Chapter 18
"Cikin tsoro ta bude idonta ta fara dube-dube sai a lokacin ta gane cewar mafarki takeyi,ajiyar zuciya tayi tace Alhamdulillah sannan ta mike ta nufi bathroom jikinta a sanyaye,bata dadeba ta fito daga wankan ta tsaya jikin mirror bayan ta shafa lotion tasa powder kadan sai lipstick,night gown tasa sky blue bayan ta feshe jikinta da perfume ta dauki wayarta ta nufi dinning,zaune ta tarar da mum da khushi wannan karon harda dad shima,kusa da dad ta zauna cikin tsokana tace hey dad,dafa bayanta yayi kadan yace hey beti....shiru tayi taci gaba da wasa da wayarta,mikewa khushi tayi ta janyo food flask din dake jere ta zuba mata masar dankali hade da egusi soup din da yaji catfish da sausage,sosai anee ke jin dadin abincin don ta dade bataci abinci dayawa bama kamar yauba,shirune ya ratsa kafin mum ta kalli dad tace alhaji dama yanzu meenal ke rokon alfarmar tanaso gobe idan Allah ya kaimu taje gidansu tayi ko sati dayane tunda kaga makarantar tasu ma sun tafi strike,kenan kaga zata samu damar zuwa gidan iyayen najeeb tayi musu jaje,gaban aneesa ne ya fadi wanda har ta gagara controlling kanta sai data kalli mum da sauri sannan ta kalli dad don jin amsar da zai bawa mum din,shiru yayi kadan yace of course hakan ma is a nice idea toh shikenan babu damuwa gobe insha Allah sai ta shirya din taje,murmushi khushi tayi tace thank you dad nagode Allah ya saka da alkhairi,kallonta yayi yace babu komai sannan ya kalli aneesa dake faman scrolling pictures din dake wayarta ba tare da tasan abinda take dubawarba yace yawwa aneesa daga nan zuwa safiya kiyi kokari ki yiwa meenal booking din ticket,okay dad tace sannan ta mike ta koma apartment dinta gudun kar a gane halin da take ciki,tana shiga daki ta zauna gefen gado ta dora hannunta akanta tace ya Allah wannan wacce irin rayuwace?wannan wacce irin kaddarace haka take faruwa dani?fashewa tai da kuka cikin tausayi take fadin i don't want to loose her ya zama dole nayi duk abinda zan iya saboda na raba khushi da kowa,cikin farin ciki khushi ke shirye shiryen kayanta saboda ita kanta cikin kwana biyun nan da akayi kidnapping din najeeb sam ba dadin duniyar take jiba,tuni ta shirya komai cikin travelling bag dinta....karfe 8 aneesa ta fito sanye cikin abaya peach colour wanda yayi mata kyau sosai batayi wani heavy makeup ba saboda ita batason duk abinda zai takura mata by the way makeup is not her favorite,tana shirin jan kujera ta zauna mum ta fito itama cikin bubu na lace red colour tace yawwa aneesa dakinki zanje yanzu dafatan kinyiwa khushi booking din ticket saboda banaso tayi tafiyar dare,kallonta tayi fuskarta babu alamar dariya tace yes mum nayi booking tun jiya da daddare flight din 11am zata bi amma fa mum tare na siya mana tickets din saboda nima inason zuwa,gaban khushi ne ya fadi cup din tea dake hannunta taji yana shirin faduwa ta sake rikeshi gam a zuciyarta tace ya Allah anee ki barni na huta haka na gaji da wannan rayuwar da muke ciki,amma a zahiri murmushi tai jin anee tace tare zasu tafi,shirun da mum tayi yasa anee sake tabe baki tace mum bakice komaiba,ni dai baruwana ki bari alhaji ya fito seki fada masa kunfi kusa mum ta fada cikin tsokana,bata karasa maganaba dad ya karasa hannunsa rike da news paper yace menene naji ana kiran sunana?cikin shagwaba tace dad wai don kawai don nace zan bi meenal muje gidansu shine mum tace wai ita ba ruwanta in tambayeka da kaina,dariya yayi yace toh ke banda abinki idan zaki gidansu har se kin tambayeni ai duk matsayinku dayane sannan itama kinga ai a wajenmu take zaune saboda haka kema ya kamata ki dinga zuwa gidansu,tsalle tayi tace yes that's my dad shiyasa nake sonka,a tare suka zauna bayan sun karasa cin abincin dad ya dauko 200k ya bawa khushi ta karba tana godiya,aneesa ta shiga ta hada kayanta itama ta fito duk daba wasu kaya dayawa ta diba ba tafi ganewa idan taje ta siya kaya achan,karfe 10:40am suka karasa airport din,bayan jirgi ya fara tafiyane wani kyakkyawan saurayi wanda ya zauna a gefen khushi ya kalleta fuskarsa cike da murmushi yace hey nice to meet you,itama murmushin tayi ba tare da tace mishi komaiba,sake fuskantarta yayi yace i,m khalid by name what about you?ba tare data kalleshi ba tace meenal,murmushi yayi yace wow nice name can we be freinds please?a fusace anee ta juyo cike da masifa tace how dare you?are you out of your sense?kai wanne irin mayen mutum ne tun dazu ka cikamin kunne da surutu meye hakane wai?cikin mamaki yake kallon aneesa ganin yanda ta dage sai masifa takeyi kamar ita yayiwa magana,shima cikin masifa yace hey look gold digger kawai ba dake nakeyin magana ba balle kice an takura miki, a zafafe ta sake cewa baza ayi shirun ba irin yan iskan mutanen nan neku marasa mutunci toh wlh idan ka sake mata magana sai nayi maka abinda zaka dade kana mamaki,dariya yayi saboda yanda yaga ta dage tana ta masifa duk da yanason hard people's kamar anee amma sam bata birgeshiba ganin yanda take ta masifa ba wani manners,be sake ce mata komaiba illa kallon khushi da yayi yace hey beautiful I'm talking to you,kafin khushi ta sake cewa komai tuni anee ta riko wuyan rigarsa ta mareshi hakan ya jawo hankalin mutanen dake kusa dasu cikin mamaki suke janye hannun anee daga rigar khalid,cikin fushi khushi ta kalli anee tace what are you doing anee?meye kikeyi haka?murmushi Khalid yayi ya kalli mutanen dake bashi hakuri yace karku damu aneesa ce yar gidan tsohon minister petroleum,dama an dade ana labarinsu kasan yan lesbian ne akan nace inason kawartata shine har ta mareni,cikin mamaki kowa ya rike baki sannan suka kallesu sukace Allah ya shiryeku la,anannun Allah duk iskancinku dai baku isa kun auri junankuba sai dai ku qare a haka,tuni gumi ya fara wankewa khushi fuska kenan duk duniya ma ansan halin da suke ciki?ganin anee ta dage sai zazzaga masifa take tana mayarwa duk wayanda sukace musu yan lesbian ya sata riko hannunta suka zauna tace easy anee kiyi shiru idan munje gida se muyi maganar
"Babban driver dad din aneesa ne ya karasa dasu har kofar gidansu meenal,cikin farin ciki da zumudi umman khushi ke kawo musu abinci da duk wani abin sha wanda be wuce karfin arzikinsu ba,tunda suka isa gidan khushi bata cewa anee komaiba illa nazarin hukuncin da zata yanke,kallon khushi tayi fuskarta babu alamar wasa tace idan har saboda nayi fada akankine kike fushi toh lallai daga yau kin fara fushi har karshen rayuwarki saboda banga wanda ya isa yayi rayuwa dakeba idan bani ba,amma anee wannan abinda kikeyi ba abune mai kyauba kuma baya dacewa meyasa zaki dinga tona mana asiri in public it's an embarrassment kina bata mana suna a duniya ne nidai gaskiya banaso ta karasa maganar cikin fushi ba tare data kalletaba,ganin yanda ran khushi ya baci yasa anee dago fuskarta muryarta sanyaye tace i,m sorry khushi ni kaina wani abin bana sanin sanda nakeyi,khushi you are beautiful wallahi ina sonki banaso inga kowa tare dake sai ni don Allah try to understand me khushi I really love you darling,ta karasa maganar tana rike hannunta kamar me neman gafara,aneesa meye kukeyi hakane?idan wasa ma kikeyi ku dena wannan ba dabi'ar da musulmi bace mace ta kalli yar uwarta mace tace tana sonta....a firgice gaba dayansu suka kalli umman khushi dake tsaye bakin kofa tana kallonsu,cikin rawar murya da rashin gaskiya aneesa tace no umma ina bata wani labarine abinda ya faru nake kwatantanta mata ba wai da gaske bane,shiru umma tayi kadan tace koma menene bai kamata ba,sannan ta kalli khushi da gabanta ke dukan 100k lol tace taso inason magana dake,khushi na fita anee tayi ajiyar zuciya cike da damuwa tace tabbas lokacin da duniya zatasan irin soyayyar da nakewa khushi tayi tunda har mahaifiyarta ta gane halin da muke ciki nasan tabbas daga rana irinta yau zaa rabani da farin cikin rayuwata har abada
Thank you for reading my story!!!
Special thanks to apple,thank you dear for the amazing and suprised gift thank you once again for the love and support
Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro