1.
KANO.
MARIS, 2002.
"Maryam ki yi sauri ki kawo mun kayan miyan mana sai na makara. Ke fa tsiyata da ke kenan."
"Yi haƙuri Umma," Maryam ta ce daga bakin famfo inda ta ke ƙoƙarin gama gyaran kayan miya. Da sauri ta zuba su cikin roba ta yi hanyar kicin in da Umma ke jiran ta.
Umma na tsaye gaban cooker tana soya kaji. "Yi sauri ki markaɗa kafin a ɗauke wuta."
Kujerar tsugunno ta janyo ta taka ta ɗauko kofin blender da tushen da ke saman slab. Bayan ta juye kayan miyan ta kunna socket ɗin ta yi musu niƙa ɗaya.
"Umma na gama."
"Ajiye su a nan. Kin ɓare tafarnuwan?"
"Eh, gata chan har na daka."
Umma ta yi mata murmushi. "A gaishe ki."
"Babu wani abu da zan yi miki?"
"A'a, babu je ki abun ki."
Maryam ta koma gefen Umma tana ƙoƙarin leƙa tukunyar. Kai ta ɗaga ta kalli mahaifiyarta. "Umma dan Allah ki bari in haɗa kajin."
"A'a Maryam," Umma ta girgiza kai. "Kin ga babanku zai dawo yau, ki bari dai wata rana."
"Allah Umma na iya, babu wahala. Na ga yanda kike yi. A soya kayan miyan su soyu sosai a sa kayan ɗanɗano sai a zuba kazar da aka soya a ciki a juya har sai sauce ɗin ya kama jikinta."
Umma ta yi dariya tana kaɗa kai. "Tabbas kin iya."
Murmushi Maryam ta yi tana jin daɗi. "To za ki bari in yi?"
"Idan ban bari kin yi ba ai yau na bani da mita. Ɗauko kayan haɗin ki fara ɓarewa kafin nan shinkafar ta yi, sai a haɗa kazar."
Da sauri ta ɗauko robar da ke ɗauke da kayan ɗandanon girki, Umma ta ɗiban mata yanda zai isa gudun kar ta je ta cika gishiri ya yi yawa.
Maryam ta haɗa naman da taimakon Umma, tana ta jin daɗi. Bayan sun gama da gudu ta nufi ɗakin su ta faɗawa 'yar uwarta abunda ya faru. Tana shiga ta iske Idris ya haye kan Zainab suna dambe, Safiya kuma na gefe rungume da Bashir tana kallon su.
"Kai ku bari mana," ta ce tana ƙoƙarin raba su. Bata san ƙafar waye ba sai ji ta yi an mangareta har ta faɗi.
Safiya ta kyalkyale da dariya. "Ke ma wa ya ce ki raba su. Ki bar su wanda ya ji zafi zai bari."
"Wallahi sai na faɗawa Abba in ya dawo," Zainab ta ce tana kuka tana ƙoƙarin sake chakumo wuyar Idris. Ƙarfin namiji da mace ba ɗaya ba, ya fizge ya nufi ƙofa Zee na bin shi tana ce wa wallahi sai ta rama.
Kafin Idris ya fita Umma ta shigo. Ta bisu da kallo yanda ɗakin ya yi kacha kacha kaman filin yaƙi. "Kai! Kai! Kai!"
"Umma wallahi Zee da Idi ne." Safiya ta yi saurin cewa. "Tun ɗazu su ke dambe sun ƙi su dena kin ga har bige Ya Maryam su ka yi."
Umma ta kalli Maryam da ke riƙe da goshi sannan ta maida kallonta kan Zee da ke kuka da Idris da ke ta faman haki. "Abban ku na dawowa zan faɗa mai. Duk wanda ya yi dambe bai da tsaraba. Maza ku gyara ɗakin, ku wuce ku chanza kaya. Yara za su haukata ka...." ta tafi tana mita.
"Abba ya kawo mana alawa da minti wasu sai dai kallo," in ji Safiya tanawa ƙaramin su Bashir wasa.
Zee ta ƙara zumɓuro baki. "Sai mun sha. Ko Idi?"
"Eh mana!"
Maryam ta girgiza kai. Kaman ba su suka gama faɗa yanzu ba. Tashi ta yi ta taimaka aka gyara ɗakin. Horn ɗin da su ka jiyo ya sa kowa ya bar abunda ya ke su ka fita da gudu ana ihu. "Abba! Abba! Abba!"
Suna tsalle har motar ta tsaya Abba ya fito. Da gudu suka nufe shi inda ya durƙusa yana jiran su. Duka ya sa hannun ya rungume su yana ta murmushi.
Bashir ya ɗaga sama yana sauraron su duk da baya fahimtar abunda su ke cewa, ɗan duka magana su ke yi lokaci ɗaya Maryam ce kawai ta yi shiru tana murmushi.
"Yaya Maryam, wannan ƙannen naki za su fasa mun kunne." Ruƙo hannun su ya yi ya ce to a shiga ciki sai kowa ya yi mai bayani.
Umma na falo tana jin hayaniyar su. Ta chanza kaya ta shirya cikin shadda da ta haskaka baƙar fatar ta sai baza kamshi ta ke yi tana jiran shigowar mijinta.
Arc. Ahmad ya shigo tare da yaran da wannan murmushi da ake samu ko yaushe a fuskar shi musamman idan yana tare da iyalinsa. Murmushin da ke fuskarsa ya faɗaɗa da ya yi tozali da matarsa sanyin idanunsa kuma uwar 'ya'yan shi.
A gefenta ya zauna, yaran suka haye mai cinya. Su Zee da Idi sarakan rashin ji. Maryam kuwa tana maƙale a gefen shi ita da Safiya.
"To, a bari Abba ya huta ko? Ku tafi ɗaki, kuma na ji wasu sun yi faɗa ni da su ne."
Duka suka rankaya su ka tafi. Maryam har ta kai ƙofa ta dawo. "Abba sannu da zuwa, ya hanya?"
Hannu ya ɗaura kanta ya shafa. "Lafiya lau Yaya Maryam. Kuna lafiya?"
"Lafiya lau. Allah huta gajiya." Da gudu itama ta bi bayan 'yan uwanta.
Abba ya dauke ido daga kan ƙofar ya maida kan Umma. "Sannu Sa'adah, Allah Ya yi miki albarka. Kin ji kaina har yana nema ya fara ciwo."
Umma ta yi dariya. "An dawo lafiya? Ya hanya?"
"Lafiya lau tunda na dawo na same ku cikin ƙoshin lafiya. Hanya kam mun sha ta, titi kaman ba zai ƙare ba."
"Ka shiga ka yi wanka sai ka ji ɗaɗin jikin ka."
Abba ya mike yana naɗe hannun riga. "Ko zamu je ki yi mun gashi ne?"
Da sauri Umma ta rufe fuskarta da tafin hannuwanta. Abba ya yi dariya ya wuce ciki.
Arc. Ahmad da Sa'adatu sun yi aure tun ƙuruciya. Farkon ganinta ya san tabbas ya haɗu da uwar 'ya'yan shi. Yanzu shekaru sun ja Allah Ya azurta su da yara har biyar. Maryam mai shekaru sha biyu sai Safiya, Idris, Zainab da ɗan auta Bashir. Duka shekaru biyu ne tsakanin su.
Bayan Abba ya shiga ɗaki Umma ta mike da niyar zuwa kicin ta kawo mai abinci. Sai dai bata matsa ba Maryam ta yi sallama ɗauke da tray.
"A gaishe ki Yaya Maryam," Umma ta kirata da sunan da mahaifinta ke tsokanarta da shi. "Ina Safiya?" Wannan kam son jikinta ya yi mata yawa.
"Tana ɗaki," Maryam ta amsa. A gefe ta ajiye tray din, ta ɗauko ledar da ake shimfiɗawa a ci abinci ta shimfida sannan ta ɗauko tray ɗin da ajiye a kai. Fridge ta bude ta ɗauko kunun ayan da ta taya Umma shima ta ajiye. Komai ta jera shi tsab.
"Allah Ya yi miki albarka Maryama."
"Ameen Umma." Ta amsa sannan ta fice.
Abba ya fito sanye da farar jallabiya ya tsaya gefen Umma. Sai da ta ɗaga kai ta kalle shi tsabar banbancin tsayin su. "Mu je ka ci abinci."
Ita ta zuba mai abincin ta miƙa mai. Ya tambaye ta in ta ci ta ce mai a'a. "To matso in baki."
Ahmad kenan, Umma ta ce a zuciya. Ba a raba shi da zolaya. A wasu lokutan tana ji kaman tafi ko wace mace sa'a a duniya da ta same shi a matsayin abokin rayuwa. Mutum ne mai nagartattun halaye, daidai da sau ɗaya bai taɓa tauye mata hakƙinta ba. Sannan uwa uba gashi mahaifi na gari, jajirtacce wurin ganin yaran shi sun samu dukkan abunda su ke buƙata, daga karatu, tarbiya da kayan alatu na zamani. Babu ta inda ya rage su da komai.
Yatsa da ta gani gab da idonta ya sa ta ƙiftawa, ta dawo daga duniyar tunanin da ta tafi. Cokali ne gab da bakinta. Kai ta girgiza ta buɗe bakin ya saka mata. Haka ya gama ciyar da ita kafin ya zuba na shi abincin.
Bayan ya gama cin abinci ta tsiyaya kunun aya a kofi ta miƙa mai. Ya sha ya yi hamdala. "Abinci ya yi dadi, musamman kazar."
"'Yar ka ta hada."
"Wa? Safiya?" Abba ya yi dariya ganin kallon da Umma ta yi mai. "Allah Ya yi mata albarka. Maryam ai akwai kokari."
Umma ta labarta mai yanda su ka yi dazu da kuma abubuwan da suka faru da baya nan. Shima yanda tafiyar ta shi ta kasance ya labarta mata. Dama kwangila ya je nema a Maiduguri kuma cikin rahamar Allah an dace.
"Yanzu saura mu fara aiki." Ya ƙara zuba kunun ayan.
"Masha Allah. Allah Ya taimaka."
"Ameen, ameen." Jaka ya janyo daga gefe ya dawo da ita gaban shi. "Kinga kira mun yaran nan."
Umma ta mike ta kira su. Sun ma riga ta isowa falon. Idris ne a gaba. A tsakiya suka saka shi su ka zagaye. Ya ciro tsarabar kowa ya miƙa mai.
A tare su ka ce, "Abba mun gode. Allah Ya kara budi."
Addu'ar da a kullum yaran su ka yi ya ke saka shi farin ciki mara misaltuwa. "Ameen 'yan gidan Abba. Zo ku faɗa mun da mai da mai ya faru da bana nan."
Nan aka buɗe sabon babi, kowa na ƙoƙarin bada na shi labarin.
Umma ta zauna a gefe tana kallon su. Mutumin da ya ce a gajiye ya ke shine ya ke nema a bashi labari.
***
Yara sun taso daga makaranta gefen titi a cike kowa da group ɗin su ana tafiya ana raha. Maryam na goye da jakarta ita da ƙawarta Bilkisu Kabir. Ƙawarta ce tun nursery har zuwa yanzu. Suna tafiya suna hira.
"Ni ko maths ɗin yau da a ka yi ban gane shi ba." Inji Bilkisu.
"Ai kuwa babu wahala. Gobe lokacin break sai in nuna miki in kina so."
"Ina so mana. Ke kuwa Maryam Ahmad kin ji daɗi, da anyi abu kike ganewa."
Maryam ta yi dariya. Ita idan ana karatu ko kallon gefe bata yi duka hankalinta ta ke mayarwa kan malamin a haka ta ke gane komai. In kuwa bata gane ba ta riƙa tambayan malamin kenan har sai ta fahimta. Malaman makaranta har sun santa.
Daidai isowarta gida daidai fitan ƙanin Abbanta Baba Musa. Tana ganin shi ta ruga ciki a guje ko gaishe shi bata yi ba. Ai kuwa ta samu Ummanta na kuka a tsakar gida. Jakarta ta yarda ta tsugunna kusa da mahaifiyarta. "Umma me ya miki?"
"Babu komai," Umma ta ce tana ƙoƙarin share hawayenta. Bata so Maryam ta dawo ta isketa haka ba.
"Umma ki faɗawa Ab..."
Tsawar da Umma ta daka mata ta katse ta. "Kar ki sake ki faɗa mai. Idan kika faɗa zan gamu da ke. Tashi ki je ki chanza kaya ga abincin ki chan."
Jiki a sanyaye Maryam ta ɗauki jakarta. Ƙaran TV da ta ji yasa ta leƙa falon inda ta samu ƙannenta na kallo an ƙure ƙaran yanda ba za su ji komai da ke faruwa a waje ba. Kai ta girgiza ta tafi daƙin su da ake kira da ɗakin 'yan mata. Ita da Safiya da Zee su ke kwana kowa da gadon shi.
Tunanin abunda ke kawo Baba Musa gidan ta ke yi. Ba yau hakan ya taɓa faruwa ba kuma baya zuwa sai Abban su baya nan. Ranan da ta fara gani ta zo faɗawa Abba Umma ta make ta har ta ji ciwo, tun lokacin bata ƙara yunƙurin faɗi ba. Ko ma meye tana addu'a Allah Ya sa Abban ta ya sani. Dan idan ya sani sai ya gamu da Baba Musa da ya saka Umma kuka.
Wardrobe ta bude ta ɗauko kaya. Gefenta gyare ya ke tsab, na Zee da Safiya kuwa kayan a chakude su ke. Riga da wando ta ɗauko ta saka sai ta ƙara fitowa a 'yar karamar ta. Maryam ba dai ƙanƙanta ba. Abbanta ma 'yar mitsila ya ke ce mata. Duk ƙannenta sun fi ta girma.
A maimakon ta je ta zuba abinci ɗakin Umma ta tafi. Gidan su ba babba bane amma ba za a kira shi da ƙarami ba. Dakuna huɗu ne sai falo daya da kicin da kuma madaidaicin tsakar gida.
Umma na zaune kan gado ta yi tagumi tana tunanin kalaman Musa. Ya fara bata tsoro. Tana ganin Maryam ta ƙaƙalo murmushi. Yanzu zata zo ta cikata da tambayoyi.
"Umma..." Maryam ta kira a hankali. Gefenta ta zauna ta ɗaura kanta a kafaɗar Umma sannan ta rungumeta.
Umma ta saki ajiyar zuciya. Ina ma zata iya da ta yi kuka ko sauran ɗacin da ke ranta ya fita. Ta tsinci kanta cikin tsaka mai wuya bata san inda zata saka kanta ta ji sanyi ba. Wanda ya kasance shi ke magance mata duk wata matsala ba zata iya tunkarar shi da zancen ba kai tsaye ba.
"Kin ci abinci Maryam?" Kai ta girgiza. "Tashi mu je to, nima ban ci ba." Tasan idan ba haka ta yi mata ba zata sa damuwa a ranta.
Gaba ɗaya ranan idon Maryam na kan Umma. Da Abba ya dawo kaman ta faɗa mai amma tuna abunda Umma ta yi mata wancan karan ya hanata. Tana ji Abba na tambayan Umma me ya same ta ta ce mai kanta ne ke ciwo.
Idan sun yi ƙarya Umma faɗa ta ke musu wani lokaci har dungurin su ta ke yi amma gashi ita tana yi wa Abba ƙarya.
"Ku fa malaman asibiti kun fi kowa ƙin son shan magani. Safiya dauko akwatin magani da ke ɗaki na. Haba Nurse Sa'adah, a ce kan ki na ciwo kuma ba ki sha maganina ba. Uhm? Sanadin wani abu ya same ki."
Safiya ta kawo mai ya ciro paracetamol ya ɓallo guda biyu ya miƙa mata. Umma ta karɓa ta sha ba dan taso ba dan kawai ta kawar da tunanin shi daga son sanin abunda ke damunta.
Abba ya ce Umma ta je ta kwanta shi zai shirya yaran su tafi islamiya. A mota ma ya kaisu. Da ya dawo ya samu Umma na shara. Dama ya san bazata kwanta ba.
Bakin gado ya zauna ya zaro kwali daga cikin drawer. "Bar sharan nan, zo ki zauna."
"Ɗaikin ya yi datti."
"Ke dauɗa ko a ina take ai hango ta kike yi. Ni banga wani datti da ya yi ba. Taho ki zauna," ya miƙa mata hannu. Gab da shi ya zaunar da ita ya miƙa mata kwalin.
A hankali ta bude ta ciro kwali ƙarami da kuma wani abu na plastic yellow da bata san menene ba. An dai rubuta 'pay as you go', 'MTN your best connection'. Sake karantawa ta yi ta ga 'starter pack' da 'Nigeria' rubuce kan jan layi.
Ta ɗago ido ta kalle shi. "Baban Maryam menene wannan?"
"Wannan shi ake kira SIM card."
"SIM card," ta maimaita. Ƙaramin kwalin ta ɗauko. Hoton wani abu ne a kai. Ta buɗe ta fito da shi tana juyawa.
Abba ya karɓa. "Wannan kuma wayar salula ce. Nokia 3310 sunanta. Da wannan zan iya kiran ki a ko da yaushe mu gaisa, nima tawa na cikin jaka. Kin ganta ƙarama kuma zata shige cikin jakar ki."
Umma ta karɓi abun al'ajabin ta juyata a hannunta. Kallon landline ɗin da ke ajiye kan tebur ta yi. "Yanzu wannan ƙaramin ze yi abunda wancan ke yi?"
Abba ya yi dariya. "Baturen kenan." Bayanin yanda abun ke aiki ya yi mata Umma na ta gyada kai tana sauraron abun al'ajabi.
Bayan ya saka shi SIM card ɗin a ciki ya kunna salular sai gashi ta yi haske hannaye biyu su ka fito.
"Sai ka ce vidiyo." Umma ta ce tana dariya. "Amma wannan ta fi dubu ashirin ko?" Ganin Abba ya yi shiru ta kalle shi. "Tafi haka?" Ta ce a tsorace.
"Ke dai ina ruwan ki."
"Baban Maryam...." ta kira shi. "Nawa?"
Abba ya sosa kai. "Babu tsada. Wayar dubu hamsin, SIM ɗin kuma talatin."
Umma ta dafa ƙirji tana zaro idanu. "Dubu tamanin kenan fa. Haba Baban Maryam, da wani abun ka yi da su."
Kwalin ya ture daga kan cinyarta ya janyota jikinsa. "Sa'adah idan ban miki ba wa zan yi wa? Duk faɗi tashi da na ke yi dan ke da yarana na ke yi sai mahaifiyata. Ko nawa ne zan iya kashewa a kan ki."
Tuni hawaye su ka taru a idanun Umma. Abba ya sake janyota jikinsa ya rarrasheta da salo mai ratsa jiki da zyciya.
•
•
•
•
Salamu alaikum!
Barkan mu da dawowa🤭 ban taɓa zaton zan fara rubuta sabon littafi da wuri haka ba.
Da fatan 'Lokaci ne' zai samu karɓuwa kaman yanda 'Rayuwar Maimoon' ya samu, ko fiye da haka.
I have so many things planned for this book. Ku tayani addu'a Allah Ya bani iko.
To ya babi na ɗaya? I want your honest reviews.
~Maymunatu Bukar💕
Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro