Chào các bạn! Vì nhiều lý do từ nay Truyen2U chính thức đổi tên là Truyen247.Pro. Mong các bạn tiếp tục ủng hộ truy cập tên miền mới này nhé! Mãi yêu... ♥

11.






For zainabu-abu and Khadijah__yusuf your comments keep me going. Nagode❤️






Zuwa yanzu Maryam ta gane kan karatun. Tun satin farko ta siya duk wani handout da ya kamata. Ta maida hankalinta sosai kan karatunta.

Tana matuƙar kewan Ummanta da sauran ʼyan gidan. Kullum sai sun yi waya. Har yau dai bata je weekend ba amma kullum tana waƙar zuwa. Baba Malam ya ce mata ta dage ta kai mid-semester.

Zaman hostel ne har yanzu ta kasa sabawa da shi musamman bayi. Gashi dalibai sun gama dawowa kan ka ce me bayin ya yi gaja-gaja babu kyan gani.

Ranan nan Zubaida ta ja su karatu da daddare Maryam ta ga irin gagari da ake yi cikin makaranta kafin ma a samu wurin zama. Lokacin da suka ɗauka suna neman aji ya isa mutum ya karanta shafi biyu na handout. Sannan wurin cike yake ga hayaniya bata ma fahimci abunda ta karanta ba.

Tun lokacin ta ce ba da ita za'a yi wannan ba. Zuby babu yanda ba ta yi ba akan zasu nemo wani wurin amma ta ƙi yarda. Tunda Allah Ya sa su biyu ne kaɗai a ɗakin su a nan ta ke karatu ita da Hamida. Suna karatun su lafiya ƙalau ba tare da wata matsala ba. Idan abu ya shigewa ɗaya daga cikin su ɗaya ta yi mata bayani. Idan su ka maida hankali sai su yi awa uku suna karatu ba tare da sun yi wa juna magana ba.

Ranar ta kasance asabar babu lectures. Ba su tashi ba sai wurin sha ɗaya da rabi. Wanka su ka fara yi sannan Maryam ta dafa musu indomie. Tunda miyar da Umma ta yi musu ta ƙare su ka gane shayi ruwanae. Ashe miyar nan ba ƙaramin taimakon su take yi ba. Yanzu sai dai su ci indomie ko kayan madara irin su corn flakes da sauran su.

Tunda Maryam ce ta girka Hamida ta ɗauke plate ɗin da suka ci abincin ta haɗa da tukunyar ta tafi waje ta wanke. Ta dawo ta tsaya waje, daga  bakin ƙofa ta ce, "Gaskiya ya kamata mu yi miya. Na gaji da cin indomie."

Maryam ta daga kai ta kalleta. "Ina zamu samu kayan miya?"

"Ba mun ga kasuwa ranan ba? Ba za'a rasa a ciki ba. Tunda ba abunda mu ke yi shirya mu je."

Dogayen hijabai suka zumbula suka fita. Ashe kasuwar nada girma sosai. Daga waje sai ka ganta ƙarama sai ka shiga zaka ga ainihin girmanta. Sun siya kayan miya sannan su ka bada aka markaɗa musu a wurin.

Hamida ta tambaya mai kayan miyan ko akwai wurin da zata samu naman shanu. Ya yi musu kwatancen wurin a nan cikin kasuwar. Kafin ma su shiga wurin suka san baza su iya siyan naman ba saboda ƙazantar wurin.

Maryam ta kawo wata shawarar. "Mu siya gasasshiyar kaza mana mu saka a ciki, ko ya kika gani?"

"Hakan ya yi."

A social centre su ka siya kazar sannan su ka koma ɗaki. Gaba ɗaya yinin ranan miya su ka tsaya yi. Maryam ta kira Umma ta tambayeta ya ta yi miyar dan ta daɗe kuma bata lalace ba.

"Ku tafasa kayan miyan har sai ruwan ya ƙone sannan ko soyata sosai da wuta kaɗan."

Haka suka yi. An ƙona kaninzir dai ba kaɗan ba. Shinkafa suka dafa daman sun siyo salad suka haɗa da shi.

Miyar ta kwanan musu biyu. Tun daga ranan su ka gane yin miya. Basu bari ta ƙare musamman da kai ya fara daukan zafi.


***

Ƙarfe biyar Maryam da Zuby su ka fito da theatre ɗin da su ka yi lectures din Physics a nan Faculty Of Engineering. Ganin irin chinkoson da ake yi wurin fita Maryam ta ja Zuby gefe suka tsaya har chinkoson ya ragu.

Gaba ɗaya a gajiye take. Yau tun ƙarfe bakwai ta fito ko komawa ɗaki bata yi ba. Yunwa ce ke cinta kamar ta ci babu.

"Maryam dan Allah rakani Comm market in siyo madara."

"Kai Zuby. Gaskiya ba zan iya ba wallahi har wani jiri-jiri na ke ji."

"Minti biyu fa kawai Maryam. Dan Allah."

Ita bata cika so ana mata magiya ba duk sai ta ji an kashe mata jiki. Hakanan ta danne ta ce su je amma tana wuce minti biyu zata tafi ta barta. Zuby ta yi murmushi suka tafi.

Ba su kai ga barin Faculty ɗin ba Maryam ta ji mutum a gefenta ya jera da ita yana tafiya. Ta daga kai taga waye dan ta tsorata. Mutumin ya yi mata murmushi haɗe da yi mata sallama.

Ƙasa-ƙasa ta amsa. Ya yi wa Zuby sallama sannan ya dawo da hankalin shi kanta. Surutan da kwatakwata ba fahimta ta ke yi ba ya hau yi. Ta lura wasu cikin samarin makarantan nan basu da aikin yi sai bin mata a hanya musamma freshers. Wasu ki ga su yi ta washe baki kaman sun samu abun arziƙi. Ita haushi suke bata.

"Zubaida ƙawar nan taki ko bata magana ne?" Ya ce yana wani yashe haƙora.

Zuby ta yi dariyan da ya ba Maryam haushi kaman ta mangareta. Ko yaushe ta faɗa mai sunanta ma oho. "Tana yi kawai dai ta gaji ne. Tun ƙarfe bakwai muke lectures sai yanzu muka gama."

"Wai! Wai! Dole kuwa ta gaji. Sorry."

A ƙofar wani shago suka tsaya Zuby ta ce, "bari in yi sauri in siyo. Jirani a nan."

Bata ma tsaya Maryam ta amsata ba ta tura kai ta yi gaba abunta. Zuby ma bata da tunani wallahi. Yanzu ta tafi ta barta tsaye da shi. Ko kallon gefen da yake bata yi ba shi kuma ya ƙi tafiya gashi bata so ta daga kai su haɗa ido.

Tana ko daga kai suka haɗa ido ya yi mata murmushi. "Na zata ba za ki kalleni ba ai. Nasan kina cewa wannan ya cika naci ya ƙi tafiya."

Bai yi ƙarya ba kusan hakan take tunani amma sai ta bige da mai yaƙe.

"Sunana Khalid. Ina studying Chemical Engineering. Final year."

"Maryam, Biochem. Hundred level."

Yanda ta yi maganar ya ba shi dariya. "Nice to meet you Maryam. Bari in tafi kafin in yi overstaying welcome ɗina. In sha Allah we will meet again soon. Bye."

Bai daɗe da tafiya ba Zuby ta dawo. Waige waige ta fara yi. "In ya ke?"

"Wa?"

"Khalid mana."

Harara Maryam ta galla mata ta yi gaba. Da sauri Zuby ta kamota. "Ke Maryam Allah ba haka a ke yi ba. Ki chanza wallahi."

Maryam ta ci burki ta kalli Zuby cike da mamaki. "Me na yi?"

"Kin wani haɗe girar sama da ƙasa kaman fuskar ki bata taɓa sanin me ye raha ba. Haba dan Allah."

Yau taga ikon Allah. "Kawai sai in fara wage mai haƙora akan wani dalili?"

"Ni ban ce ki wage mai haƙora ba amma at least smile mana. Yaro dan kyakkyawa da shi yana miki magana kina wani basarwa."

"Ni na roƙe shi ya yi mun magana? Ki ji ki da wani zance. Kuma kawai dan kyakkyawa ne sai a ka ce dole sai na kula shi. Ke kika lura da kyan shi ma dan ni yanzu ko sake ganin shi na yi ba lallai in gane shi ba."

"Ni dai na faɗa miki ba haka a ke yi ba. Ba'a wa namiji wulaƙanci wallahi."

Iko sai Allah! Ko me ya kawo zancen nan oho. Ita ta yunwar da ke cinta ta ke yi ba ta namiji ba. Kuma ma meye abun wulaƙanci a abunta ta yi. Maganar ce bata da ra'ayin yi, to dole ne? Ba zata iya tsawaita zancen ba dan haka ta share Zuby su ka cigaba da tafiya.

A ƙofar hostel ɗin su Maryam su ka yi sallama. Da kyar ta kai kanta ɗaki. Tura ƙofar ɗakin ta yi tana cewa, "Hamida Muhammad Bello kin dafa mun abinci?"

Baƙuwar fuska ta gani tsaye a tsakiyar ɗakin. To ko dai ba ɗakin su ta shiga ba? Fitan da zata yi taga ashe bata iso block ɗin su ba, block B ta hayo. Kunya kaman ta nutse da sauri ta ba yarinyar haƙuri ta janyo mata ƙofarta.

"Wayyoooo." Maryam ta ce tana jan ƙafa.

Yanzu sai ta sauka ta ƙara hawa block ɗin su. Yau dai ba ƙaramar wahala ta sha ba. Rabon da ta sha wahala haka tun farkon zuwan su.

A daddafe ta kai ɗakin su. Ta samu Hamida da ƙawarta suna cin abinci. Ko hijab bata cire ba, jaka kawai ta ajiye ta ɗauko cokali. Bata dawo hayyacinta ba sai da cikinta ya ɗauka.

"Sannu," Hamida ta ce tana miƙa mata pure water.

Kai Maryam ta gyada ta shanye ruwan nan tas. "Wayyo! Yau na sha wahala. Anya gobe zan je lectures kuwa?"

"Eh dole ki ce haka saboda kin waye. Wayaga Maryam na cewa ba zata aji ba."

"Ke ba ki san irin baƙar wahalan da na sha yau ba."

"Ko ma meye dole ki je aji ko in kira Umma ehe. Sumayya ga ƙanwata Maryam, Maryam ga Sumayya."

Maryam ta harari Hamida da ke dariya. "Shekara nawa na baki?"

"Duka wata huɗu Hajjaju bai kai shekara ba."

Maryam ta maida kallonta kan ƙawar Hamida. "Yi haƙuri Sumayya, na dawo ba'a hayyacina ba. Ya kike? Ya makaranta?"

Sumayya ta yi murmushi. "Lafiya lau."

Maryam ta miƙe tsaye sai a sannan ta cire hijabinta. Gado ta haye Hamida na ce mata kar ta yi bacci dan an kusa kiran Maghrib.

"Ba bacci zan yi ba," ta faɗa tana danne hamman da ta taso mata.

Daga runtsawa bacci ya yi gaba da ita sai ji ta yi Hamida na tada ta ta yi sallah. Bayan ta idar ta tambaya Hamida ina ƙawarta.

"Bata daɗe da tafiya ba. Ga popcorn."

Ledar da Hamida ta wurgo ta chaɓe. Ranan bata yi karatu ba. Kuma Allah Ya so ta washegari sai ƙarfe sha ɗaya take da aji.

Washegari da safe har Hamida ta gama shiryawa Maryam bata san an yi ba. Misalin ƙarfe tara kiran Umma ya tada ta.

"Maryam ya na ji muryar ki haka ba ki da lafiya ne?"

"Lafiyata ƙalau Umma, bacci na ke yi shi yasa."

"Babu class ne kike bacci har wannan lokacin?"

"Akwai, sai ƙarfe sha ɗaya amma."

"Oh to, a dai maida hankali." Umma ta ce. Daganan ta yi shiru na dan wani lokaci kafin ta sake magana. "Rasuwa aka yi Maryam."

Da sauri ta miƙe zaune saurin baccin ya wartsiƙe gaba ɗaya. Gabanta na faɗuwa ta tambaya, "Wa ya rasu? Inna lillahi wa inna ilahi raji'un!"

A duk sanda ta ji labarin mutuwar wani sai ta tuna da Abbanta. Shekaru sun gushe amma kullum ƙewarsa ƙaruwa take yi a zuciyarta.

"Matar Baba Zubairu Allah Ya yi wa rasuwa yau da asuba."

"Allahu Akbar! Allah Ya jiƙanta da rahama. Allah Ya bata ikon amsa tambayoyin ƙabari. Wayyo Anti Ladidi. Ta yi rashin lafiya ne?"

Idan aka sanar da kai mutuwan mutum mu'amalar ku ta ƙarshe ke fara dawo maka. Shi yasa har yau sallamar su ta ƙarshe da Abbanta na nan manne a zuciyarta kaman yau abun ya faru.

Ganinta na ƙarshe da Anti Ladidi an daɗe sosai. Tun wani zuwa da suka yi ita da Baba Zubairu Kaduna. Bata santa ba sosai amma duk haɗuwarsu matan ta yi mata kirki, tana da sakin fuska.

"A'a. Mutuwar farat ɗaya tazo."

Allah sarki Baba Zubairu. Yana chan yana jin yanda Umma ta ji da ta rasa Abba. Mutuwa irin haka babu ciwo tafi girgiza. Babu zato babu tsammani sai da ka ji an ce wane ya mutu.

"Allah Ya jiƙanta."

Rayuwar kenan. Wasu na zuwanta wasu na tafiya. Haka za a yi ta yi har ƙarshen duniya.

"Ameen," Umma ta amsa muryarta na sarƙewa.

Ko bata faɗa ba Maryam ta san mutuwar ta fama mata nata ciwon. Da bature ya ce 'time heals all wound' ƙarya ne. Lokaci ko kaɗan bai rage radaɗin rashin Abba a zuciyoyin su ba. Kullum da shi suke tashi da shi su ke kwanciya. Sha'anin duniya na iya kawar da zuciya daga tunani amma ba dai a manta gaba ɗaya ba.

"Ki kira shi ki yi mai gaisuwa."

"In sha Allah. Ki gaida su Mama."

Bayan sun yi sallama Maryam ta nemo lambar Baba Zubairu sai dai ta kasa kira. Wayyo Anti Ladidi. Ita kuma haka Allah Ya tsara mata. Bata bar yaran da za su riƙa yi mata addu'a ba. Allah sarki.

Ƙarfin gwiwar kira ta tattaro sannan da dannan kan lambarsa. Har ta kusan tsinkewa ya ɗauka. Da ka ji muryarsa ka san yana cikin tashin hankali. Bayan ta yi mai gaisuwa ta su ka yi sallama kasa motsawa. Bata san lokacin da hawaye su ka gangaro ba. Da sauri ta share su ta sauka daga kan gadon.

Ruwan wanka ta jona a heater bayan ta tabbatar ƙofar ɗakin rufe take. Ɗakin ta gyara kafin ruwan ya yi zafi. Bayan nan ta yi wanka sannan ta shirya. Tana rufe ƙofa wayarta ta yi ƙara cikin jaka. Zuby ce ke kira.

"Zuby ga ni nan fitowa."

"Ai ki yi zaman ki kawai babu aji, yanzu na kira class rep ya ke faɗa mun."

"Ah toh madallah, dama ba son zuwa na ke yi ba."

Ta yi sallama da Zuby ta koma ciki dama bata kai ga rufe ɗakin ba. Riga da sket ne a jikinta, ta cire su ta linke sannan ta sa doguwar rigar bacci. Sune kayan zaman hostel ɗinta.

Bashin bacci da ake binta ta biya. Ta sha bacci sosai buga ƙofar da aka riƙa yi ne ya tada ta. Waya ta dauko ta duba lokaci taga ɗaya har ta gota. Ko kiran sallah ma bata ji ba.

Ƙofa aka sake bugawa ta miƙe. Sumayya ce ƙawar Hamida. "Yi haƙuri na tayar da ke."

"Babu komai, lokacin sallah ma ya yi dole in tashi. Ina Hamida?"

"Ta tsaya siyan abu."

Sumayya ta shiga ciki Maryam kuma ta dau buta ta nufi bayi. Tana cikin sallah Hamida ta shigo. Bayan ta idar suka gaisa ta ke faɗa mata rasuwar da aka yi.

"Allah Ya jiƙanta da rahama."

"Ameen."

A nan Sumayya ta yini ranan su ka yi ta hira abun su. Kwadayi su ka riƙa ji Hamida ta ce su yi kallalaba. Dama suna da sauran kaya miya. Sumayya ta yi grating ta yanka albasa, Maryam ta kwaɓa, Hamida ta soya.

"Yajin nan ya haɗu." Inji Sumayya tana dangwala wainar a ciki. "Gaskiya a diban mun."

Hamida da Maryam su ka yi dariya. Sumayya ta gyara zamanta. "Ni ko Maryam tunda na ganki na ke ta ƙoƙarin tuna ina na san fuskar ki?"!

Maryam ta kalleta da mamaki. "Ni? Anya mun taɓa haɗuwa kuwa?"

Sumayya ta gyada kai. "Mun taɓa gaskiya, because your face looks familiar sosai. Bance komai ba dan na kasa tunawa."

Maryam ta ƙurawa Sumayya ido ko zata tuna idan ta taɓa ganin fuskarta. Kai ta girgiza. "Wata ƙila dai mai kama da ni kika taɓa gani."

"Toh, babu mamaki."

Daga nan su ka cigaba da hirar su. Aka dauko shafin primary school. Sumayya ke faɗa musu lokacin tana primary sune marasa ji. A Bauchi ta girma, har yanzu iyayenta na chan, makaranta ce ta kawo ta Zaria.

"Ah ni kuwa babu ruwana. Kin san wanda su ke zama a gaban aji ba su fiye hayaniya ba. Allah sarki, lokacin ni da babbar ƙawata Bilkisu Kabir. Ko ta wace duniyar yanzu?"

"Ya kike ce sunar ƙawar ki?" Sumayya ta tambaya tana karkata kai gefe.

"Bilkisu Kabir." Maryam ta maimaita.

"Na tuna!" Sumayya ta ce da ƙarfi tana tafawa. "Wallahi na tuna inda na gan ki. A Kano take ita Bilkisun ko?"

"Eh." Hamida ta amsa.

Sumayya ta yi murmushi. "Cousin ɗita ce Bilkisu ai. Babbanta ƙanin Mamana ne. Muna zuwa hutu gidansu  a Kano, a nan na taɓa ganinki."

Ta lissafo abunda zata iya tunawa kuma duka bata yi kuskure ba. Ikon Allah!

Sumayya ta yi dariya. "Na tuna na raka ta gidanku so ɗaya. Ba ki chanza ba sam Maryam."

"Har yanzu tana nan yar mitsila ko?" Hamida ta yi dariya.

Maryam ta harareta amma itama murmshi ta ke yi. "Wayyo Bilkisu. Dukan mu bamu riƙe zumunci ba." Lokacin da su ka rabu waya bata yawaita ba babu damar musanyar lamba. Gashi tunda su ka bar Kano ko hanyarta ba su sake bi. Amma bata taɓa mantawa da ita ba. "Ya take? Tana ina yanzu?"

"Tana BUK tana karantar medicine."

"Masha Allah!" Dama tun suna yara kullum maganarta idan ta zama likita, sai gashi Allah Ya nufa. "Ki bani numbarta in kirata."

"Toh. Amma bari in kira miki ita yanzu. Ina son in yi mata surprise."

Sumayya ta ɗauko wayarta ta nemo lambar Bilkisu. Bugu biyu ta dauka.

"Hello Summy." Muryar Bilkisu Kabir ta cika ɗakin.

Maryam ta yi murmushi. Bilkisun ce kuwa! Duk tsawon shekaran nun bata manta da muryarta ba.

Sumayya ta yi mata alama da ta yi shiru. "Na'am Billy. Ya makarantan?"

"Lafiya lau kin ganni yanzu na dawo lectures. Ya Zarian?"

"Lafiya lau. Billy albishirin ki."

"Goro fari tasss! Me ya faru yar uwa?"

"Gaskiya kafin in sanar da ke sai kin bani tukuici."

"An taɓa bada tukuici kyauta bata zo hannu ba?"

"Wannan kyautar ta musamman ce."

"Kin sa na ƙagu inji. Na yarda to, faɗi me kike so."

"Zan yi tunani a kai. Kin san wa na haɗu da ita a makaranta?"

"Ina zan sani Sumayya. Ni ki faɗa mun me ye albishirin."

"Shi ne albishirin ai."

"Na bada gari ki faɗa kawai."

Sumayya ta haɗa ido da Maryam. "Wata Maryam Ahmad na haɗu da ita ta ce mun ta san ki."

"Me kika ce?" Bilkisu ta ce da ƙarfi. "Maryam Ahmad! Na santa wallahi na santa. Ƙawata ce tun nursery. Bayan Abbanta ya rasu su ka bar Kano ban sake ganinta ba. Allah sarki ʼyar mitsila. Ta ya kuka haɗu? Kin karban mun number ɗinta dai ko."

Sumayya ta miƙawa Maryam wayar. "Bilkisu Kabir." Ta kira sunanta tana dariya.

"Inna lillahi! Maryam Ahmad! Ke ce! Ya Allah! Ashe rai kan ga rai! Maryam!"

"Na'am Bilkisu."

"Wayyo Allah na! Ya kike? Ya Umma? Ina Safiya da Zee da Idi da Bashir?"

"Suna nan lafiya. Suna Kaduna. Ya su Umma da Abba, da sauran ʼyan gidan?"

"Kowa na nan lafiya. Wallahi kaman in rufe ido in ganni a Zaria. Maryam Ahmad! Kin ƙara girma dai ko."

Maryam ta fashe da dariya. "Ban sani ba."

Bilkisu ma ta yi dariya. "Wallahi abun kaman a mafarki. Dole in kira Ummana."

Sun dade a waya suna gaisawa sai da Sumayya ta kwace wayarta kar su ƙaran mata da kati.

"Dan Allah Summy turo mun number dinta yanzu-yanzu."

"Bari ma zan kira ki." Maryam ta ce.

Daga nan su ka yi sallama. Har yanzu Maryam bata daina mamakin abunda ya faru ba. Tana yawan tunawa da tilon ƙawarta a lokacin amma bata ta yi zaton za su sake haɗuwa ta haka ba. Lambar ta amsa wurin Sumayya ta yi saving sannan ta kira.

"Hello Bilkisu, ni ce."

"Toh Maryam bari in yi saving yanzu. Sai mun sake waya."

Sanadin farfaɗowar ƙawancen da aka kulla shi tun yarinta kenan. Maryam da Bilkisu suna waya idan an kwana biyu. Sun sake sabawa kaman shekarun da suka dauka ba su yi magana ba su faru ba.





Sorry it's coming late🙏🏽❤️

~Maymunatu Bukar💕

Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro