Chào các bạn! Vì nhiều lý do từ nay Truyen2U chính thức đổi tên là Truyen247.Pro. Mong các bạn tiếp tục ủng hộ truy cập tên miền mới này nhé! Mãi yêu... ♥

Chapter 22

"Yau kam da wuri moon ta tashi tanaso taje gidan aunty falila don tunda ta samu labarin auren Iqbaal hankalinta yake a matukar tashe sam ta rasa menene yake yi mata dadi sedai tunaninta shin wanene zata fadawa matsalarta?banda maryam babu wanda yasan labarin cewar auren Iqbaal da moon ba don soyayya aka ginashi ba hatta aunty falila batasan cewar Iqbaal baya son moon ba,ko breakfast batayi ba ganin duk saurin shirin da takeyi har 11 yayi bata fita daga gidan ba.....cikin sanyin jiki moon ta tura kofar dakin ta shiga kamar yanda tayi tunanin ganinsa kwance yake akan gadonsa yanata bacci da alama jiya bai kwanta da wuri ba shiyasa har yanzu yake ta bacci

"Tsaki tayi ta juya ta fita daga dakin ta koma bedroom dinta,handbag dinta ta dauka da phone dinta ta nufi parking lot din gidan,da gudu driver ya karaso ya budewa moon mota cikin girmamawa ta shiga shima ya shiga motar har sai da suka fita daga gate din tukunna ya kalleta yace hajiya ina zamuje?

"Muryarta kasa-kasa tace gwarinpa,basu jima suna tafiya ba suka karasa gidan aunty falila,jikinta sanyaye ta shiga cikin gidan inda gabanta ke matsanancin faduwa,shin da wanne idon ma zata kalli aunty falila har tayi mata wani bayanin cewar Iqbaal ze kara aure?daga yin aurensu duka duka ba'a wuce 3 months ba

"Runtse idonta tayi ta shiga palour din cikin sallama,da sauri aunty falila ta taso tana mamakin ganin moon...moon kece haka zuwa babu sanarwa gaskiya naji dadin ganinki aunty falila ta fada tana karbar handbag din hannun moon

"Haba Aunty falila mutum don zezo gidansu har seya wani sanar ai dama cewa nayi suprise zan baki moon ta karasa magana tana zama a daya daga cikin couches din dake jere a palour din

"Tohm indai hakane kuwa kinyi nasara don gaskiya you really suprised me,dafatan komai lafiya ya Iqbaal din dafatan shima yana lafiya?

"Turo baki tayi kadan tace lafiya lau Aunty falila komai lafiya lau

"Tohm ya kuma baby na?aunty falila ta karasa magana tana kallon cikin moon

"Cikin kunya moon ta harari Aunty falila tace uhmm Aunty nifa ko breakfast banyi ba daga zuwa na zaki fara yimin questions kamar yar jarida....Allah yasa dai yau ma akwai sauran gurasa dinnan irin wacce kika taba yimin irinta ko?

"Dariya Aunty falila tayi tace kedai moon bansan sanda zaki dena shegen kwadayin nan ba indai harkar yaji ce kedai kinaso,kamar kinsan da safen nan aka kawomin gurasa bari in tashi in hada miki tunda kince ko breakfast bakiyi ba kuma na fada miki ba'aso mai ciki ta dinga zama da yunwa ko,bata jira amsar da moon zata bata ba ta mike ta nufi kitchen

"Sosai moon taci abinci dayawa don bata yi tunanin ma zata ci abinci dayawa kamar haka ba,jikinta a matukar sanyaye ta ajiye wayar da ke hannunta a gefe sannan ta kalli aunty falila wacce ta mayar da hankalinta tana kallon tv show tace aunty,cikin kulawa aunty falila ta dago ta kalli moon tace kai moon ba dai har kin cinye abincin ba?

"Murmushi moon tayi tace eh mana kinsan ai inason gurasa sosai yanzun ma idan na tashi tafiya sai kin zubamin wata a food warmer na tafi da ita,a tare sukayi dariya sannan shiru ya shiga tsakaninsu kadan kafin maimoon ta sake kiran sunan aunty falila a karo na biyu

"Juyawa tayi ta mayar da hankalinta wajen moon tace inajinki menene wai?

"Aunty dama Iqbaal ne ze sake aure nan da 2 weeks moon ta karasa magana cikin tsananin takaici da jin kunya

"What?aure kuma?shine abinda aunty falila ta fada da sauri cikin tsoro tace kinga banason shashancin banza da wofi wannan wanne irin banzan wasa ne haka ko an fada miki ana wasa da irin wannan abin?aunty falila tayi magana a fusace

"Murmushi moon tayi tace wallahi aunty ba wasa nakeyi miki ba da gaske nakeyi aure ze kara nan da 2 weeks don shekaran jiya ma aka kai lefe gidansu yarinyar akayi fixing date,cikin wani kalar mamakin auntie falila ta zubawa moon ido tana kallo ba tare da ta iya furta komai ba saboda yanayin nauyin da bakinta yayi mata,sai a lokacin ne take son fuskantar wani abu ta bangaren moon sedai ta tabbata lokaci ya qure mata,da kyar ta hadiye yawun da ke bakinta tace maimoon

"Cikin murmushi moon tace na'am aunty

"Shin kinason mijinki kuwa?

"Da kyar moon tayi kokarin kawar da damuwar da ke face dinta tace ina sonshibmana aunty me kika gani?

"How can he do this shit to us?duka duka auren naku yaushe akayi banda ma aure ne na masu wayewa da boko taya zaa ce har zaa miki kishiya ki kalla ajiyar da yayi miki a cikinki amma duk da haka har kallo kike akan iqbaal beyi miki lefi ba?auntie falila ta karasa magana tana kallon maimoon da tuni ta rasa ma kalar amsar da zata bata

"Shiru ta sake yi kadan tace aunt i have no idea amma nafi tunanin arranging marriage ake shirin yi masa don gani nake iqbaal bashi da wani interest akan auren nan don har yanzu da bakinsa bai fadamin cewar he's getting married ba har yanzu

"And then so what?iqbaal ba yaro bane karami maimoon and maza duk halinsu dayane babu zancen ra,ayi ko wani shiri idan har iqbaal ya yarda zai kara aure to maganar wani amincewa da zancen komai ya kare saboda haka yanzu kinga dare yayi ga kuma yanayin jikinki kije gobe insha Allah zan shigo gidan naki da wuri sai mu karasa magana insha Allah zanyi duk binciken da zanyi kafin wayewar gari zan duba inga abinda ya dace insha Allah komai zezo mana cikin sauki sannan inaso yanzun ki turamin handle din yarinyar da zai aura ko picture dinta zanyi bincike da kaina daren yau insha Allah

"Shiru maimoon tayi kadan tace okay Auntie insha Allah i will send you everything as soon as possible,bata karasa magana ba wayar ta ya fara kara da alama someone is calling her cikin sauri ta duba screen din wayarta inda gabanta yayi mugun faduwa.....it was iqbaal.,,why iqbaal?menene kuma?auntie falila ce ta kai idonta kan wayar ganin maimoon bata da niyyar daukan wayar tace ki dauka mana ba mijinki bane?

"Jikinta babu wani kwari tayi saurin picking call din ganin yana shirin katsewa tace hey

"Driver is waiting for you shine abinda iqbaal ya fada a takaice ba tare da ya sake cewa komai ba ya kashe wayanshi....jikinta sanyaye tace driver?

Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro