19.
Kaman wasa ta gama jarabawar first semester. Lokaci na gudu. Duka yaushe su ke ta shirin tahowa makaranta gashi yanzu har an kammala. A haka za ki ji an ce sun gama makarantar gaba ɗaya.
Maths din da bata yi ne jarabawar ƙarshe wa ʼyan aji ɗaya. Dan haka ita yau ta gama Hameeda da Sumayya saura musu ɗaya da za su rubuta jibi. Jibin jarabawar safe ce dan haka suna fitowa za su tafi. Ba dan ba dan ba da ta yi gaba amma ta san ta shiga uku wurin Hamida. Har duniya ta naɗe ba zata dena yi mata mita ba.
Ita kaɗai ce a ɗakin Hamida da Sumayya sun fita. A gajiye take dan haka ta hau gado dan ta runtsa sai dai baccin gaba ɗaya ya gujeta. Tsaki ta yi ta miƙe zaune sai kuma ta koma ta kwanta. Ko ba komai zata huta.
Sati ukun da aka yi ana exams gaba ɗaya bata san inda kanta ya ke ba. Ta yi karatu sosai saboda tana so ta fito da sakamako mai kyau, ko ba dan ita ba dan Abbanta da Ummanta.
Da yawan lokutta tana tunani ya rayuwarsu zata kasance da Abba bai rasu ba. Tasan zai fi kowa ƙarfafa mata gwiwa. Akwai jarabawan da ta shiga yi ta manta da duk abunda ta karanta. Haka ta yi ta kiran sunan Allah, chan sai ta ji murya kaman ta Abbanta tana bata baki. Daga ƙarshe dai ta amsa duka tambayoyin ko ɗaya bata tsallake ba.
Tana cikin wannan tunanin bacci ya yi awon gaba da ita sai jin muryar Hamida ta yi tana ce mata ta tashi ta yi sallar Maghriba.
Maryam ta yi miƙa tana kallon yanda garin ya fara duhu. Wai, tasha bacci. Arwala ta yo sannan ta yi sallah. Kan abun sallar ta ƙara kwanciya saboda har yanzu idonta akwai sauran bacci.
"Eh lallai Ya Maryam kin gama jarabawa," Hamida ta ce. "Baccin za ki koma? Kodayake ban ga laifin ki ba, ni da banda kwanciyar hankalin nan kin ganni nan ai ko gezau idona a bushe."
Maryam ta yi dariya. "Kema kin kusa samun kwanciyar hankalin yin bacci Hamida."
"Ke Maths dinnan abun tsoro ne. Calculus banzan course ne. Ni ban san me yasa mu ke yin shi ba."
"Tunda ki ka ga kuna yi yana da amfani mana. Sai nan gaba za ki gane hakan."
"Jiya naga course form dinmu na level two, kinga tulin Physics din da zamu yi? Na shiga uku ga MK ze yi graduating ya barmu. Gaskiya dole ya haɗa mu da wani kafin ya tafi. Amma anya akwai wanda zai koya mana karatu mu fahimta irin MK kuwa?"
Maryam ta gyada kai. Da wuya kam. Dan shi tsakani da Allah ya ke zama ya koyar da su. Kuma zai musu shi dalla-dalla kaman ʼyan nursery sannan baya taɓa yin gaba sai ya tabbatar da sun fahimta sosai.
"Dama ya yi bautar ƙasan shi a nan wallahi, kin ga shar da mu."
"Eh lallai Hamida. Sannu."
"Ke ba ki san yanda hankalina ya ke a tashe ba. Kinga tambayoyin ne wai? Ga shi ana ta cewa ʼyan Physics Department dinnan ba su da kirki."
"Ai kya bari ki gama da aji ɗaya tukun ki fara damuwa da abun aji biyu ko Hajiya? Ke da ko seconde semester ba ki fara ba balle aje maganan two hundred level."
"Abun ne da tsoro wallahi. Gwiwata ta fara saki da Chemistry dinnan. Kuma wai harda practical ake yi na kusan awa takwas. Ko me ake dubowa haka oho! Kuma 'yan Biochem an ce kuna yi."
"Ni dai ki barni haka dan Allah. Mutum ya gama exams ke kuma kin zo kin ɗaga mana hankali. Ke dai kawai ki yi addu'ar Allah Ya bamu sa'a."
Hamida ta gyada kai. "Hakane. Allah Ya taimake mu."
"Toh ko ke fa."
Ɗan sauran baccin da ya rage a idonta surutun Hamida ya kore shi. Miƙewa ta yi ta koma kan gado. Ta ƙosa ta koma gida, ba ƙaramin kewarsu ta yi ba. Ta kira Umma su ka gaisa sannan su ka yi hira mai tsawo da ƙannenta. Bayan ta gama wayar ne taga kiran MK har biyu.
"Salamu alaikum," ta ce a hankali bayan ya dauki kiran.
"Wa'alaikumus salam, Ya Maryam ina wuni."
Dariya ta yi, "yau ni ake gaisarwa?"
"Eh mana. Ba ki ji sunan ki ba? Ya Maryam. Congratulations an gama jarabawa."
"Saura fargaban sakamako."
"Kar ki damu in sha Allahu za ki ga sakamako mai kyau."
"Allah Ya sa, amma ina tsoro."
"It's normal to be scared. Ki yi ta addu'a. Yaushe za ki koma Kaduna?"
"Jibi su Hamida za su rubuta 105 da safe, tana dawowa za mu tafi. Kai yaushe za ka tafi?"
"Ni ina nan."
"Ba ka gama lab work ba?"
"Na gama. Amma akwai sauran abubuwan da ban kammala ba. Kuma hutun duka na sati biyu ne, kan ki ce me ya ƙare."
Maryam ta gyara zamanta kan gado tana jinjina kai. "Lallai a gaishe ka. Ni hutu ko na kwana ɗaya ne sai na koma gida. Kodayake ka kusa gamawa ka huta gaba ɗaya shi yasa ka ke ganin hutun sati biyu ba komai bane."
Sun debe lokaci mai tsayi suna hira har aka kira sallar Isha'i.
"Bari in bar ki haka."
"Sai anjima," ta je kashe wayar ta ji ya kira sunanta. "Na'am? Ka ce wani abu ne?"
MK ya gyara murya daga ɗayan gefen. "Idan ba kya komai gobe zamu iya haɗuwa?"
Ba tare da wani da dogon tunani ba Maryam ta ce mai eh. "Sai ka zo Allah Ya kaimu."
"Ameen."
Tana ajiye wayan suka haɗa ido da Hamida. Hamida ta ɗage mata gira tana shu'umin dariya. "Ya Maryam kenan."
Maryam ta juya idanu. "Mene ne Hamida."
"A'a, ni me kika ji na ce. Bakina alekum. Ba yanzu zan yi magana ba sai nan gaba."
Maryam ta juya idanu. Suna cikin haka Sumayya ta shigo. Ta daɗe da zama ʼyar ɗakin gaba ɗaya. Allah bai haɗata da roomates na gari ba. Faɗan yau daban na gobe daban. Kullum suna wurin security ana musu alƙalanci. Ɗakin su da sarari sosai, tare suka je ɗakin Sumayyar su ka kwaso kayanta.
"Hamida me yasa kike son tsokanar Maryam wai?" In ji Sumayya tana ajiye jakarta.
Hamida ta zaro idanu waje. "Ni me na yi dan Allah. Ban fa ce komai ba. Wai Sumy kin lura yanzu Ya Maryam bata cewa mu fita tare idan MK yazo? Sai dai kawai ta saɓa mayafi ta yi gaba abunta."
Sumy ta fashe da dariya. "Yanzu ta yarda ba wurin mu ya ke zuwa ba."
Hamida ma ta yi dariya. "Tun yaushe."
Maryam bata da lokacin su, dan idan Hamida da Sumayya suka sakata a gaba bata da bakin kare kanta. Indai a magane ne su biyun nan ba'a taɓa kadasu. Shi yasa ƙawancen su ke da ƙarfi, halin su ɗaya wurin tsokana da neman magana.
"Idan kun gaji se ku yi shiru ai."
Suka sake fashewa da dariya. "Yanzu dai Ya Maryam me za ki dafa mana?" Sumayya ta tambaya bayan ta saita kanta sun daina dariya.
"Ban gane mai zan dafa ba? Ni na ce muku zan yi girki."
"Naga wai kin gama jarabawa."
"Ohh ohh, saboda na gama jarabawa sai aka ce girki ya dawo kaina. Toh gaskiya nima a gajiye nake."
"Kai Ya Maryam ki taimaka. Wallahi calculus dinnan babu sauƙi. dy/dx kawai nake ji ana cewa amma ba fahimta na ke yi ba." Sumayya ta ce da jimami. "Ni ko a secondary ban yi Further Maths ba. Allah sarki Mr. Ajayi, yana ta ce mana mu zaɓa Further Maths saboda gaba muka ƙiya muka zaɓa Food and Nut saboda girke-girke."
Me Maryam zata yi idan ba dariya ba. "Idan za ku ci macaroni toh."
Da sauri suka haɗa baki, "zamu ci mana."
***
Tunda MK ya kirata ya ce gashi nan tahowa gabanta ke faɗuwa. Zuciyarta na tsananin duka kaman zata tsaga kirjinta ta fito.
Faɗuwar gaban ko na menene? Maryam MK ne fa, ta faɗawa kanta, menene na fargaba har haka?
Wayarta da ta yi ƙara ta firgita har tana yarda wayar. Allah Ya so ta su Hamida ba su ɗakin da ta sha tsokana. Daman kafin su tafi karatu sai su ka yi mai isar su.
A hankali ta kara wayar a kunnenta na hagu. "Salamu alaikum."
"Wa'alaikumus salam Maryam, gani a waje."
"Toh gani nan zuwa."
Ta furzar da iska. Madubin da ke maƙale jikin locker ta kalla. Doguwar riga ce a jikinta, yaɗin mai laushi mara nauyi. Pashmina ne rataye a wuyarta kallar toka, kala ɗaya da rigarta, ta yi rolling da shi. Fuskarta babu komai illa kwalli da man leɓe.
Wurin da ya saba zama ta ganshi a zaune. Sanye ya ke da manyan kaya hullarsa sai kyalli ta ke yi sai ka ce yau take juma'a. Yana hangota ya miƙe tsaye, murmushi shimfiɗe a fuskarsa.
Bakinsa ya motsa alamun magana amma bata ji me ya ce ba. A gaban shi ta tsaya sai ta ganta wata ʼyar ƙarama. Kaman ko ya san me yasan me take tunani ya ce, "dama haka kike ʼyar mitsila?"
Maryam ta ɗan harare shi ta gefen ido. Dariya ya yi yana washe duka haƙoransa. Leda ya miƙa mata, ta karɓa tana mai kallon tambaya. "A little gift for finishing exams."
"Gift kuma? Toh idan result ɗin ya fito ban yi ƙoƙari ba fa?"
Mk ya ɗan kalleta. "Wannan na gama exams ne. Idan result ya fito sai in san wanda zan baki, congratulatory ko consolation gift. Amma I am confident congratulatory gift zan ba ki."
Maryam ta jinjina mai kai. Allah Ya sa toh. Dan har ƙasan ranta tana tsoron fitowar sakamakonta duk da ta san ta yi iya bakin ƙoƙarinta.
"Mu dan taka idan ba za ki damu ba." MK ya ce.
Maryam ta gyada kai. Jerawa su ka yi suna tafiya. Bata tambaye shi ina za su je ba. Su ka yi hanyan Faculty of Engineering. Tun fara takawarsu ya karɓa ledar daga hannunta, ya ce idan sun dawo zai bata.
"Kin tuna farkon haɗuwar mu?"
Bata yi tsammanin tambayar ba sam. Ta ɗaga kai ta kalle shi ta samu shima ita ya ke kallo.
"Ranan da muka je tutorials a FSLT mana."
MK ya girgiza kai. "Ba ranan muka fara haɗuwa ba."
"Ba ranan ba? Anya kuwa mun taɓa haɗuwa kafin nan?"
"We did. Kin san saboda ke na yarda in yi muku tutorials?" Da mamaki ta kalle shi. "Tunda na shigo makarantar nan ban taɓa yiwa wasu tutorials ba idan ba abokai na ba, sai a kan ki."
"Ni kuma..."
Ta rasa me zata ce. Har yanzu tana tantamar haɗuwar da ya ce sun taɓa yi. Da sun taɓa haɗuwa tabbas da ta tuna.
Suna ta tafiya sai ga su a wurin Comm Market ta baya wurin Engineering. Street light ya haska wurin.
"A nan na fara ganin ki." Khalid ya furta da murmushi a fuskarsa. "Kin dawo lectures ke da wata ƙawar ki. Zubaida sunanta if I am not mistaken."
Maryam ta zaro ido waje tana kallonsa cike da mamaki. Shine ya mata magana ranan da ta da rako Zuby siyan madara? Ranan ta yi lectures tun ƙarfe bakwai, ta gaji sosai. Tabbas ta tuna wani ya yi mata magana lokacin amma sam bata kalle shi ba ko riƙe abunda ya ce dan a lokacin burinta kawai ta koma ɗaki. Har Zuby na mata mita wai ba'a yiwa maza haka.
"Kai ne?" Har yanzu mamaki bai bar fuskarta ba. "Me yasa baka taɓa faɗa mun ba?"
Khalid ya dage kafaɗa. Tafiya ya fara yi Maryam ta bi shi. Hanyar komawa hostel su ka ɗauka.
"Tun ranan na ke addu'ar Allah Ya sa in sake ganin ki. Allah Ya amsa addu'ata ki ka zo FSLT ranan. Ba ni ya kamata in yi tutorials din ba amma saboda ke na yarda na yi."
Sun zauna kan kujera Maryam ta kasa cewa komai sai kallon shi ta ke yi. Murmushin fuskar Khalid ya faɗaɗa. "Bayan an gama ina ta tunanin yanda zan yi miki magana sai ga Hamida ta same ni. Ba tare da wani dogon nazari ba na amince. Ranan na sha tsokana da mita wurin abokai na. The first time na yi tunanin za ki gane ni amma sai naga babu alamun recognition a idon ki. Da na yi niyan faɗa miki amma wata zuciyar ta bani shawarar yin shiru har sai mun saba."
Khalid ya yi gyaran murya ya gyara zaman shi ya zama suna fuskantar juna. Idonsa a kan fuskarta har kallon ya so yin yawa saida ya yiwa kansa faɗa ya kauda kai da sauri.
"Maryam?"
Kiran sunan har tsakar kanta. Ba zata iya dagowa ta kalle shi ba. Shima bai matsa ba. Ya cigaba da cewa, "Tun ranan da na fara ganin ki wani abu ya ja hankalina gare ki. Watannin da mu ka yi tare ya sake tabbatar mun you are special. Maryam, ban taɓa jin wata a raina kamar haka ba. Ban taɓa soyayya ba saboda hakan ban san ko ita ce ba. All I know is, kullum da tunanin ki na ke kwana da shi na ke tashi. Natsuwar ki da hankalin ki ne suka sake janyo ni gare ki. Na ƙara tabbatarwa zuciyata ba ta yi lefi ba da ta ce sai ke."
Khalid ya ja lumfashi sannan ya furta abunda zuciyarsa ta daɗe da son amayarwa. Lokaci ya yi. "Maryam ina son ki bani dama in nemi soyayyar ki."
Tunda ya fara magana sai a lokacin ne Maryam ta dago kai ta kalle shi. Suna haɗa ido ta yi saura kauda nata saboda yanda tsigar jikinta su ka tashi. Kalamansa sun shiga kwakwalwarta sun samu matsugunni sai nanata su ta ke yi. Bata taɓa zaton haka daga gare shi ba. Ƙawayenta nata tsokanarta amma ta yi zaton duk shirmen su ne.
"Maryam?" Khalid ya kira zuciyarsa a akaifa. "Ba ki ce komai ba."
Me zata ce mai? Eh? A'a? Bata sani ba? Ita ba yarinya ba ce ta san sa'anninta na da samari, har wanda ba su kaita ba ma. Amma bata taɓa hango kanta a irin yanayin ba. Shin ta kaima ta yi saurayi? Ba karatu ya kawo ta ba?
"Khalid..." ta fara cewa sai kuma ta yi shiru. Wallahi bata san me ya kamata ta ce mai ba.
Kallonsa ta yi. Daga ganin fuskarsa ta san yana fargaban amsar da zata ba shi. Bata taɓa mai wani kallo ba bayan mai koya mata karatu. Ta san yana da kirki da kuma halaye nagari.
"Ban san me zan ce ba."
Khalid ya yi murmushi. "Na fahimta. Ba sai kin ce komai ba yanzu, amma ki yi mun alƙawari za ki yi tunani a kai."
Maryam ta gyada kai. Shi ya fara miƙewa ita ma ta miƙe, ya miƙa mata ledar ɗazu. "Duk hukuncin da kika yanke ya yi, but I just hope it will be in my favour. Sai da safe Maryam."
Ta koma ɗaki (in a daze). Zaune kan gado babu abunda ta ke ji sai kalaman Khalid. Zuciyarta na cewa ta ce a'a, ta maida hankalinta kan karatunta, sai dai wani gefe na raɗa mata me ye aibun Khalid? Ta san yanda ya ke da kirki da ruƙo da addini. Cikin su uku ya fi sakin jiki da ita. Yanzu ta gane dalilin haka.
Maryam ta saƙa ta warwara amma ta rasa abun yi a haka Hamida ta shigo ɗakin ta same ta.
"Ina Sumayya?"
"Tana waje tare da Bello."
Bello, saurayinta.
"Lafiya Maryam? Na ganki a firgice wani abu ne ya faru?"
"Hamida MK..."
"MK? Subhanallah, me ya same shi?" Hamida ta tambaya a firgice.
"Wai yana so na."
Hamida ta sauke lumfashi sanna ta yi tsaki. "Dalla! Ina sha ma wani abu ya same shi. Dama waye be san MK yana son ki ba?"
Maryam ta zaro ido. Hamida ta yi dariya. "Ke kaɗai ce ba ki gani amma he has been so obvious ina ga shima bai san ya fito fili har haka ba."
"Me zan ce mai Hamida?"
"Ba ki son shi?"
"Oho! Ni ina na sani!"
Hamida ta yi dariya. "Zauna ƙawata, faɗa mun me ya faru." Bayan Maryam ta gama faɗa mata, ta jinjina kai. "Ya baki lokaci ki yi tunani kenan. Amma ke me kike ji a kan shi?"
"Ban sani ba Hamida."
"Ki amsa tambayoyin nan tsakanin ki da Allah. Ya kike ji idan kina tare da shi? Are you comfortable with him? Kina yawan tunanin shi? Kina kewarsa lokacin da ba ya kusa? Kin damu da walwalarsa da farin cikinsa? Do you trust him? Sai na karshe, yanzu idan ya ce miki ya samu wata ya za ki ji a ran ki?"
Maryam ta kifta ido tana kallo Hamida. "Hamiidaaaaa! Duk ina kika san wannan?"
Hamida ta yi fari da idanu. "Kin ganni nan ba ƙaramar malamar soyayyah za'a yi ba."
Maryam ta fashe da dariya. "Haqqun. Naga alama ai."
"Yanzu ke dai ki yi tunanin amsar tambayoyin da na miki, ta hakane za ki gane idan za ki iya bashi dama."
Da wannan tunanin Maryam ta kwanta barci. Washegari su Hamida na dawowa daga jarabawa suka kama hanya. Ta yi tunanin kiran Khalid anma ta fasa bata shirya ganinsa saboda bata da amsar da zata ba shi. Har bakin get Sumayya ta raka su. Ita sai gobe zata tafi. A ƙasa da awa ɗaya suka isa Kaduns garin gwamna. Kamar kullum Maryam ta fara sauka aka ƙarasa da Hamida.
"Toh Ya Maryam sai mun yi waya. Ayi hutu lafiya."
Ƙaramar jakar baya kawai ta dauko. Tsakar gidan babu kowa. Ɓangaren Mama da Baba Malam ta isa ta san suna nan sauran ʼyan gidan sun fita. Ta ji daɗin ganin kakanninta sosai inda Mama ta yi ta tsokanarta. A irin wannan yanayin ne ta ke kewar Inna.
Bata daɗe a ɓangaren su ba ta nufa ɗaki bayan Mama ta faɗa mata abincinta na nan a falo. Bayan ta yi wanka ta ci abinci, sai barci. Ƙaran wayarta ne ya tada ta. Da sauran barci a idonta ta amsa wayar muryarta chan ƙasa. Jin muryar Khalid ya sa ta miƙe zaune da sauri.
"Hello Maryam kina ji na?"
"Mmmmm."
"Shine kika tafi ba ki kirani ba ko?"
"Uhmm.."
"Ya kika samu mutanen gidan?"
"Baba Malam da Mama kaɗai na samu. Su Zee na makaranta, Umma kuma na wurin aiki."
"Toh ki gaishe su. Ya hanya?"
"Za su ji in sha Allah. Hanya lafiya."
"Allah Ya huta gajiya."
"Ameen."
Daga nan su ka yi shiru. Tunda ta amsa wayar zuciyarta ke dukan uku-uku, cikinta kuma ba ciwo ya ke yi ba amma ya ƙulle kaman wasu abubuwa na yawo a ciki.
"Maryam," Khalid ya kira sunanta a hankali.
"Na'am?"
"Kin shirya bani amsa?" Yana fargabar amsar zata bashi dan idan ta ce bata amince ba bai san ya ze yi ba.
Kaman yana gabanta ta girgiza kai. "A'a."
"Toh shikenan. Take your time. Ayi hutu lafiya. Sai anjima."
Ita ta katse kiran, riƙe da wayar a hannu. Babu daɗewa ƙannenta suka dawo tare da Umma. An sha ihu da tsallelen murnan ganin juna.
Maryam ta yi kewarsu sosai ranan kwana su ka yi hira. Maganar MK da ta Hamida na maƙale a ranta.
Me ya kamata ta yi?
•
•
•
•
•
Salamu alaikum jama'a💕
Who missed me? Na ɗan samu sarari na ce bari in yi updating. Da fatan kuna mun addu'a🥹 dan Allah a taimaka. Starting exams in less than two weeks so I will see you after I am done.
Mu dawo kan mutanen mu. What was that confession!😻 Khalid fa be zo da sauƙi ba.
Toh jama'a wace irin amsa kuke ganin Maryam zata ba shi?
And tell me, where do you see the story heading?
Duka mu haɗu a kwament section🤭
Kar a manta a saka ni a addu'a🥹🥹 nagode.
~Maymunatu Bukar💕
Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro