17.
Assālamu ʿalaykum wa raḥmatu-llāhi wa barakātuh.
Kwana da yawa!🤭 Na yi kewar ku sosai na yi kewar yar mitsilan Abba.
hajjoabukur ce ta dauki nauyin wannan babin💃🏻 ku garzaya domin karanta littafinta da ke nan wattpad.
Tana tafiya kawai ta ji an rufe mata ido ta baya. A firgice ta juya zuciyarta kaman zata faɗo. Lumfashi ta sauke ganin waye.
"Ƙawata Maryam!"
Maryam ta harareta tana maida lumfashi. "Zubaida kin bani tsoro."
"Yi haƙuri. Ina ta kiran ki ba ki ji ba. Ko duk fargaban exams dinne ya kama ki tun yanzu?"
"Ayyah ban ji ba." Juyawa ta yi ta ci gaba da tafiya Zuby na gefenta. "Exams kuma da yardan Allah za mu yi passing so babu wani fargaba."
"Allah Ya bamu sa'a."
Tare su ka isa ajin inda su ka same shi cike da mutane. Wasu zaune a ƙasa wasu a tsaye, wasu zaune kan kujerun theatre din. A gaban kujerun ita da Zubaida suka zauna. Mintin su ashirin suna jiran malamin. Sai da lokacin shi ya kusa ƙarewa sai gashi ya zo. Kuma bai wani daɗe ba ya tafi. Da yake jarabawa nata matsowa duk yawancin malamin sun gama courses ɗin su daidai ne ke aji yanzu.
"Ki zo muje ɗaki na kafin next class." Zubaida ta ce wa Maryam.
Tunda su ka dawo hutun mid-semester Zuby ta dawo kaman yanda ta ke da. Har haƙuri ta ba Maryam a kan shareta da ta yi, kuma ta faɗa mata dalilinta na yin haka.
"Lokacin wani tashin hankali ya faru a gida amma yanzu an warware komai Alhamdulillah."
Maryam ta daɗe da sanin rayuwar Zuby ya banbanta da nata, duk da kuwa dukan su sun rasa mahaifi.
Bayan rasuwar Abba rayuwar su tabbas ta chanza amma chanjin ba chan-chan.
Ba haka ta kasance da Zuby ba.
Gaba ɗaya rayuwarta ta chanza daga inda ta santa. A nan Zaria suna gidan dan uwan mahaifin su ne, bayan rasuwar baban su maman su ta koma Yobe da zama. Dama su asalin ʼyan chan ne. Sam zaman gidan dan uwan baban su baya masu daɗi. Ita da ƙaninta ne suke zaune a nan saboda makaranta. Sauran ƙannenta su uku suna wurin maman tunda su ƙanane. Babban cikin su shekarar ta shida.
Zuciyar Maryam ta karye da Zuby ta bata labari. Ta kuma ji ba daɗi da ta yi saurin yarda da abunda zuciyarta ta bijiro mata akan dalilin da Zubyn ta share ta.
"Idan mun je me za ki dafa mun?"
"Duk abunda kike so. Jiya ma Yaya Habu ya kawo mun miya."
Maryam ta daga mata gira. "ʼYar gatan Yaya Habu. Yaya Habun nan na ji da ke."
Zuby ta yi tsaki. "Ke rabu da shi. Zai gaji ma ya dena ne. Yanda uwar shi ke gallaza mun a yanzu ma ya a ka ƙare bare na zama surukarta. Iyakaci kawai in ci kuɗin shi kafin lokacin."
Maryam ta yi dariya ta girgiza kai. Suna isa ɗakin Zuby ta kunna risho ta dafa taliya sannan ta dumama miyar da aka kawo mata. Bayan ta gama ta zubawa Maryam ta miƙa mata.
"Na gode," ta ce tana kai cokali baki. "Mmm amma miyar ta yi daɗi."
"Ai Ya Habu ba dai iya girki ba."
Maryam ta zaro ido. "Shi da kan shi ya ke yin miyar ya kawo miki?"
Zubaida ta gyada kai. "Kika wani zaro ido. Kin san shine babba kuma 'yan uwanshi mata duk ƙanana ne, shi ya ke taya maman shi aiki."
"Ya huta abun shi."
Zubaida ta taɓe baki. "Shi ya sani. Wai shi fa a ganin shi auren shi zan yi," ta kyalkyale da dariya. "Ko maza sun ƙare a duniya ba zan taɓa auren shi ba. Gwara in mutu ba aure."
"Ki daina kula shi tunda kin san ba kya son sa. Ba kyau kina sa mai rai alhali kin san ba son shi kike yi ba. Ba ki ganin kaman kina yaudaran shi."
"Yana dai yaudaran kan shi. Shi dan bashi da hankali bai ga irin baƙar wahalar da na ke sha ni da dan uwana wurin uwarsa ba shine ya ke tunanin zan so shi. Ai ko dan in rama abunda Hajiya ke mun wallahi zan yi abunda ya fi haka. Ita ba zan iya yi mata komai ba amma idan wani abu ya samu Habu kaman ya same ta ne tunda duk cikin yaranta ta fi son shi. Ina son ta ji kunci sosai a cikin zuciyarta har ta ji inama zata iya cireta daga ƙirjinta ta huta."
"Zubaida..." Maryam ta kira sunanta a sanyaye.
"Hmm Maryam ke dai a bar maganan. Ni ban ma san yanda aka yi Hajiya bata san yana bi na ba dan da ta sani da anyi yaƙin duniya na uku."
Daga nan kuma akalar hirar ta su ta chanza. Sosai Maryam da Zubaida su ka ƙara sabawa da junan su.
Ƙarfe biyu saura suna shirin tafiya aji aka kira Zubaida aka faɗa mata malamin ba zai zo ba.
"Hutaroro, sai in tafi ɗaki in huta. Anjima ina son in fita karatu."
"Har yanzu tutor dinnan na ki na nan?"
Maryam ta miƙe tana rataye jaka. "Yana nan fa. Mun kwana biyu ma ba mu yi karatu ba suna ta test."
"Wani course ya ke ma?"
"Chemical engineering."
"Engine boy ne kenan. Ni nawa tutor ɗin dan duniya ne."
"Toh ko za ki zo mu je wurin MK?"
Zuby ta girgiza kai. "A'a ki bar shi kawai. Na samu wani ma wannan weekend ɗin zamu fara."
"Okay toh shikenan."
A bakin ƙofar hostel su ka yi sallama Zuby ta koma ciki Maryam ta kama hanyar nasu hostel ɗin su.
"Maryam Ahmad."
Da mamaki ta juya ta ga waye ke kiran sunanta gaba ɗaya haka. Wani saurayi ne fuskar kaman ta san shi a wani wuri amma ta kasa tunawa.
Dariya ya yi ya tsaya gefenta. "Kar dai ki ce ba ki gane ni ba."
Maryam ta yi murmushi. Tabbas ta san fuskan amma ta manta sunan shi kuma ta manta a ina.
"Haba Maryam Ahmad. Yanzu kin manta da ni. Ni kam ban taba mantawa da ke ba."
Tashin hankali. Shi ko waye wannan?
"Dagaske ba ki gane ni ba." Ya ce cike da mamaki. "Head boy ne fa. Ibrahim ne."
Sai a lokacin ta tuna inda ta san shi. Tabbas shi ya yi headboy da suna JS3. Murmushi ta yi ta ce, "Allah sarki. Ina wuni."
"Lafiya lau. Ashe nan ki ke, ban
sani ba ai. Wani course?" Kai ya gyada bayan ta faɗa mai. "Masha Allah. Allah Ya taimaka. Ni ina Vetinary medicine."
Ibrahim ya so jan gaisuwar ta yi tsawo Maryam ta saurin katse shi. "Sai anjima."
"Sai anjima. Ki gaida twin din ki."
A makaranta duk wanda ya san Maryam dole ya san Hamida. Ta amsa mai da zata ji ta yi gaba abunta.
"Hamida ba ki san wa na gani ba yanzu a waje." In ji Maryam a lokacin da take ajiye jakarta a kan gado.
"Dan makarantan mu ne halan. Nima cikin satin nan sai wani haɗuwa na ke yi da su. Wasu ma ban zata za su gane ni ba har su yi mun magana. Wa kika gani?"
"Ibrahim headboy. Wanda ya yi headboy da muna JS3."
"Ibrahim lover boy za ki ce ba headboy ba." Hamida ta fashe da dariya.
"Wannan dariya haka. Kin bar ni a duhu." Sumayya ta ce tana kallon ƙawarta.
"Tsohon saurayin Yaya Maryam ne. Kai na sha chocolate da sweet. Ni ake kira a ba saƙo. Yarinyan nan ta ƙi karɓa ni ko in shanye tass."
Maryam ta girgiza kai. Ta san dama Hamida sai ta ɗago zancen.
Hamida ta sake fashewa dariya, "Akwai wata letter da ya taɓa turowa..."
"Toh ya isa haka!" Ta yi saurin katse ta.
"Gaskiya ban yarda ba sai an faɗa mun." In ji Sumayya.
"Ba da ni ba toh."
Wayarta ta dauka ta bar ɗakin Hamida na ta dariya ta ma kasa ba wa Sumayya labarin. A wurin zama da aka jera kujerun kankare ta zauna. Kewar gida ta ke yi dan haka ta dannan sunan Umma a wayarta. Kiran na shiga aka ɗauka, muryar Safiya ta riski kunnenta.
Sun daɗe suna hira har saida aka yi mata warning katinta ya ƙare.
Kiran wata baƙuwar lamba ya shigo wayarta. Da kaman ba zata dauka ba dan har saida kiran ya kusa tsinkewa ta latsa kan wurin amsa kiran. A take ta yi nadamar amsa kiran saboda wani ashar da ta fara cin karo da shi.
"Ki faɗawa Sa'adatu na ce ta yi kaɗan. Ba ɗan sanda ba ko dan itace zata saka a kan wurin nan sai na karɓa haƙƙi na. Musan da ta sani a da ba shi bane a yanzu. Har sai inda ƙarfi na ya ƙare tukun. Ni da ita mu zuba, shega ka fasa dan halak sai yanka."
Kaman an daskarar da ita a wurin ta kasa motsi ta kasa tsinana komai. Ko kashe wayar ta kasa yi har saida Baba Musa ya gama amayar da abunda ke ransa. Daga ƙarshe ya ƙara zage Ummanta tas sannan ya kashe wayar.
Hawaye masu ƙuna da raɗaɗi ne suka gangaro fuskarta. Wannan wani irin bala'i ne. Har sai yaushe Baba Musa zai kyale su su ji da maraicin da ke damun su. Da za'a iya bada dukiyan da ya ke ta nacewa a kai a dawo da Abbanta da ita da kanta zata dauka ta bada.
Shekara nawa da barin Abbanta duniya amma Baba Musa har yau bai bar su sun huta ba. Ya bari su ji da rashin da ke damun su. Har yau har gobe raɗaɗin rashin Abba bai rage a zukatan su ba.
Ba wannan ne karon farko da ya nemeta ba sai dai bai taɓa kiranta ba sai dai ya aiko saƙon SMS kaman yanda ta san yana aikawa Umma. Bata taɓa faɗawa kowa ba. Yana aiko saƙon ta ke gogewa. A ganinta babu amfanin faɗa kawai zai kawo tashin hankalin da bata buƙata.
Ta rasa me zata yi ta manta da kalaman Baba Musa. Ɗaki ta koma inda ta samu Hamida da Sumayya na hira. Bata sa musu baki ba ta haye gadonta. Tasbihi ta fara yi har barci ya dauketa.
***
Saura mai ƙiris ya gama makarantan nan.
Abunda Khalid ke tausasa zuciyarsa da shi kenan.
Lallai Hausawa sun yi gaskiya da suka ce aski idan ya zo goshi ya fi zafi. Shekarar shi biyar a makarantan nan, bayan ko wani zango na karatu yana ganin ba zai sake shan irin wahalar da ya sha ba sai an dawo makaranta ya ga ai wanda ya yi a baya nafila ne.
Tunda ya shigo ajin karshe ake gasa mai aya a hannu. Malaman duk yanda za su bata maka result sun sani.
Saboda idan ba tsabar mugunta ba wasu irin tambayoyi ne a ka yi musu.
"MK ya test?"
Wani dan ajin su ne ya mai tambayan. Khalid ya yi murmushi. "Alhamdulillah, amma dai toh...."
"Ah haba. MK kuka ce haka mu mai zamu ce."
Ya yi dariya. "Allah dai Ya bamu sa'a."
A waje ya haɗu da Nas da Wakili. "Daga gani test dinnan ya maka sauki MK." In ji Wakili.
"Dama paper na taɓa bawa MK wahala ne." Nas ya ce yana kaiwa Khalid duka a kafaɗa. "Guru ne wannan ko ka manta."
Matsawa gefe Khalid ya yi yana ture hannun Nas daga kafaɗarsa. Shi yanzu matsalarsa shi ne yanda zai cire kansa daga matsalar da ya jefa kan shi.
Ana gobe za su fara test Ya Ramlah ta kira shi a kan lallai ya kamata ya je gida tunda ya dawo zangon karatun nan bai je ba. Ya yi koƙarin ya nuna mata an kusa fara jarabawa ba ya da wannan lokacin. Amma sam ta ƙi ta fahimce shi har ta yi fushi da shi.
Bai cika son yana samun saɓani da yayyunsa ba musamman Ya Ramlah, dan duk ciki sun fi shiri da ita.
Yanzu ya gama test sai nan da sati daya zai fara jarabawa. Wannan ne lokacin komawa gida. Amma shi bai shirya zuwa Kano ba.
"Wai MK kana jin abunda na ke cewa kuwa?"
Sam hankalinsa ba ya wurin. "Yi hakuri ban ji me ka ce ba."
Nas ya mai wani kallon da bai gane na meye ba. "Tambayar ka na ke yi ina yar cute baby doll ɗin ka." Yana gama faɗa ya matsa a wurin dan ya san MK hannu zai kai me.
Khalid bai san me ya sa yake tare da Nasir har yanzu ba.
Saboda ya kasance tare da kai a lokacin da babu kowa.
Rabon shi da Maryam tunda ya fara test. Kuma maganan gaskiya ya yi kewarta sosai.
"Ni ranan kaman ita na gani a tsaye da wani dan Vet." Da sauri Khalid ya juya ya kalla Wakili. "Ba ita ba ce mara tsawon cikin su ba?"
Nas na dariya ƙasa ƙasa ya ce, "ita ce, wata mara haske haka."
"Tabbas itace. Yaron da na ganta da shi notorious ladies man ne."
Dariya na cin Nas da kyar ya ke iya magana. Kallon MK ya ke yi inda ya daskare a tsaye. "Ah haba. Kasan ʼyan ƙanana—" bai gama magana ba Khalid ya make shi.
Yasan abunda zai faɗa, ba yau ya fara faɗa ba. Ransa ya ɓaci bai ma tsaya jiran abokan na sa ba.
Ya ruga da ya yarda son Maryam ya mai kamu ba kaɗan ba. Ta ya hakan ya faru? Bai sani ba. Tun ranan da ya fara ganinta ta shiga ransa. Bayan sun fara mu'amala ya kula da hankalinta. Tana da hankali fiye da sa'anninta. Amma fiye da komai, nutsuwarta ne ya fi jan hankalinsa. Sau da yawa yana samun kansa da kallon yanda ta ke abubuwanta musamman in sun fita karatu. Komai a nutse ta ke yi kaman tana da dukkan lokaci, ko da kuwa babu. Ko tafiyarta abun kallo ne. Da ɗaiɗai da ɗaiɗai ta ke takawa kaman me tsoron ƙasa.
Bai taɓa tunanin zai tsinci kansa a wannan halin ba. Abu ɗaya ya kawosa Zaria. Ya gama digiri ya ƙara gaba. Ya gina kansa ya tsaya kan ƙafafuwansa sannan ya yi iya bakin ƙoƙarinsa wurinta inganta rayuwar Ummansa
Mata basu cikin tsarin da ya yi wa kansa a yanzu. Yasan ba zai zauna haka nan ba har ƙarshen rayuwansa. Amma a yanda ya tsara sai chan gaba zai fara wannan tunanin. Chan gaba in ya kawar da matsalolin da suka kewaye shi.
Sai gashi yanzu komai na nema ya chanza. Ba san ya so yake ba, dan bai taɓa ɗanɗanawa ba. Amma ya san tabbas abunda ya ke ji game da Maryam ya fi so.
Wasu za su ce ya yi wuri, bai isa ya gama tantance abunda ya ke ji game da ita ba a cikin dan ƙanƙanin lokaci. Amma ya san kansa. Abun da yake ji game da ita ba zai iya zama komai ba sai soyayya.
Soyayyar da ya ce ba ze yi ta ba a yanzu sai gashi ta zo mai a bazata, a lokacin da bai taɓa tsammani ba. A irin gidan da ya taso so ba abun sha'awa bane.
Saboda iyayensa, in har zai yi amfani da iyayensa a matsayin misili ba zai taɓa aure. Amma yana da hankalin da ya san cewa ba haka aure ya ke a ko ina ba.
Kaman Ya Ramlah. Har baya son zuwa gidanta saboda yanda mijinta ya ke tarai
Idan ya je gidan su Nasir ma haka. Alhajin su baya iya boye kulawar da ya ke wa matarsa.
Amma ba haka ya kasance a gidan su. Ya tashi a environment daban da sauran. Da zai iya raba Mama da mahaifinsa, da tuni ya yi. Yana ɗaya daga cikin dalilin da baya son komawa gida. Sam baya son ganin su a tare.
Ya koma ɗaki ya yi wanka ya chanza kaya. Zai je cin abinci amma sam baya da sha'awar cin abincin.
A hanya wayarsa ta yi ƙara, kiran Ya Ramlah ya shigo. Da kaman ba zai dauka ba amma ya san zai ƙarawa kansa laifi ne idan ya ƙi.
Ko gaisawa ba su yi ba. "Wai kai Khalid me yasa a rayuwarka kana da taurin kai baka jin magana. Ba yau ka ce zaka dawo ba."
"Ya Ramlah.... cewa na yi wata ƙila zan dawo yau. Test ɗina na ƙarshe an daga shi sai yau na yi, ban ma daɗe da fitowa ba. Kin ganni nan ma zan je neman abunda zan ci tun safe babu abunda na saka a ciki na."
"Toh na ji, na ji.. gobe zaka taho kenan?"
"Ya Ramlah dole sai na zo wai? Kullum fa sai mun yi waya da Mama. Ni kin san.... Dama bayanan ne shine zan dawo. Amma yana nan, bana so in zo mu haɗu."
"Khalid yaushe zaka gane cewa abunda kake yi ba Baba kaɗai ya ke shafa ba? Harda Mama, harda mu. Wai kasan Ammar ya fara tafiya, ya fara magana, bai sanka ba bai san ya kamannin ka suke ba. Haba Khalid. A ƙoƙarin son janye kan ka daga wurinsa, you are also pulling yourself away from us. Ka yi tunanin mu mana. Idan ma baza ka yi tunanin mu ba saboda ba mu isa ba, good and fine. Mama fa? Mama fa Khalid? Me ye laifinta? Dan ta zauna da shi?"
"Ya Ramlah....."
"Mmm mmm kar ka kira sunana. Ka yi tunani a kai, abunda kake yi ka san baka kyautawa. Khalid ta ya zaka tafi ka yi wata da watanni baka zo ta ganka ba? Kana nan baki da hanci a Zaria. To idan ka yi nisa shikenan ba zamu riƙa ganin ka ba sai bayan shekaru. Ko kuma ka tafi shikenan sai dai a waya. Waya zumunci ne? Zumunci a ƙafa ya ke ai, ba a waya ba. Waya ya zo ne dan ya sauƙaƙe mana rayuwa kawai. Kuma kar ka manta tana da haƙƙi a kan ka. Bawai dan ka kirata ko ka tura mata wani abu wanda bama ta da buƙata, ba shi ke nufin ka sauke haƙƙinta a kanka ba. Ka je ta ganka ta ji daɗi shima wani abu ne. Mun sani Khalid, mun sani when it comes to the father department ba mu yi sa'a ba. Amma jarabawar mu kenan. Ya rage naka, za ka ci jarabawar ko zaka faɗi."
Kit ta kashe wayar ta barshi da jiki a sanyaye kaman an jefa shi cikin ruwa. Abincin da be je ya ci ba kenan ya koma ɗaki.
Kalaman Ya Ramla na ta mai yawo. Ya yi kewar gida, sosai. Amma idan ya tuna zai koma yaga mahaifinsa sai ya ji gaɓa ɗaya baya son ya koma.
Idan ya zauna a ɗaki zai iya haukacewa shi kaɗai dan su Nas ba su dawo ba.
Rigarsa da ya cire ya maita ya fita ba tare da ya san inda ze je ba.
Sai gashi ya tsinta kansa a ƙofar hostel ɗin su Maryam.
Toh yanzu da ya zo, kiranta ze yi ta fito ko kuwa?
Bai tsaya ya yi dogon tunani ba ya kirata. Dan idan ya zurfafa tunanin zai iya juyawa ya koma.
Cikin sa'a kuwa ta dauko. Nan fa ake yinta. Me zai ce mata?
"Ya test ɗin ka?" Tambayar da ta mai kenan bayan sun gaisa.
"Alhamdulillah, yau mu ka gama. Saura exams."
"Allah Ya taimaka."
"Uhm...uhm..." ya ce yana sosa kai. "Kina ɗaki kuwa? Gani a bakin hostel ɗin ku."
Shiru bata amsa ba har ya yi tunanin ko ta kashe. "Gani nan zuwa."
Ajiyar zuciya ya yi bayan ta kashe wayar. Yamma ya yi dalibai sun fara fitowa shaƙatawa. Da yawa kuma suna hanyan tafiya karatu. Shima ya kamata a ce yana hanyar aji amma ganin Maryam na gaba da zuwa karatu a yau.
A kan kujerun kankare da ke gaban hostel din ya zauna. Kaman an ce ya daga ido ya ganta tana fitowa sanye da doguwar riga ta yafa ƙaramin gyale a kai. Tana ta waige waige da alama tana neman inda ya ke. Suna haɗa ido ta saki murmushin da ya nufi zuciyarsa kai tsaye.
Subhanallah! Har wani kyau ta ƙara.
Kalaman Nas da ke bata mai rai ya tsinta kansa da tuni. 'Cute baby doll'. Ƙanƙantan ta ya yi yawa. Da bata faɗa mai shekarunta ba da ba zai taɓa cinka daidai ba.
A gefen shi ta zauna su ka ƙara gaisawa. "Ya kake ji saura maka semester ɗaya da rabi...a'a ɗaya da kaɗan ma tunda wannan ta kusan ƙarewa."
"Da na ƙosa in bar makarantan nan, amma," ya juya ya kalleta amma hankalinta na kan mutanen da ke harkan gaban su, "amma banda yanzu."
Waigowa ta yi ta kalle shi. "Lallai. Ko ni da na fara yanzu na ƙosa in gama."
Dariya ya yi yana girgiza kai. "Haba Yaya Maryam," tunda ya ji Zee na kiranta da shi ya kama sunan. "Bai ci a ce har kin gaji ba. Ba ki yi komai ba fa."
"Na sani! Amma jami'ar ba haka na yi tunani take ba."
"Ya kika yi tunanin take?"
"Kawai zaka zo bai wuce ka je aji sau huɗu a sati ba amma har ranan assabar muna zuwa aji."
Me Khalid ze yi idan ba dariya ba. "Jami'ar kenan. Amma fa ba dole sai kin je aji kullum ba. Za ki iya zama abunki."
"Hmm mmm! In samu carry over kenan. Ka san yanda Umma ta tsorata ni da carry over kuwa."
A cikin addu'o'in da mahaifiyarsa ke masa harda tsari daga carry over.
"In sha Allah ba za ki samu ba."
Maryam ta fara sabawa da Khalid dan sun daɗe suna hira har saida aka kira sallar maghriba.
Bayan sun yi sallama ya samu kan shi da faɗa mata.
"Gobe zan tafi Kano."
Maryam ta yi murmushi. "Ya kamata ka je gida. Ka daɗe baka je ba, tunda aka yi resuming."
Dariya ya yi. Kaman Ya Ramla ta raɗa mata a kunne.
"Me kike so in kawo miki?"
"Ba sai ka kawo mun komai ba," ta amsa tana girgiza kai. "Allah Ya kiyaye hanya. Ka gaida mutanen gida."
"Za su ji in sha Allah. Kar ki damu zan kawo miki gurasa."
Dariya ta yi ta shiga ciki. Sai da ya tabbatar ta wuce ya juya ya kama hanya. Wayar sa ya ciro daga aljihu ya kara a kunne.
"Hello Ya Ramlah, gani nan tahowa gobe. Amma.... a gidan ki zan sauka."
•
•
•
•
•
Mun daɗe bamu haɗuba! Ina wunin mu? Ya muke? Da fatan an yi azumi da sallah lafiya!🫶🏼
Toh jama'a, me ye ra'ayoyin ku game da wannan babi? Me kuke ganin zai faru a gaba?
~Maymunatu Bukar💕
Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro