Chapter 26
"Cikin tashin hankali su dad suka karasa gida zuciyarsa cike da tuhumar shin meyasa ake tuhumar aneesa da lefin kisan kai?bayan motansu yayi parking ne suka fita gaba dayansu bayan mum ta nunawa khushi bangaren da zata ajiye travelling bag dinta,cike da mamaki ta shiga dakin sedai har yanzu ta kasa tuna komai a cikin wannan gidan,tana shiga palour din dad ya kalli mum da sauri yace wai kina jin me mutanen nan suke cewa kuwa?ajiyar zuciya mum tayi tace suwa kenan alhaji?cikin fushi ya kalleta yace ohh tambaya ta ma kikeyi kenan kina kallo fa yan sanda suka tafi da aneesa a gabanki saboda mahaukatane sun saba shaye shaye zasuce wai suna zarginta da kisan kai,itama mum ajiyar zuciya tayi tace toh yanzu dai sai abi komai a hankali a gano gaskiyar zance saboda ita hukuma dai ba,a fada da ita kuma sun san me sukeyi,kallonta ya sakeyi a fusace yace kenan kina nufin kin yarda da abinda suka fada kenan saboda kin saba shashanci wlh banda a gabana kika haifi aneesa da sai ince ba kece uwartaba saboda yanda kike nuna mata tsana,murmushi mum tayi tace ashe kana tsoron wannan ranar har kayi sake tazo ta sameka ko ka manta lokacin danake fada maka cewar ina zargin samun aneesa da bindiga amma ka nuna min sam ni banida hankali sai yanzu kuma zaka nuna damuwarka akai?hannu yasa ya dakatar da ita cikin fushi yace koma meye dai kinsan inada tarin kudi da dukiya ko,toh zakiga aikin kudi koda zan zama banida komai a kasar nan zanyi amfani da kudina don ganin aneesa ta fita daga hannunsu,yana gama fadar haka ya fita ransa a bace ya shiga mota ya wuce police station din da aka kai aneesa.......alhaji na fita mum ta nufi dakin khushi sedai kwance ta tarar da ita tana bacci dama yawanci babu abinda takeyi sai bacci tunda tayi loosing memory dinta,dad be wuce 3 hours ba ya dawo tare da aneesa cikin farin ciki yace wuce dakinki kije ki huta,turo baki tayi cikin fushi tace dad wai meyasa bakazo da wuriba har seda kasa na fara gajiya,cikin sakin fuska yace I'm sorry princess akwai dalilin da yasa haka amma yanzu komai ya wuce take rest please,turo baki tayi alamar bata yarda da maganar da dad ya fada mataba ta wuce apartment dinta,wanka tayi bayan ta fito tayi sallah ta fito dinning area,bata tarar da komai akan dinning table dinba tsaki tayi ta nufi kitchen da kanta ta bude fridge yoghurt ta gani da cookies kawai tsaki tayi ta dauka ta dawo palour ta zauna ta faraci,bata wani ci dayawaba saboda sam bata fiye son yoghurt ba,shiru tayi kamar me tunanin wani abu ta mike tsaye da sauri ta nufi bangarensu khushi,jikinta sanyaye ta tura kofar dakin ta shiga still barci ta tarar tanayi,tsugunawa tayi a gefen gadon ta zuba mata ido kamar bata taba ganintaba har saida tayi spending kusan 10 minutes tana kallon khushi har batason kifta idonta daga kanta,hannu tasa ta cire gashin daya rufe fuskar khushi,jin motsi yasa khushi saurin bude idonta cikin rashin fahimta taci gaba da kallon anee kamar ranar ta fara ganinta sannan ta mike ta zauna cikin murmushi kadan tace sannu,shiru anee tayi kamar batason amsa maganar da khushi tayi mata fuskarta cike da damuwa tace khushi.....kamar wata doluwa haka khushi taci gaba da kallon aneesa cikin sanyin murya aneesa tace can't you remember me upto now?cikin rashin fahimta khushi tace yes i cant remember you but meyasa kike kirana da khushi?iya sanina khushi is not a name amma meyasa dukanku kuke kirana da wannan sunan?ajiyar zuciya anee tayi sannan ta gyara zamanta bayan ta janyo hannunta tace khushi don Allah ki saurareni ya kamata ace yanzu kinsan wacece ni wajenki,kallonta taci gaba dayi cike da tuhuma tace wacece ke?and who are you to me?shiru anee tayi har na tsawon 2 minutes sannan ta sakeyin ajiyar zuciya tace i am your love khushi,cikin mamaki khushi tace how?ran aneesa ne ya baci ta mike ranta a bace bayan tayi tsaki tace dama bazaki gane komaiba yanzu sam bakyasona banga amfanin zama nayi miki bayanin koni wacece ba saboda ko kin tunani ba wani abu zakiyi akaiba,tana karasa fadar haka ta nufi hanyar fita a fusace ta fice daga dakin bayan ta rufe kofar dakin da karfin gaske,saurin toshe kunnenta tayi jin yanda karar rufe dakin yayi affecting kunnenta yasa ta dora hannunta a kunnenta kanta yaci gaba da juyawa wasu irin memories suna dawo mata kanta,wani irin ihu taci gaba dayi kamar mahaukaciya bayan an jiyota ne su mum suka taru akanta aka kira doctor ya dubata,murmushi yayi ya kalli mum yake fada mata cewar yanzu meenal ta dawo dai-dai tana iya gane duk abubuwan da ta mantasu zata iya cigaba da ganesu a hankali,sosai mum ta nuna farin cikinta kamar zatayi kuka saboda farin ciki shima dad haka dama tunaninsu taya zasu fadawa su abba cewar khushi tayi loosing memory dinta bayan sun sanar dasu cewar kawai sunje USA yin siyayya ne....bangarensu abba sosai sukeyin shirye shiryen bikin meenal amma abinda yake basu mamaki shine jin sam basa samun wayar meenal din sedai idan sun kirasu dad suce musu tana lafiya,bangaren najeeb shima ya rasa gane kan alamarin khushi da aneesa ganin meyasa zaa saki aneesa bayan ga abinda ta aikata?sannan meyasa yanzu meenal bata damu da rayuwarsa ba?kenan maganar da ake fada masa akan meenal gaskiyane cewar aneesa tayi alwashin babu namijin daya isa ya auri khushi idan har tana raye,tsaki yayi shi kam sam lamarin khushi ya fice mishi aransa duk irin soyayyar da yakeyi mata amma sam bata damu dashiba ko kadan....
"Bayan an tabbatar da warkewar khushi hakan yayi dai-dai da saura kwana 6 bikinta,mum ta umarci khushi data hada kayanta ta koma gidan hajja yagana yar sudan wacce takeyin gyaran jikin amare,itama bangaren khushi taji dadin haka saboda sam bata kaunar su dinga hada hanya da aneesa saboda indai tana ganinta zata dinga sanja mata tsarin rayuwarta(Lol mutane dayawa suna min dariya wai ban iya pronouncing sanjawa ba hahah mu a garinmu idan kikace chanjawa dariya zaa miki i swear)sosai hajja yagana take cigaba da gyara khushi da zafafan products dinta na gyaran jiki tayi kyau sosai kaman a saceta,anee ta shiga cikin tsananin damuwa saboda ko wayarta khushi ta dena dauka idan tayi pinging dinta a whatsapp sam bata kulata hakan yasa aneesa ramewa cikin 4 days duk ta fice a hayyacinta,ta wani bangaren hankalin khushi ya fara kwanciya kadan ganin yanda cikin kwana 4 suka fahimci junansu da najeeb inda taci burin yi masa biyayya bayan sunyi aure,ba wani events dayawa aka shiryawa bikin nasu ba saboda khushi ba mace bace me son hayaniya sosai....kamu,henna day sai daurin aure kawai za,ayi.....ana gobe zaa fara events din khushi ta dawo gidansu,a gajiye ta shiga tayi wanka bayan ta fitone ta tarar da mum zaune tare da baqi sun fara zuwa especially wanda suke nesa da state dinsu,tsugunnawa tayi ta gaishesu cikin ladabi bayan sun gaisane mum tace yawwa meenal dama jiran fitowarki nakeyi jeki kitchen ki hadamin kunun gyada duk dake amaryace ance baa saku aiki amma nidai yau sena saki saboda nafi jindadin naki,murmushi khushi tayi cikin jin kunya tace toh mum,direct kitchen din ta wuce don shiryawa mum kunun gyada din,jin kamar motsin mutum bayanta ya sata juyowa da sauri a tsorace,hada ido sukayi da anee wannan karon kalar kallon da aneesa keyi mata ya banbanta da kalar kowanne kallo da takeyi mata fuskarta babu alamar wasa tace i wanna talk to you
Thank you for reading my story!!!
See you tomorrow
Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro