Chapter 5
A gajiye maimoon ta karasa dakinta don sam yau ranar da alama babu sa'a ranta a matukar bace ta zauna a kan gado sai a lokacin ta tuna rabonta da abinci tun da safe shima tea kawai tasha da biscuit,tsaki tayi ta mike ta nufi inda fridge yake ta dauko sandwich da juice ta zauna bakin gado tanaci,sosai Maimoon ke tura abincin bakinta kamar wacce ta shekara bata ci abinciba saboda yunwa,wasu zafafan hawayene suka zubo a idonta cikin kuka tace i miss you mom...i will keep missing you forever
Towel ne hannunsa peach colour yana goge gashinsa wanda ya jike da ruwa saboda wankeshin da akayi,wayarsa ya dauka akan gado sannan ya fara kiran mom bata jima ba fuskar mom ta bayyana jikin screen din wayarsa it was a video call,cike da zumudi mom tace nayi fushi tun dazu nake expecting din wayarka amma shiru sai yanzu
Dariya yayi yace i am so sorry honey ayyuka sosai suka rikeni amma naso kiranki dazu saboda kiga irin tarin gifts din dana samu mom gaskiya MLDJC ba karamin company bane mom yana da matukar kyau da tsaruwa kinsan meye mom?
Dariya tayi tace a'a sai ka fada
Mom kar kiso kiga yanda naji tsoro lokacin da zanyi signing sai naji kamar bazan iyaba mom
Murmushi ta sakeyi tace zaka iya iqbaal just be yourself i trust you nasan zaka iya rike duk wani dukiya na mahaifinka kuma ina ci gaba dayi maka addua sosai
Really mom ya karasa magana yana mata wink
Niko ina maimoon?dafatan tana yi maka aiki yanda ya kamata mom ta fada cike da jiran amsa
Mom "that girl is a bitch " sam bata jin magana amma i will teach her a lesson soon ya karasa magana ransa a hade
Itama mom hade ranta tayi tace iqbaal karka cutar da maimoon na yaba da hankalinta kuma na tabbata komai maimoon zata fada maka zatayi haka ne saboda gyara
Oh that's cool,kina nufin ni har yanzu sai an yimin gyara ko?you are praising a bitch ni kuma kina nunawa banida hankali right?be jira mom tayi magana ba yayi disconnecting call din sannan ya jefar da wayar akan gado yace "what the fuck"
Da sauri maimoon ta mike tsaye bayan ta gama amsa wayar dad wanda ya bata sako ta sanar da iqbaal gobe suna da baqi a office,mayafi ta daura a kanta da kyar take iya daga kafarta saboda gajiyar da tayi,knocking din door ta fara yi bata dade tana kwankwasa kofar ba yace "come in"
Tura kofar tayi ta shiga zaune ta tarar dashi akan couch kwalaben wine da vodkas ne jere gabansa saurin dauke kanta tayi a zuciyarta tace tir da rayuwarka iqbaal
Dago kansa yayi ya kalleta a hankali yace you?
Daga kanta tayi cikin ladabi tace yes dama dad ne yace in fada maka gobe by 9am CEO din MNP enterprises ze kawo wa company dinka ziyara ta karasa magana gabanta naci gaba da faduwa
Okay...ya fada ba tare da ya dago ya kalletaba
Goodnight ta fada a hankali sannan ta juya zata fita daga dakin,murda kofar taci gaba dayi amma taqi buduwa da alama anyi locking din kofar ne da key,gabantane ya sake faduwa cike da tsoro ta juyo ta kalli iqbaal da ya bawa glass cup din hannunsa mahimmanci yana shan abinda yake ciki tace kofar ya kulle ka budemin please
Murmushi yayi yace i know
Gyara tsayuwarta tayi tunaninta yanzu iqbaal ze bude mata kofar ko kuma ya bata key din ta bude amma sai taga sam bashi da niyyar haka sai gyara zamansa da yayi
Kamar zatayi kuka ta sake cewa sauri nakeyi please inaso na kwanta da wuri saboda gobe na tashi d wuri
Murmushi ya sakeyi yace i know amma ki samu guri ki zauna
Jikinta sanyaye ta zauna a daya daga cikin kujerun da aka sanya saboda kawata parlour din kuma sunyi matukar dacewa da gurin,idonta ta sauke akan iqbaal shima kallonta yayi a hankali ya cije lips dinsa yace kayan da kika sa dazu daga yau inaso ya zama uniform dinki irinsu zaki dinga sakawa a duk lokacin da zamu fita ya fada yana zubawa wine din nashi refills yana sake zukar cigarette
Daga mishi kai tayi tace okay ammm amma kasan smoking is injurious to health ta karasa magana tana kallon hayakin da yake fitarwa a bakinsa da hancinsa
Murmushi yayi bayan ya daga kwalbar vodka ya nuna mata daidai saitin da aka rubuta smoking is injurious to health a jikin kwalbar yace i know
Shiru tayi tace okay
Bai sake cewa komai ba ya sanya remote ya bude mata kofa,kamar wacce take akan kaya haka ta mike tsaye ta fita da sauri har tana cin tuntube,dariya yayi a hankali yace "miss world peace"
Yau da wuri iqbaal ya tashi,bangaren dad dinsa ya wuce bayan sun gaisane Alhaji sayeed yake sake yiwa iqbaal bayanin duk wasu sirrika da sauran companies din da ze dinga kula dasu,be wani jima wajen dad ba ya fito,yau ma iqbaal ya riga maimoon karasawa gaban mota
How dare her?Ya fada a fusace
Yau ma da sauri ta karaso gurin har tana shirin faduwa ganin iqbaal tsaye yana jiranta cikin muryarta me sanyi tace i am sorry please jiya mura ya kamani sai nasha maganin mura kafin na kwanta ya sani bacci sosai shiyasa ban tashi da wuriba i am so sorry
Who the hell do you think you are?i am your boss you know it right?wait wai ma what's your education level ne?
Muryarta na rawa tace degree holder
Oh you are a degree holder amma kwata kwata bakisan tsarin aiki da dokar saba,kina yin abu kamar wata jahila wacce batasan komaiba,rayuwarki tafi kala da yan talla sam baki dace da aikin da kika daukarwa kankiba and this is the last warning duk ranar dana rigaki zuwa gurin nan ki sanyawa ranki cewar kin gama aiki a gidan nan
Shiru tayi gaba daya kanta sarawa yakeyi sam iqbaal besan darajar dan adam ba bata karasa tunaniba iqbaal ya shige mota da sauri itama ta shiga cike da bacin rai
"Wai Alhaji tunda yaron nan ya dawo banji kace wani abu ba akansa naga tun kafin ya dawo kake shirya plans kala kala amma ya dawo har jiya an fara mallaka masa dukiyar Alhaji sayeed banji kace wani abuba adda fatu ta karasa magana tana kallon mijin nata
Murmushi yayi yace me kikeci na baka na zuba ba dai yanzu an danqa masa dukiyar tashi ba toh zanga ta yanda ze riketa wai ma banda lalacewa irinta yaya sayeed gani a matsayin dan uwansa uwa daya uba daya amma ko sau daya be taba tunanin ya sanyani cikin dukiyarsa ba amma ya dauki komai nasa ya bawa yaro karami marar tarbiya ai wallahi nayi alkawarin kamar yanda na lalata rayuwar yaya sayeed shima iqbaal kwanannan ze gaji mahaifinsa don a wheel chair zasu kare rayuwarsu dukansu
Bushewa adda fatu tayi da dariya tace haka nakeso me gidana rabin raina ni kaina na kagu inga ina wasa da mahaukatan kudade nifa banki a kashesu ba wlh saboda idan suka mutu komai za,a baka a hannunka a matsayinka na kanin mahaifinsa
Fatu kenan ai basai an kashe mutum ba ake samun lafiya yanzu bakiga shi yaya sayeed dinba lokaci daya nasa akayi masa muguwar allura aka kashe masa gaba daya jikinsa dole ya ajiye aikinsa na komai ya rungumi wheel chair yake zaune toh shi abinda zanyi wa iqbaal se yafi na yaya ya karasa magana yana sanya takalminsa covered shoe
Ayiririri cike da farin ciki tayi guda tace Allah ya ida nufi Allah ya dafa maka mai gida ai insha Allah sai sun zama abin tausayi
Dariya suke yi kamar ransu ze fita,balkissa ce ta kalli walida tace kai walida wlh cikina kamar zeyi ciwo saboda dariya nasan yanzu ana chan wasa ya fara kyau
Dariya balkissa tayi tace ai zataci kaniyanta ba ita bodyguard ba mai kare lafiyarsa ko to zata kare lafiyarsa yau da kyau kuwa,cigaba sukayi da dariya kamar wasu mahaukata
Ba tare da ya kalli maimoon ba yace my suit
Okay tace da sauri ta fita daga office din ta nufi mota ta manta bata dauko mishi suit dinba a mota daya cire dazu a hanya,bata dadeba ta dauko rigar ta dawo hannunta rike da suit dinsa ta mika masa,karba yayi yasa sannan ya dauki wayarsa ya kalli maimoon yace let's go
Babban conference hall din da ake meeting suka karasa tuni iqbaal ya fara gaisawa da manya manyan baqin da suka kawo wa company dinsu ziyara wanda yawancinsu multi billionaires ne,sedai abin mamaki kowa sai kallon iqbaal yakeyi kamar wani mahaukaci idan suka karanta rubutun da akayi jikin takarda aka liqa jikin rigar iqbaal,kamal zolla CEO din tahar investments ne ya kalli iqbaal cike da mamaki yace what's going on here sir?Yana cigaba da taba takardar jikin rigar iqbaal wanda mutane dayawa suka gani sedai tsoro da kunya ya hanasu magana
Cike da mamaki iqbaal yayi saurin duba gaban rigarsa,tabbas takardace an rubuta "I LOVE YOU MAIMOON" cikin tsananin mamaki iqbaal yake cigaba da kallon takardar da sauri ya cire takardar daga jikinsa a fusace ya juya ya kallo maimoon ya sauke mata mari har guda 2 a cheecks dinta
A firgice cike da tashin hankali ta dafe kumatunta tsoro da tsananin faduwar gaba suka hanata cewa komai sai kallon iqbaal da take yi inda sauran mutane sama da dari suka mayarda hankalinsu wajen kallonsu iqbaal
What an embarrassment!Who do you think you are?are you out of your sense?Saboda baki da hankali da tunani har zaki dauki paper kiyi min irin wannan shit din ki sanyamin jikin kayana,look i dont love you and i will never love you bitch stupid brat you are nothing but a guard to me....yana gama fadar haka ya jefa mata takardar jikinta ya fita daga conference hall din ransa a matukar bace
Kallon da mutanen gurin ke mata ya sanyata mutuwar tsaye duk da batasan menene ya faruba amma ji takeyi kamar ta nutse kasa saboda kunya,takardar dake kasa ta dauka ta karanta cike da mamaki ta bude baki tace what?waye yayi min wannan abun?
Kuna karanta book amma bakwa comment,meyasa please?thank you for your votes amma comment shine abinda yake karamin confidence din rubutu,silent readers show yourselves please i know you love me😉wink wink don Allah ku dinga comment
Vote
Share
Comment
Heroine 🦋
Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro