Chào các bạn! Vì nhiều lý do từ nay Truyen2U chính thức đổi tên là Truyen247.Pro. Mong các bạn tiếp tục ủng hộ truy cập tên miền mới này nhé! Mãi yêu... ♥

15.













Kwanan Maryam biyu tana fanshe barcin da ta kwana biyu bata yi ba. Tunda ta zo ko tsintsiya bata ɗauka ba bare ta shiga kicin.

Wannan weekend ɗin Umma na off. Maryam ta sha hira sosai da Ummanta. Ba ƙaramin kewarta ta yi ba.

Maryam na magana Umma na ta kallonta sai dai bata jin abunda Maryam ɗin ke cewa. Tsananin kamanninta da marigayi Arc. Ahmad kawai ta ke gani. A yaran ita da Idris ne dama su ke kama da Abban na su, sai dai Idris be yi kama da shi sosai ba kaman yanda Maryam ta dauko shi. Ba kama ba kaɗai harta wasu dabi'unta sak irin na shi.

"Umma!" Maryam ta kirata da ɗan ƙarfi.

Umma ta kyafta ido tana dawowa daga duniyar tunanin da ta faɗa. Murmushi ta wa Maryam din su ka cigaba da hira abun su. Gidan babu kowa sai su kaɗai. Sauran yaran sun tafi islamiya, Mama da Baba Malam kuma sun fita ziyara.

Maryam da Ummanta sun daɗe suna hira. Tara su ka shiga kicin su ka dafa abincin rana. Hakan ya tunawa Maryam yarintar ta lokacin da take ta roƙon Umma ta bari ta yi abu. Da kuma lokacin da karanbaninta ya sa talgen tuwo ya sheƙo mata. Har yanzu tabbon na nan.

A lokacin babban burinta shine ta ganta a cikin kicin. Umma ta fattataketa ta koreta amma ba shi zai hanata komawa ba.

Akwai wani lokaci da ya daɗe da shuɗewa amma a zuciyarta kaman yau ne abun ya faru.

Abbanta ya tambaye su mai su ke so su zama idan sun girma. Amsarta bata chanza ba har yau. Sai ma son abun da ya ƙaru a zuciyarta, shi yasa ta matsa Umma ta sakata a catering school.

Kullum maganan Abba shine su yi rayuwa mai inganci. Basu taɓa neman abu ba su samu ba ko menene kuwa. Baya da wani buri a rayuwa sama da farantawa iyalinsa rai. Ya gwammace shi ya rasa su su samu.

Haka Ummanta.

Ko bayan Abba ya rasu Umma na iya bakin ƙoƙarinta wurin ganin rayuwarsu bata chanza ba gaba ɗaya. Sai dai abunda ba za'a rasa ba. Duk abunda su ke so wani lokacin kafin ma su nema zasu gan shi ajiye yana jiransu.

Shi yasa babban burin Maryam a rayuwa shine ta farantawa iyayenta rai. Zata dage sosai yanda za su yi alfahari da ita.

Ba su daɗe da gama dafa abincin ba su Zee su ka dawo daga makaranta. A faranti ɗaya Maryam ta zuba musu harda ʼyan mazan. Suna ci suna hira. Idanuwanta su ka fara yaji alamun ƙwalla. A yanayi irin haka ne matsanciyar kewar Abba ke kamata. Da kyar ta haɗiye kukanta, dan ta san tana farawa wurin zai ɗauka gaba ɗaya.

Bayan sun gama ci Bashir ya ɗauke plate ɗin Zee ta share wurin. Hirar sai ta koma falo. Kowa nata ƙoƙarin ba Maryam labarin abubuwan da suka faru da tana makaranta. Ana cikin hirar Safiya ta ɗauko littafi Maryam ta tayata assignment.

"Wani subject ne?" Maryam ta tambaya tana karɓan littafin.

"Chemistry ne. Tun last week aka bamu wai take home assignment na mid term break. Na yi na yi amma na kasa solving. Saboda mugunta a internet teacher ɗin ya ɗauko questions ɗin."

Maryam ta karanta tambayoyin taga ba irin wanda ta saba gani bane. Hannu ta miƙa Safiya ta miƙo mata biro da takarda. Tambayoyi huɗu ne. Ta farko ta fara solving ta maƙale. Ta biyun ma haka. Ta ukun ma haka.

Sau uku tana ƙoƙarin solving questions ɗin tana maƙalewa. Ta daga ido ta kalla Safiya. "Wannan tambayoyin sai ke, na kasa."

"Ki yi wa Allah Yaya ki amsa mun. Wallahi idan ban yi ba kashi na ya bushe. Malamin a bakin get zai tsaya gobe da safe babu damar kwafa a makaranta."

"Ki kaiwa Umma."

"Ita na fara kaiwa ta ce in je in nemo wanda zai mun ita babu mai wasa mata ƙwaƙwalwa tana zaman zaman ta."

Maryam ta tuntsire da dariya. "Bari in gani ko zan iya." Ta yi solving ta samu amsa amma ita kanta ta san ba daidai bane. "Da alama Hajiya Safiya za ki sha bulala gobe."

"Ga shi kuwa Mr. John ya iya duka." Zee ta ce tana dariyar ƙeta.

"Hakanan zan kwafa na ki in rubuta. Ya ga na yi ƙoƙarin yi na kasa. Ni da da wani dan ajin mu a kusa da na je na kwafe wallahi."

"Mutum ɗaya na sani da zai iya yi miki solving questions dinnan."

Tun ɗazu Safiya a tsaye ta ke, jin abunda Maryam ta ce ta zauna kusa da ita da sauri. "Wa kenan Yaya?"

"Mai koya mana karatu a makaranta."

Charaf Zee ta amshe kaman da ita ake magana. "MK ko?"

Safiya ta waiga ta kalla Zee sannan ta maida kallonta kan Maryam. "Waye MK? A ina ya ke?"

"Mai mana karatu na ce miki, kuma yana Zaria yanzu haka."

"Dan Allah Yaya ki kirashi."

"Tabɗi jam! In kira shi in ce mai me? Kuma dai daga abun arziƙin da yake mana a makaranta sai in maida shi kaman wata calculator."

"Dan Allah Ya Maryam ki taimaka. Maki goma za'a ba duk wanda ya yi daidai. Da ban sa rai ba amma tunda akwai wanda zai iya solving yanzu ina so."

"Sai ki sake cire rai."

"Kai mana Yaya. Dan Allah. Ki kirashi ni zan mai bayani idan ba za ki iya ba."

Safiya ta yi ta magiya har saida Maryam ta yarda. Zee aka aika dauko wayar a ɗaki.

"Nima ban san wani karanbanin ya sa na faɗa ba," Maryam ta ce ƙasa ƙasa tana nemo sunan MK a wayarta. "Gaskiya Safiya ki haƙura ba zan iya kiran shi ba."

"Yanzu Yaya maki goman ce ba ki so in samu?"

Safiya harda yin abun tausayi babu yanda Maryam ta iya dole ta kira. Sai dai bai ɗauka. Tana dariya ta ce bai ɗauka ba kuma kira ɗaya zata yi. Bata gama rufe baki ba wayar ta fara ƙara. Dariya ta koma wurin Safiya.

Maryam ta harare ta. "Ki yi shiru to in amsa kin tsaya kina dariya kaman sabon kamu."

Safiya ta yi wa bakinta alaman zip tana ƙunshe sauran dariyar da ke cinta.

"Hello, salamu alaikum."

Daga chan bangaren MK ya amsa cike da fara'a. "Wa'alaikumus salam Maryam."

"Na'am. Ina wuni? Ya gida?"

"Lafiya lau. Kin manta ina makaranta."

Da murmushinta ta ce, "haka. Na manta. Ya makaranta?"

"Gata nan babu daɗi kun gudu kun bar mu. Ya su Umma?"

"Suna nan lafiya."

"To a gaishe su. Ina Zee?"

Ta kalla Zee da Safiya da ke kallonta kaman sun samu talebijin. "Gata nan tana kallo."

Safiya da Zee su ka kalli juna suna tambayan juna da ido wa Maryam ɗin ke nufi.

"Madallah. Duk ki ce ina gaida su."

"Za su ji in sha Allah."

Ganin kaman wayar na zuwa ƙarshe kuma Maryam bata yi maganar assignment ɗin ba, Safiya ta taɓata tana nuna mata takardun da ke baje a ƙasa. Maryam ta harareta Safiya ta rama.

"Ki faɗa mai mana Ya Maryam kar wayar ta tsinke." Ta ce da ƙarfi yanda ta san zai ji.

Aikuwa a kunnen shi. "Maryam me za'a faɗa mun?"

Idanuwan Maryam kaman zasu faɗo dan harara. Safiya kam ko a jikinta sai murmushin nasara da take yi.

"Safiya ce aka bata chemistry assignment a makaranta mu ka kasa solving."

"Harda ke?"

"Harda ni me?"

"Aka kasa solving ɗin."

"Da wahala. Na yi amma na san ba daidai bane."

"Zan ci ki tara idan kin dawo. Yanzu ai kin zama chemistry expert."

Maryam ta yi dariya. "Wannan sai ku ban kai nan ba."

Shima ya yi dariya. "Karanto mun questions ɗin. "Maryam ta karanto mai su gaba ɗaya. "Na san na gobe Monday ne. Yanzu zan yi solving sai in turo miki ta email, ki yi mun sending email address din ki ta text."

"To. Mun gode. Allah Ya saka da alkhairi."

"Ko dai saurayin Yaya ne?" Safiya ta ce tana kallon Zee.

Maryam na kashe wayar ta bi Safiya da gudu. Kaman ƙananan yara suka ruƙa zagaye falon. Haka Umma ta shigo ta same su. Ta yi salati da sallalami.

"Wai lafiyar ƙalau kuwa?"

Safiya na haki ta boye bayan Umma. "Umma wai dan na roƙeta ta kira saurayinta ya mun assignment shine ta ke bina zata duke ni."

Maryam ta makawa Safiya harara. Umma ta yi dariya. "Yaya Maryam saurayi gare ki ban sani ba."

Kaman ƙasa ta buɗe ta nutse. "Umma fa MK ne da yake koya mana karatu fa."

"Ba wani nan Umma kar ki yarda. Ba ki ga yanda ta ke magana ba. Ba ka ma jin abunda ta ke cewa."

"Wallahi Safiya ki kiyaye ni. Ko ya turo solution ɗin ba zan nuna miki ba tunda kin raina ni."

"A'a ke kuwa Maryam, daga wasa. Ko dai dagaske ne."

Maryam ta turo baki tana kallon Umma. Taya zata ce dagaske ne? Tsakani da Allah. Daga ta ce yana koya mata karatu kuma sai a dauko wani zancen daban.

"Zan ga wanda zai nuna miki assignment ɗin." Ta ce wa Safiya sannan ta juya ta tafi ɗaki.

Tana shiga wayarta ta yi ƙara. Har ya yi solving ya turo. Email ɗin ta buɗe, hoton takardar da ya yi solving a kai ya turo. Solution ɗin wurin shafi biyar. Lallai Allah Ya bashi kwakwalwa, ji yanda ya yi solving cikin ƙanƙanin lokaci.

Safiya ta ƙwalawa kira. Sai gata ta zo da gudunta. Wayar ta miƙa mata. "Ba dan halinki ba."

"Na gode Yayata ta kaina."

Dama da littafinta da biro ta zo. Tana kwafa tana jinjina kai. "Amma Mr. John da gangan ya bamu questions ɗinnan. Na tabbata babu wanda zai iya amsa tambayoyin nan daidai."

"Ki ce za'a kama ki kenan." Maryam ta yi dariyar ƙeta.

Safiya bata tanka ba ta cigaba da rubutun ta. Ita babban abunda ke gabanta shine ta kwafe solutin ɗin tas. Daga baya zata ba yayarta amsa.

Tana kwafan layin ƙarshe kiran MK ya shigo wayar. Safiya ta yi gajeren murmushi ta miƙawa Maryam wayar harda kashe mata ido.

'Yarinyan nan ta raina ni,' Maryam ta ce a zuciya. Amsa wayar ta yi su ka yi magana na minti ɗaya ta miƙawa Safiya wayar.

Safiya ta zaro ido. "Me zan yi da shi?" Ta ce da muryar raɗa.

"Oho." Maryam ta bata amsa tana ajiye  mata wayar a gabanta. MK ne ya ce ta ba Safiya wayar.

Safiya na cira idanu ta kara wayar a kunne. "Salamu alaikum, ina wuni?"

"Wa'alaikumus salam Safiya. Lafiya lau. Ya gida?"

"Alhamdulillah. Na gode da solving mun questions da ka yi. Allah Ya saka da alkhairi."

"Ameen babu komai. Dama shi yasa na kira, kin gane steps ɗin kuwa?"

Safiya ta kalla littafin. Ita bata tsaya bin kan ta yanda ya amsa tambayoyin ba. "A'a, ban gane ba." Ta faɗa mai gaskiya dan ta san ko ta natsu ta duba ba fahimta zata yi ba. Gwara kada ta cuci kanta.

MK ya hau yi mata bayani dalla dalla yanda zata fahimta. Safiya ta nutsu tana sauraran sa tana gyada kai. Sun kusa awa ɗaya yana yi mata bayani kaman ba kati su ke ci ba. Inda bata fahimta ba Safiya bata yi nauyin baki ba wurin neman ƙarin bayani.

Maryam har ta fita ta dawo basu gama ba. An gama da tambayoyin assignment ɗin Safiya ta buge da yi mai wasu tambayoyi akan Chemistry ɗin.

Bayan minti talatin da dawowar Maryam ɗakin Safiya ta yi mai sallama ta miƙa mata wayar, tana bata ta fita a ɗakin.

Maryam ta duba mintunan da su ka yi suna waya ta jinjina kai. "Sannu da ƙoƙari, ka haɗu da Safiya sarkin tambaya."

MK ya yi dariya. "Duk tambayarta ai bata kai ki. Idan kika fara gabana faɗuwa ya ke yi kar in je ki ƙureni in kasa bada amsa."

Maryam ta tuntsire da dariya. "Banda sharri."

"Da gaske. Shi yasa na ke yi muku bayani yanda za ku gane dan kar ki yi tambaya."

Maryam ta girgiza kai har yanzu da murmushi a fuskarta. "In dena tambaya kenan."

"A'a ni ban ce ba."

"Sai da safe, dama Safiya ta gama cinye maka kati."

"Ah haba, duka mintin mu nawa. Good night."

Sai da ta kashe Khalid ya sauke wayar shi daga kunne. Hannu ya sa ya shafa sumar kansa da ta ɗan taru. Ya ji daɗin kiran Maryam da kuma magana da ƙanwarta Safiya. Haka na nufi ta fara sakin jiki da shi kenan? Yana fatan hakan.

Shi kaɗai ne a daƙin tunda ya fara solving Nas ya fita dama su biyu suka rage duk sauran sun tafi hutun mid semester. Khalid babu yanda be yi Nas ya tafi gida ba amma sarkin taurin kan nan ya ƙiya. Nas ya yi hakan ne dan kar Khalid ya kasance shi kaɗai.

Har ƙasan ransa Khalid bai so hakan sai dai idan fanni taurin kai ne Nas ya dama shi ya shanye. Shi ya zaɓa ƙin zuwa gida da kanss baya son hukuncin da yanke ya shafi amininsa.

A hankali ya furzar da iska daga bakinsa. Kira wurin uku sun shigo lokacin da ya ke waya da Safiya, sarai ya ga kiran waye ya ƙi ɗauka yanzu baya da niyan kira.

Kaman haɗin baki sai ga kiran ya sake shigowa. Khalid ya tsurawa wayar ido har kiran ya kusan tsinkewa. Ringing ɗin ƙarshe ya dannan wayar ya amsa kiran sannan ya sa speaker.

"Sannun ka Khalid!" Muryar mace ya fito tar muryarta a matuƙar bace. "Wato duk faɗan da muka maka ya shiga ta kunne ɗaya ta fita ta ɗayan. Wai me kake ji da shi ne Khalid?"

Shiru Khalid ya yi bai amsa ta ba. Ta kuwa ƙara tunzura ta inda ta ke shiga ba tanan ta ke fita ba. "Au ka yi shiru ka maida ni mahaukaciya ko?"

Sai a lokacin ne Khalid ya buɗe baki ya yi magana. Idanuwansa tuni suka yi ja suka kaɗa. "Ya Ramlah ni ban son me kike so in ce ba."

"Khaliddddddd...." Ta ja sunan shi da kwantacciyar murya. "Gobe ka taho gida."

Kai ya girgiza kaman tana gaban shi. "Ya Ramlah zuwa na baya da amfani. Ran kowa zai ɓaci ne, gwara in yi zamana. Besides inada abubuwan yi a makaranta, kin san final year na ke."

"Ahh ahh! Daɗin abun dai na yi final year ɗinnan da ban yi ba yau da na sha haushi. So calm down kid! Ni zan baka labarin final year ba kai zaka bani ba."

"Na ji. Ina Ammar?"

"Gashi chan yana wasa. Yanzu Khalid ko dan Mama baza ka je gida ba?"

Khalid ya runtse ido. "Ya Ramlah..."

"Tsakani da Allah Khalid. Ita me ye laifinta? Ya zaka bari laifin su ya shafeta kuma kasan she needs you in that house."

Kalamanta tamkar sukar mashi a zuciyarsa. Hutun da aka yi kafin a dawo first semester dimnan sam bai mai daɗi ba. Dama zaman gidan su ba daɗi ya ke mai ba amma wannan hutun ya fi ko wanne muni. Kullum al'amuran gidan sake taɓarɓarewa su ke yi.

"Zani Ya Ramlah amma ba yanzu ba."

Ya Ramlah ta sauke ajiyar zuciya. "Shikenan Khalid. Tunda ba za ka samu daman zuwa ba dan Allah ka riƙa kiranta a kai a kai."

"Wannan ba sai kin faɗa mun ba. Rana bata fitowa ta faɗi bamu magana aƙalla sau uku ba."

"That's good. Auta kaine ɗan gaban goshi kiranka ɗaya shine namu so hamsin."

"Ke kika sani. Sai anjima."

Khalid ya runtse ido na ɗan wani lokaci maganganun yayarsa na mai yawo a kai. Tabbas Mama na buƙatar shi a kusa sai dai kwata kwata baya iya jure zaman gidan.

Dalilin da ya sa ya tafi boarding kenan tun Js1. Babu wanda ya taɓa boarding a gidan in banda shi. Haka ma jami'a duk yayyun shi BUK su ka yi. Shi kaɗai ya zaɓa ABU ba dan komai ba dan ya yi nesa da gida. Hundred level sai da session ya kusa ƙarewa ya je gida. Shima ba da son ranshi ba, su Ya Ramlah ne su ka yi mai taron dangi dole ya tafi.

Babu abunda ya ke so a duniyar nan sama da mahaifiyarsa. Bai haɗa sonta da komai ba amma saboda wasu dabi'u nata dole ya ke nisantar kan shi daga gareta.

Idanuwansa suka faɗa kan takardun da ya yi wa Safiya solving tambayoyi. Amma ba tunanin Safiya ya ke yi ba tunanin yayar Safiya ya ke yi.

Har yanzu yana mamakin kansa yanda ya ke ji game da Maryam. Wannan yanayi baƙo ne a wurinsa, bai taɓa jin haka akan ko wace mace ba.

A kalan gidan da ya tashi bai taɓa tunanin zai ji sha'awar yin soyayya ba sai gashi ta kama shi farat ɗaya.

Yana maraba da ita. Zaita daƙon abunsa har sai lokacin saukewa ya yi domin a rayuwa komai lokaci ne.

Wayarsa ya ɗauka ya kara a kunne bayan ya yi dialing yana cewa, "Hello Mama..."



****

Ranan talata Umma ta dawo daga wurin aiki ta dawowa Maryam da albishir.

"ʼYar mitsilan Abba kin san me ya faru?"

Maryam na kan kujera hankalinta a kan film ɗin da take kallo. Ɗauke idonta ta yi daga kan TVn ta maida su kan Umma.

"Ban sani ba Umma sai kin faɗa."

"Yau wata dattijuwar patient ɗina na ji tana neman masu yin snack ɗiyarta ta haihu za su yi taron suna ranan juma'a, ni kuwa na ce mata ta kawo yarinyata ta iya."

Maryam ta zaro ido. "Kika ce mata Umma? Kuma ta baki?"

"Me ye kike wani zaro ido, baza ki iya bane in ce ta nema wasu?"

"A'a ba haka bane Umma. Kawai dai ina tsoron kar in yi ba daidai ba in yi mata asara."

Umma ta yi murmushi. "Yaya Maryam ai sai da gwaji ake ƙwarewa. Idan kina tsoro ba za ki taɓa ganin progress ba. Meatpie kaɗai ta ce take so kin ga kuwa kin yi meatpie a gidan nan yafi a irga ko ba haka ba."

Maryam ta gyada kai. "Hakane." Duk cikin snacka shi tafi yi saboda son da Baba Malam ke wa meatpie.

"Yanzu dai na karɓa lambarta na ce zan kirata in faɗa mata nawa kuɗin zai kama."

Chan ƙasa ranta fargaba ne da tsoro amma hakan bai hanata murna ba. "Ina zuwa Umma," da sauri ta shiga ɗaki cikin litattafanta ta ɗauko wata memo.

A makarantar koyar abincin harda yanda zaka fara sana'a aka koya musu. Yanda za cire riba da sauran su. Falo ta koma ta zauna kusa da Umma.

"Pieces nawa ta ke so? Sai an je kasuwa an ji farashin kayan aikin tukun za'a san nawa kuɗin zai kama gaɓa ɗaya."

"Pieces hamsin ta ke so."

Dama idan zata yi na gida ita da Hamida su ke zuwa su siyo kayan aiki. "Gobe sai mu je kasuwa da Hamida."

Umma ta ce Allah Ya kaimu. Tana ganin yanda Maryam ɗin ta kasa boye murnarta. Ta yi murmushi ta shiga ɗaki a zuciya tana yi mata addu'ar dacewa. A fili kuwa ta ce, "Allah sarki Ahmad. Allah Ya kai haske ƙabarinka."










~Maymunatu Bukar💕

Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro