

Kaman yanda Principal ya ce yaran ba abokansa bane sai kwanan nan. Yaro da kyale-kyale wani game da su ke zuwa da shi na kwallo ya ja mai hankali, daganan su ka kulla abokantaka. Ya ce be san abunda su ke yi ba sai daga baya. Kuma idan su na yi baya shiga cikin su sai yau ne ɗaya ya ce lallai sai ya gwada. Yana karɓa principal ya kama su.

Umma ta daina kuka amma hawaye na zubowa.

"Idris ka ga abunda ya sa a ke ce muku banda abokan banza. Da baka shiga cikin su, har ka fara, a ka ce ka gwada kaga daga nan kai ma ka zama ɗaya daga cikin su. Shaye-shaye na ɗaya daga cikin abubuwan da ke ɓata rayuwa...."

Idris yana kuka yana daga kai har Baba Malam ya gama Mama ta yi nata. Baba Zubairu kam addu'a ya yi mai. Jikin shi ya yi sanyi sosai. Tabbas kullum faɗan Umma banda biyewa abokai.

"Je ka ba Ummanka haƙuri." In ji Baba Zubairu.

Sai dai kafin Idris ya motsa Umma ta bar falon tana sake fashewa da kuka. Mama da sauri ta bita.

"Haba Sa'adatu. Menene haka? Ke kunnen ki kin ji be taɓa yi ba. Ke da za ki godewa Allah abun be tsananta ba shine ki ke kuka."

"Mama gani na ke duk laifi na ne. Kina ji fa wani abun buga game ne ya ja shi wurin su."

"Ko duk duniya ki ka tara ki ka ba yaro dole ze ga wani abu da ze bashi sha'awa a waje. Ni dai ki godewa Allah abun be yi muni ba an gano bakin zaren da wuri. Da a ce a chaji ofis a ka kira ki fa ko wani wurin mafi muni. Ki gode Allah a makaranta ne kuma abun be yi nisa ba."

Umma ta gyada kai. "Hakane." Har Mama ta kusan fita Umma ta tsaida ta. "Kema kina ganin saboda be da uba ne ko?"

Da sauri Mama ta jiyo. "Kash kash, ashsha Sa'adatu. Me ya kawo zancen nan kuma? Sauran yaran duka ba da ubannin su kika ce ba. Hakan ya hana su shiga cikin halin ne? Ƙaddara ce kuma tana kan kowa. Allah Ya ce zai jarrabe mu da dukiyoyinmu da yaranmu, yaran Be ce marayu kaɗai ba. Dan Allah ki daina wannan tunanin."

Kai kawai ta iya dagawa. Bayan fitar Mama ta sha kuka har zuciyarta ta dena radaɗi sannan ta yi arwala ta yi nafila. Ta daɗe a sujuda, bayan ta idar ta daga hannuwanta sama ta kai kukanta wurin Ar-Rahman me jin kan bayinSa, Allah ne gatanta, ta san kuma idan fa roƙe Shi ze amsa.

"Ya Allah. Ka na gani ina baki ƙoƙarina, Ya Allah na kawo kukana wurinKa, kai Ka ɗai Za Ka iya share mun hawayena. Ya Allah ga marayun nan, Ya Allah Ka shiryan mun da su, Ka albarkaci rayuwarsu, Ya Allah Ka kare mun su, ka bani ikon yi musu tarbiyya me kyau. Ya Allah Kai ne gatanmu Ya Rabbi Ka kula damu. Ya Allah Ka shirya mun su Ya Allah Ka kare daga faɗawa gurbataciyyar hanya."

Ta daɗe tana addu'a har sai da ta ji sanyi a ranta. Tabbas addu'a makamin mumini. Babu shamaki tsakanin Allah (SWT) da addu'a. Bawa ya daga hannu ya roƙa tabbas Allah (SWT) ze amsa.

A nan kan abun sallah bacci ya ɗauketa. Motsin mutum kusa da ita ya tadata. Tana buɗe ido ta ga Idris zaune kusa da ita ido duk ya yi ja. Tausayin shi ya mamaye ta sai ga hawaye.

Idris da ya sha har yanzu kukan fushi ta ke yi sai kuka shima. Umma Sa'adatu ta rungumo ɗanta tana dan bubbuga mai baya.

"Umma dan Allah ki yi haƙuri."

"Ya wuce Idris. Ka yi mun alƙawari ba za ka faɗa wannan rayuwar ba, ka taimakeni...."

Tana hawaye ta yi mai nasiha mai ratsa jiki, gana ɗaya ya yi sanyi. Ba yabon kai ba amma yaranta na da hankali duk da ƙarancin shekarun su.

Daɗinta ya kusa gama makarantar. Bata san inda Allah ze kai shi jami'a amma zata dage da addu'a.

Allah Ya bata ikon kula da ʼyaʼyan Ahmad.



Double Update🥳

Jama'a, me zai faru nan gaba?🤔

~Maymunatu Bukar💕

Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro