Chào các bạn! Vì nhiều lý do từ nay Truyen2U chính thức đổi tên là Truyen247.Pro. Mong các bạn tiếp tục ủng hộ truy cập tên miền mới này nhé! Mãi yêu... ♥

13.






Yau Alhamis zasu rubuta test din Chemistry. Kusan kwana karatu Maryam ta yi. Karatun take yi amma ji take yi kaman ana goge wanda ta fahimta a baya.

Sati ɗaya da fara test din su kenan. Sun yi paper huɗu wannan ce ta biyar. Yau ne kuma zata fara rubuta ɗaya daga cikin courses ɗin da ke sakata fargaba.

Paper ɗin rana ce ƙarfe biyu. Dalilin haka MK ya ce ze yi musu revision kafin su shiga jarabawar. Yanada classes amma ya ce zai kashe class ɗin ranan saboda su. MK ba dai mutunci ba. Yanda kasan ƙannensa haka ya ke yi musu. Ba zai taɓa yi musu karatu ya ƙi rako su hostel ba.

Sun yi dashi zasu haɗu a rainforest dake Department Of Biology ƙarfe goma. Tun asuba ita, Hamida da Sumayya su ka yi wanka. Sumy kusan ta dawo ɗakin su da zama. A nan take kwana tun ana sauran sati ɗaya a fara test.

"Maryam kira shi ki ce mai mun fito tunda ba da waya zamu tafi ba."

Bata taɓa kiran shi ba amma tanada lambar shi a wayarta. Kullum sai dai Hamida ko Sumayya su kira shi. Bugu biyu ya ɗauka.

"Hello, salamu alaikum, ina wuni? Maryam ce."

"Wa'alaikumus salam Maryam. Kun fito?"

"A'a. Yanzu dai zamu fito. Shine na ce bari in kira ka tunda a ɗaki zamu bar wayoyin mu."

"Okay. Ina wurin already sai kun ƙaraso."

Su ka yi sallama ta kashe wayar. "Ku mu yi sauri fah yana jiran mu."

Sumayya da ke saka hijabi ta ce, "Hajiya Hamida za ki cewa ta yi sauri dan ni na shirya."

Hamida ta harareta tana ƙoƙarin ciro kaya daga locker. Ko me ta tsaya yi? Oho. Ko kaya bata saka ba bayan ta riga kowa yin wanka. Maryam ta yi ta azzazalata dan yanda bata so ta jira wani haka bata son sa wani jiranta.

"Ahh Maryam ki yi a hankali mana kar kisa in yi mantuwa."

"Naga ba ki da niyar gamawa ne ai. Ƙarfe goma har ta wuce fa tsakani da Allah. Kuma tun ɗazu yana wurin yana jiran mu."

"Yi haƙuri Yaya Maryam yanzu zamu tafi."

Maryam ta juya idanunta. Tana tsaye a bakin ƙofa ɗauke da duk wani abu da zata buƙata.

"Kin ɗauka handout ɗin da zamu yi revising da shi?" Hamida ta tambaya.

Maryam ta ɗaga mata littafin dake hannunta. Sai goma da rabi suka bar ɗakin. Maryam na ta yi musu mita.

"Wallahi kuka ja ya yi fushi ya ce ya fasa yi mana karatun ko ma ya daina gaba ɗaya ni da ku ne."

"Ya kike haɗawa da ni wai. Ke da ita dai. Ni ai na shirya da wuri." Sumayya ta yi saurin cewa.

"Ni dai na faɗa muku. Sai ka ce mun ajiye shi, mu da muke nema amma mu ke ɓata mai lokaci. Mu ya kama mu jira shi, ba shi ya jira mu ba."

"MK ai namu ne nasan zai fahimta. Kuma Yaya Maryam ai bamu taɓa latti ba sai yau. Ze yi mana uzuri."

Maryam ta gallawa Hamida harara. "Ke kika sani kuma Yaya Maryam dinnan ya fita a bakin ki."

"Haba Yayata ta kaina."

Duk abunta sai da ta yi dariya. In dai fannin tsokana ne babu wanda ya kai Hamida Bello ƙwarewa. Ko baka yi niya ba sai ta saka ka dariya.

Dayake wurin babu nisa daga hostel ɗin su nan da nan suka isa. Maryam ta fara ganin shi. Yana zaune kan tebur kansa a ɗuke yana rubutu. Tebur ɗin babba ne amma shi kaɗai ne a zaune. Kuma wurin a cike ya ke ga wasu ma a tsaye. Babu mamaki ya hana su zama ne ya ajiye musu seat ɗin.

Kaman an ce ya ɗago kai suka haɗa ido. Babu dama ta kauda kai sai ta yi mai murmushi ya mayar mata da martani.

Murmushin kan idon Hamida sai kuwa ta ce, "Yauwa! Bai yi kama da wanda ya yi fushi ba."

MK ya kalle ta. "Fushi kuma?"

"Eh. Tun ɗazu Maryam ke mun masifa wai mun ɓata maka lokaci ka yi fushi."

MK ya maida kallon shi kan Maryam dake hararar Hamida. To meye na faɗa mai. MK ya yi dariya amma bai ce komai ba. Daga nan kowa ya ci serious suka fara abunda ya kawo su. MK ya yi musu tambayoyi da baki suka amsa duka sannan ya basu wasu questions daga PQ ya ce su yi solving.

"Masha Allah! Haka nake so."

Sun amsa duka questions ɗin ba tare da sun yi kuskure ko ɗaya ba.  Hakan ya yi mai daɗi matuƙa. Da daɗi kana koyawa mutum abu yana fahimta ba ka yi ta bata lokaci ba amma baya ganewa. Hakan ne zai bashi ƙarfin gwiwar cigaba da koyar da su.

Ƙarfe ɗaya saura suka je sallah a Geography Mosque suka dawo suka cigaba. Ɗaya da rabi MK ya ce to a tsaya haka nan.

"Kun gama shiryawa. Marking scheme zaku basu."

"Da sauran lokaci fa, Maryam ta ce tana sake buɗe handout ɗin da ya rufe. "Ba zamu ƙara duba wani abu ba?"

MK ya janye handout ɗin daga gabanta. "Babu wani abu da baki sani ba Maryam."

"Ji nake yi kaman brain ɗina is empty."

MK ya yi murmushi yana kallon yanda take bubbuɗe takardun tana dubawa. "It's normal to feel that way. In kika cigaba da duba littafi za ki ruɗa kan ki kawai.  In koya miki addu'ar da nake yi whenever I am scared?

Maryam ta daga kai da sauri. Daga gani a tsorace take da test ɗinnan.

"Allāhumma lā sahla illā mā jaʿaltahū sahlā, wa anta tajʿalu-l-ḥazna idhā shi'ta sahlā. Ma'anar addu'an shine, 'Ya Allah babu sauƙi face a cikin abinda Ka sawwake, kuma Kana sauƙaƙa wahala idan Ka so.' Ki yi ta maimaitawa Allah zai kawo miki sauƙi."

"Ita kaɗai zata riƙa maimaitawa?" Hamida ta ce tana kallon shi.

MK ya yi dariya. "Harda ku Hamida. Allah Ya bada sa'a."

"Ameen mun gode. Sumy tashi mu tafi. Yaya Maryam sai mun haɗu a ɗaki. Allah Ya bamu sa'a."

"Ameen." Maryam ta amsa. Hamida da Sumayya suka yi gaba. Maryam ta tattara kan takardunta ta miƙe. "Mun gode sosai. Allah Ya saka da alkhairi."

"Ameen Maryam. Ina ne venue ɗin ki?"

"Department."

"Hanyar mu ɗaya ashe, nima department zani. Mu tafi tare."

Ta ce mai toh suka jera suna tafiya a hankali. Ya san da shi kaɗai ne da tuni ya yi gaba. Gimbiyar kuwa da ɗaiɗai take tafiya dolen shi ya yi matching steps ɗinta.

Makarantar is busy kamar kullum. Dalibai nata hada hadarsu. Khalid ya kalla Maryam dake gefen shi tana magana ƙasa ƙasa tana wasa da yatsunta. Yana ganin tsakiyar kanta, dukanta bata kai kafaɗarsa ba.

"Cramming kike yi?"

"Ina gani ne ko ban manta abunda na karanta ba."

"Ki kwantar da hankalin ki. Tambayoyin da zasu fito bara su wuce inda muka karanta ba. So, you're good to go."

"Allah Ya sa."

"And Chemistry is one of the easiest courses a makarantan nan."

"Hmmm mmmm!" Maryam ta ce da ɗan ƙarfi. "Lallai ma! Kawai kana cewa hakane saboda you are good at it."

"Kema ai kin iya yanzu. Ko baki iya ba?"

"Na iya amma kaɗan. Kai kuma ka iya sosai sosai shi ya sa kake cewa Chemistry is easy."

Khalid ya yi dariya. "Toh I will make sure kema kin iya sosai sosai har kema ki faɗawa wasu cewa Chemistry is easy."

"Allah Ya sa toh. Ni na gaji da Chemistry ɗinnan."

"Yanzu kika fara Chemistry ai. Ko kin manta Biochemistry kike?"

"Ban manta ba. Ni dai da ba'a bani course ɗinnan ba."

"Wani course kika yi applying?"

"Pharmacy."

Khalid ya gyada kai. "Da shi kika samu you'll still be doing Chemistry ai."

"Hakane."

"Ki sa a ranki course ɗin da sauƙi, amma idan kina tsoro shi zai hana ki fahimtar abunda kike koya."

"Toh in sha Allah. Na gode."

A gaban Department Of Biochemistry su ka tsaya sun fuskantar juna. "Kada ki yi saurin answering question, ki tabbata kin fahimci tambayar tukun. Ki yi ta maimaita addu'ar nan. Allah Ya bada sa'a."

"Ameen Ameen. Na gode."

"Ba komai. Books ɗin ki ya zaki yi da su?"

"Nima ban sani ba. Kar in ajiye a ɗauke mun."

"Kawo in saka miki a jaka. Idan kin fito sai ki kirani in kawo miki."

"Amma wayana na hostel fa."

"Babu damuwa, in kin koma hostel ɗin zan kawo miki."

Takardun ta miko mai. "Na gode sosai."

Khalid na tsaye har Maryam ta haye saman department ɗinsu. Handout din dake hannunsa ya kalla. Ta rubuta sunanta a jiki 'Maryam Ahmad'.

Dagaske bata gane shi ba. Tunda ya fara musu karatu ya ke jira yaga ranan da zata tuna sun taɓa haɗuwa amma har yau shiru. Dariya abun ke bashi. Ya lura ita karatunta ne kawai a gabanta. Duk sauran abubuwan bata damu da su ba. Tunda suka fara karatu bai ga ƙawar dake tare da ita ranan da ya fara ganinta ba. Ya mance sunanta. Ya san ita zata gane shi, sai ta tunawa Maryam.

Amma hakan ma ya mai. Ya samu second chance ɗin first impression. Tunda wancan ranan kaman ranta a ɓace ya ke shi yasa ma ko kallon arziƙi bata yi mai ba.

Department ɗin su ya gangara. Classes gare shi tun ƙarfe tara zuwa ƙarfe ɗaya amma bai yi attending ko ɗaya ba. Addu'ar shi Allah Ya sa malaman ba su yi shotgun ba. A kan stairs ya samu abokansa zaune suna hira.

"Shege MK! An dawo kenan." In ji Nasir yana dariyar shaƙiyanci. "Har ka gamawa 'yan matan naka karatu? Amma guy ɗinnan ya bani mamaki ranan fa. Babu jayayya kawai ya ce musu eh. Ni kuwa ba irin roƙon da ban mai ba ya koyawa wata babe ɗina karatu ya ƙiya."

"Ba kai kaɗai ba fa Nas." Wakili ya ce. "Nima ba ƙaramin mamaki na yi ba. MK da tutorial! Abunda ban taɓa gani ba. Gashi har classes ya yi missing yau saboda su. Anya kuwa abokina?"

"Kuma kun san dole da walakin goro a miya mana. Ba hakanan MK ze yi missing class ba." Wani a cikin su ya ce.

"Abokina! Matso ka faɗa mun wace ce a ciki?" Nas ya ce yana rataya hannunsa a kafaɗar Khalid. "Su uku ne kuma dai na san kai ba mai zari bane. So, wace ce a ciki? Akwai biyu dogaye suna da ɗan haske sai mara tsawon cikin su ita tafi su duhu. Wata ƙarama haka, ʼyar cute da ita kaman baby doll."

Da sauri Khalid ya ɗaga kafaɗarsa hannun Nas ya faɗi. Me Nas ze yi idan ba dariya ba, harda ihu. "Wallahi ita ce! Ƙaramar ce! Woah abokina kana wuta! Ka gabatar da kan ka ko ka tsaya sanya."

Khalid ya yi tsaki yana girgiza kai. "Kai fa baka da hankali. Gashi kana nema ka tara mana mutane."

"Ahh ahh! MK! MK! MK nawa! Yanzu dai ka yi biyayya in maka bayanin yanda zaka tsarata.....ka daina wani girgiza kai. Wallahi ka tsaya sanya a gaban idonka wani ze yi wuff da ita. Bare irin su ʼyan ƙananan nan shiga rai ne da su."

Khalid ya kai mai duka Nas ya kauce yana dariya. Haka suka sa shi gaba babu bakin ramawa.

A bangaren Maryam kuwa tana isa aka fara checking. Har yanzu basu karɓa ID card ba, da Course Form kaɗai suke amfani. An zaunar da su an bada space sosai. Addu'ar da MK ya koya mata take ta maimaitawa har aka kawo question papers da rough sheets.

Bayan minti goma invigilator ɗin ya ce zasu iya farawa. Sai da ta tofe question  paper ɗin da addu'a sannan ta juya. Zuciya na dukan uku-uku ta fara karanta questions ɗin. Objectives ne guda arba'in.

Habawa! Maryam na fara karantawa sai murmushi. Ta hango guda kusan biyar sak irin wanda suka yi solving da MK ɗazu. Sauran kuma tana da tabbacin zata iya amsa su.

Tunda da ɗuka bata ɗago ba. Solving kawai take yi tana murmushi. Ta amsa extra rough sheet har uku. Ko question ɗaya bata tsallake ba duka sai da ta yi solving ɗin su kuma amsar na cikin options ɗin.

Tunda ta fara test bata yi paper ɗin da ta kai wannan daɗi ba. Kai Masha Allah! Allah Ya yi wa MK albarka.

A gaban department taga Zuby a tsaye. Basu haɗuɗuwa sosai tunda aka fara test. Yanayin karatun su ba iri ɗaya ba. Maryam ta taka zuwa inda Zuby take suka gaisa.

Zuby ta rungumeta. "Karatu ya boye ki Maryam."

"Ko dai ya boye ki Zubaida. Da kyar ake ganin ki."

"Ke dai bari. Dole in boye dan kar a riƙa baje ni irin na yau. Kai test ɗinnan ya yi wahala."

Mamaki ya kama Maryam. Ita kuwa babu test ɗin da ya kai wannan sauƙi. "Ni kuwa bai yi mun wahala ba."

"Wannan da muka gama rubutawa? Haba Maryam faɗa kawai kike yi."

"Ban gane faɗa kawai nake yi ba. Idan ya yi mun wahala zan ji kunyar faɗa miki ne Zuby?"

Zubaida ta gyada kai. "Allah dai Ya bamu sa'a gaba ɗaya kawai."

"Ameen."

Tare su ka koma hostel Maryam ta shige Ribadu Zuby ta ƙarasa Amina. A ɗaki tana buɗe ƙofa Hamida ta yo kanta tana ihun murna.

"Maryam kin ga questions? Wayyo Allah! Solving kawai na ke yi kafaɗuna a ɗage!"

"Kai Masha Allah! Allah Ya biya MK da gidan aljannah." In ji Sumayya itama tana murmushi.

"Ameen. Yanda wannan ta yi sauƙi in sha Allah haka sauran za su yi sauƙi."

"In sha Allah!"

Jiya da dare babu wanda ya samu isassashen bacci a cikin su. Bayan sun yi sallar la'asar sun ci indomie duka suka kwanta bacci. Maryam ta fara tashi gab da Maghrib. Gobe juma'a kuma ba su da paper sai wani satin dan haka yau da dare babu wani karatun da zata yi. Kwakwalwarta ta samu ta huta itama.

Sauran kayan miyan da ya rage ta ɗauka ta yi grating. Motsinta ya tada Hamida da Sumayya.

"Yau ba karatun da zan yi." Hamida ta ce tana miƙa.

"Kaman kin shiga zuciyata. Abunda na gama tunani kenan." Cewar Maryam.

"Ni ma dai." In ji Sumayya. "Maryam me kike dafa mana?"

"Macaroni zan dafa. Miƙo mun sardine a cikin locker dama ke nake jira ki tashi."

Maryam ta dafa musu Macaroni mai dan karen daɗi su ka ci a plate ɗaya kaman yanda suka saba.

Bayan sallar isha'i kiran MK ya shigo wayarta. "Hello Maryam. Gani a gaban hostel ɗin ku."

"Okay to, gamu nan zuwa." Ta ce sannan ta kashe wayar. "Ku tashi mu je MK na gaban hostel."

Hamida ta kalleta ƙasa-ƙasa. "Me ya kawo shi gaban hostel kuma."

"Ɗazu na bashi handout ɗina ya ajiye mun dan kar a sace."

"To mu meye namu? Ki je ki karɓa handout ɗin ki mana."

"Ban son iskanci Hamida. Sumayya tashi mu je."

"Yaya Maryam ke fa ya zo gani ba mu ba." Sumayya ta yi dariya.

Maryam ta yaƙune fuska tana kallonta. Ita yazo gani? Ya dai zo bata handout ɗinta. "Ya dai zo bani handout ɗina. Dallah ku tashi mu je. Kenan baza ku mai godiya ba yanda ya taimake ku paper ɗinnan ta zo muku da sauƙi ba."

"Godiya kuma so nawa zamu mai. Ai har ya gaji da jin godiyar mu. Ke fa kullum muka gama karatu sai kin yi mai godiya."

"Ha'an! To laifi ne? Abu dai ana maka kyauta ai dole ka gode."

"Ni ban ce laifi bane. Godiya ai abu mai kyau ne. Ki cigaba, haka ake so."

"Wallahi Hamida kin raina ni."

"Ni na isa Yaya Maryam? Ai ban isa ba. Allah Ya huci zuciyarki."

Duk yanda ta yi dasu suka yi mursisi suka ƙi rakata dole ta fita ita kaɗai. Yana zaune kan kujerun kankare dake gaban hostel.

Yana hango ta ya miƙe tsaye. Ta gaishe shi ya amsa ya tambaye ta ya paper. Wani murmushi ta yi, she looked so cute and young.

"Ya yi sauƙi sosai!" Ta ce da murna a muryarta.

Khalid ya yi murmushi. "Alhamdulillah. Haka na ke son ji. In yi expecting forty over forty kenan."

Maryam ta yi dariya. "Forty? A'a ba dai forty ba."

"Thirty nine toh."

"Na san dai I won't score less than twenty."

Khalid ya girgiza kai. "Twenty ya mun kaɗan gaskiya. I want at least eighty percent. Thirty two kenan."

"Allah Ya sa, nima zan so hakan."

"I trust you, na san you will score higher than that ma." Jakarsa ya buɗe ya ciro takardunta. "Ga books ɗin ki."

"Na gode. Sai da safe."

"Sai da safe Maryam."

Ya so hirar su tafi haka tsawo amma bai ce komai ba ya barta ta tafi. Kamar kullum sai da yaga ta shiga ciki sannan ya juya.

Wurin Nasir ya isa a 90s inda ya ke jiran shi. Nas na ganin shi ya ɓata rai. Sun yi da shi zai raka Khalid wurin Maryam, Khalid ya saɓe ya tafi ba tare da ya sani ba. Haka nan Nas ya je ya faɗa wani abun da zai sa Maryam ta ƙi shi. Bakin Nasir sam baya da control. He is not willing to take that risk.

"Ka faɗa mata ko kuwa?" Nas ya tambaye shi bayan ya gama ƙorafin Khalid ya tafi ya bar shi yana jira.

"Nasir ka rabu da ni." Ya ce yana zama kan kujerun kankare dake jere a wurin.

Nasir ya yi tsaƙi yana kallon shi cike da takaici. "Allah Ya sa wani ya yi wuff da ita muga tsiya."

Ba Ameen ba. Khalid ya ce zuciya. Bai ba Nas amsa ba ya cigaba da harkar da ke gabansa. Matslar shi ne bai san ta inda zai fara faɗawa Maryam ba. Shi a ganin shi ya yi wuri ya fallasa mata sirrin da ke zuciyarsa. It's too early. Zata ga kaman dama manufarsa kenan da ya yarda ya yi musu karatu. Wanda ba ƙarya bane amma baya so ta san haka. Dan haka ya yanke shawarar bin abun a sannu.

When the right time comes, zai sanar da ita. Tsoron shi ɗaya kar addu'ar Nasir ta karɓu. Kai ya girgiza yana kawar da tunanin gefe. In sha Allahu hakan ba zai faru ba.












~Maymunatu Bukar💕

Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro