Chapter 7
Suprise chapter 👌🏻
Karar wayarta ne ya sanya maimoon ajiye samosa din da takeci ta dauko tissue ta goge hannunta ganin sunan maryam ya sanyata murmushi tace heyyy idiot!naji dadin ganin kiranki maryam ina kika shigene?
An gaisheda female bodyguard,a girl with tons of confidence maryam ta karasa magana tana dariya
Goddess you are so boring maryam,kinsan Allah daga yau na dena yiwa iqbaal komai gaba daya bashi da hankali i dont know how to explain his madness he is the worst person that i ever meet,kar kiso kiga yanda jiya yayi min a office saboda kawai an rubuta masa sunana jikin rigar sa ya mareni gaban mutane kar kiso kiga irin zaginda yake min maryam i have already hate him
Murmushi maryam tayi tace nasani Maimoon iqbaal yana da matukar zafi amma karki manta da alkawarin da kika daukarwa kanki saboda farantawa mahaifin iqbaal akan abinda yayi.....sorry maryam ana knocking door anjima zan kiraki tana fadan haka ta kashe waya ta juya don sake jin karar knocking din yayi yawa
Da sauri ta sanya hijab dinta cikin muryarta mai sanyin gaske tace waye?
Shiru babu wanda ya amsa mata sai cigaba da buga kofar akeyi kamar za'a ballashi,gabantane ya fadi tayi saurin sanya hannu ta murda kofan ta budeshi,zaro kyawawan idonta tayi ganin iqbaal tsaye fuskarsa yayi ja saboda tsananin bacin rai
Meyasa kike tambayar waye yake knocking bayan kinsan nan ba gidanku bane?ko kin manta masu gidan zasu iya shiga duk inda sukeso kuma a lokacin da suka ga dama?ya karasa magana yana zama a kujerar dake gefen dakin
Murmushi tayi tace hakane nan ba gidanmu bane gidanku ne kuma kana da damar da zaka shiga ko ina sedai baka da damar da zaka cimin mutunci ko cin fuska saboda nayi resigning din yarjejeniyar da nayi ta yi maka aiki,saboda haka baka da ikon da zaka tsaya gabana kana fadamin maganar banza saboda yanzu bani da wata alaka tsakanina dakai kuma zan bar cikin gidannan gobe insha Allah maimoon ta karasa magana cike da rainin hankali tana kallonsa a wulakance
Shima murmushin yayi yace hakane dole kiyi resigning saboda kin samu cikar burinki right?abinda ya kawoki gidan kin samu dole kuma ki barshi wai ma in tambayeki shin munin fuskarki ne yayi miki yawa har kika kasa samun wani namiji da yake da interest akanki har kika zabi ki aureni saboda talauci ya isheki da iyayenki wanda suka kasa rikeki har sai kinzo gidan mutane kin zauna?toh ina tabbatar miki cewar idan har baki janye muradinki na aurenaba wallahi tallahi i promise to make your life worst and i will try my best to make your life hotter than hell
Cikin mamaki maimoon ke kallon iqbaal wanda ta kasa gane inda zancensa ya dosa,shin har yanzu yana yin magana ne akan abinda ya faru a office jiya har yake tunanin tayi hakane saboda ta aureshi ko kuma wani abune daban?bata karasa tunaniba taji karar rufe kofar iqbaal da karfin gaske,itama tsaki tayi tace koma dai me zakayi sedai kayi amma aiko ne na dena,cigaba da cin samosa tayi duk da zuciyarta sam babu dadi,karar wani knocking din taji cike da damuwa tace ya rabb who's this again?
Waye?ta sake fada muryarta kasa kasa
Husna ce ta turo dakin ta shigo fuskarta babu wani yabo ba fallasa tace maimoon kije dad yana kiranki bata jira ta bata amsaba ta fita daga dakin
Gabantane ya fadi a hankali tace dad?meyasa dad yake kirana?hmmm nasan sharrin iqbaal ne kawai akan na dena masa aiki kuma ko me zeyi sedai yayi amma bazan cigaba da aikin wahala ba,hijab dinta ta sake sanyawa ta zira slippers dinta ta fita daga dakin jikinta babu wani kwari
Tsugunawa tayi har kasa ta gaisheda dad,zaune yake yana kallon labarai kallonta yayi cikeda tausayi yace lafiya lau maimuna,shirune ya shiga tsakaninsu kadan kafin dad ya fada wa maimoon muradinsa na auren iqbaal
Innalillahi wa inna ilaihir rajiun shine kalmar da maimoon ke nanatawa a cikin zuciyarta,ya Allah kar ka sanya abinda nakeji ya zama gaskiya Allah ka tasheni daga mafarkin da nakeyi shine abinda maimoon keta maimaitawa a zuciyarta
Nasan zakiyi mamaki maimoon kamar yanda kike yarinya mai tarbiya wacce take farin ciki da duk muradina a gareki inaso wannan karon ma ki karbi tayin auren iqbaal ki sanya a ranki cewar jihadine zaki yishi babba a rayuwarki dad ya fada a takaice
Shiru ta sakeyi inda ta hadiye yawun da yake kamar wuta cikin bakinta
Shirun da kikayi ya tabbatar min da kin amince da magana ta maimoon Allah ya shi albarka ya fada zuciyarsa cike da farin ciki
Mikewa tayi tsaye duk da irin jirin da ke dibarta ta nufi hanyar fita,da kyar ta kai kanta dakinta cikin tashin hankali ta fada gado taci gaba da ambaton Innalillahi wa Innalillahi rajiun,arranged marriage again?ya Allah ka takaitamin kaddara da jarabtar rayuwata haka tunda na taso ban taba jin dadin rayuwataba bansan meye dadin duniyaba ya Allah ka duba lamarin marainiyar Allah ka sassautamin rayuwata shine abinda maimoon taci gaba da fada tana kuka
Cikin rashin kuzari ta dauke daddumar data iddar da sallah ta kwanta kan gado,juyi take yi sam ta kasa bacci wayarta ta dauko ta kunna mobile data dinta sannan ta shiga Twitter saboda shine best social media app dinta apart from Instagram "Suna chan sunata shirin valentines mu kuma muna nan muna ta salatin annabi"shine post din da taga "arewatwittersavages" sunyi,duk da tana matukar enjoying page din nasu amma wannan karon sam ta kasa ko da yin murmushi balle dariya,fita tayi ta koma whatsapp messenger inda taci karo na message din maryam
Maryam:Yo stupid darling
Maimoon:(crying emoji)😭
Maryam:mumu what again😂
Maimoon:maryam i am lost wlh don Allah gobe kizo ina cikin damuwa sunason shirya mana arranged marriage da wannan banzan mutumin
Tana gama tura mata message din ta kashe data dinta ta jefar da wayarta gefe gaba daya komai baya yi mata dadi sam
A dole iqbaal ya sauko don cin abinci duk da ba wani yunwa yake ji ba,tura pancake din kawai yake yi ba don yana jin dadinsa ba sai don gudun surutun dad yanzu sai yace baya cin abincin
Yaya iqbaal congratulations kwananan zamusha biki ashe da maimoon gaskiya abin yayi kyau sosai balkissa ta fada tana kallon iqbaal
Ai wlhi dama bikin yaya iqbaal kawai nake jira don ni dakaina zan fitar da ashobe kuma ina tabbatar muku takalmin gold yaya iqbaal ze sanya ranar aurensa walida ta karasa magana cikin farin ciki
Tamkar ba da iqbaal suke magana ba haka ya mike ya bar gurin fuskarsa babu alamar dariya,muryan dad yaji yace nan da 30 minutes ka sameni a daki
Amma dai Alhaji idan anyi auren nan a gidan nan su iqbaal din zasu zauna ko?saboda naga akwai isashen guri zai ishesu suyi rayuwarsu hajiya labiba ta fada tana satar kallon dad
Shiru yayi kadan yace ba damuwa duk abinda iqbaal ya yanke shine daidai saboda shi zeyi aure ba niba dad ya fada a takaice
Eh amma dai idan ka bashi umarni ai zeji tunda naga mansion dinnan yana da girma sosai kuma ya kamata ace iqbaal yana kusa dakai yana kula da lafiyarka ko?
Murmushi yayi yace tsawon shekarun dana dauka babu iqbaal waye yake kula dani?ina ganin wannan mansion din nawa na billionaires street zan bawa iqbaal ya zauna saboda gidan ya dace dasu
Zaro ido haj labiba tayi ta tuno irin kyau da tsaruwar mansion din wanda kudinsa yakai $700 million (seven hundred million dollars)ace shi zaa dauka a bawa iqbaal?wani irin takaici taji tare da bakin cikin rashin haihuwa da tayi da Alhaji sayeed
Kuka takeyi mai tsananin gaske sanda maimoon ke hada kayanta don komawa gidan aunty jalila,wannan wanne irin rayuwa ne haka duk wanda ta fadawa matsalarta sedai ya bata shawarar cewar tayi hakuri ta auri iqbaal.....gaskiya bazai yiwuba hakan bazai taba yiwuwa ba ta fada tana girgiza kai
"Maimoon you have to be strong,kamar yanda bakyason iqbaal shima haka baya sonki meyasa zaki damu kanki dayawa?ki tuna wannan alfarma ce zaki yiwa mutanen da suka ceto rayuwarki watakila da yanzu bakya raye a duniya,be confident maimoon ki sanyawa ranki "nothing is impossible"komai zai tafi daidai idan har kinyi believing haka zakiyi wannan abinne a matsayin ibada be strong maimoon kuma ki zama mai rike sirrinki karki kuskura ki nunawa duniya cewar bakyason iqbaal ko kuma shi bayasonki"sakon maryam ne maimoon take ta karantawa tabbas duk abinda maryam ta fada gaskiyane kuma insha Allah zatayi amfani da shawarar
Oyoyo maimoon gaskiya baki da kirki shikenan kuma an dena ganinki ko to koma dai meye yanzu ai nice zanyi komai na shaanin bikinki Allah dai ya bada zaman lafiya aunty falila ta fada cikin tsokana
Murmushi maimoon tayi tace haba aunty falila da bakinki ai ban isa na gujekiba wlh abubuwane dayawa suka sha kaina shiyasa amma ayi min afuwa bazan sakeba kuma ai yanzu kin dinga ganina kenan ko yaushe
Ba wani nan maimoon ai yanzu kuma kina yin auren nan ina jin ganinki sai shekara shekara saboda duk namijin daya samu kyakkyawar mace kamarki ga nutsuwa ga kamun kai toh gaskiya banga abinda zesa ya dinga barinki fita ba nasan kullum kuna manne da juna Musamman yanda nake ji ana fadar angon naki ya hadu sosai kedai kawai kiyiwa Allah godiya maimoon aunty falila ta karasa magana tana kallon maimoon
Ya rabb wannan mata kina da surutu dayawa maimoon ta fada a zuciyarta amma a zahiri murmushi tayi tace nagode aunty falila
Yawwa yanzu dai sai ki nuna min hoton sirikin nawa idan kuma anyi pre-wedding pictures a nuna min don nasan hotuna kam baa magana aunty falila ta fada cike da zumudi
Gaban maimoon ne ya fadi hoto kuma?ita kam ina zata sami hoton iqbaal?babban abin kunyane kuma da zargi idan tace bata da picture din wanda zata aura this is impossible,tuni gumi ya fara karyo mata da sauri ta dauko wayarta ta shiga Instagram tayi searching "iqbaalsayeed" tuni profile din iqbaal ya bayyana ajiyar zuciya tayi tace Alhamdulillah sannan ta shiga don ganin picture din da zata nunawa aunty falila,gaba daya hotunan anyi sune kusa da bar harda wanda yake yana shan giya sannan sauran duk tare da mata yake fararen fata wasu a beach wasu a club
Saurin fita tayi daga Instagram sannan ta kashe data dinta zuciyarta na bugawa da sauri tana addua kar Allah yasa aunty falila ta hango hotunan,murmushi maimoon tayi tace gaskiya ina matukar son angona kuma yana da tsada sosai saboda haka bazan baki hotonsa ba har se kinyi min kyauta idan tayimin sena nuna miki
Vote
Share
Comment
Heroine 🦋
Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro