Chapter 2
"Maimoon"pick my phone please mom ta fada tana sake sanya waya a kunnenta,cikin sauri maimoon ta daga wayan cike da farin ciki tace hey second mom i am so sorry ina sport field kika kirani mom ya london?
Lfy lau maimoon ya nigeria?
So boring mom insha Allah idan na samu hutu a office zan kawo muku ziyara
Wow really maimoon i will be happy zanji dadi sosai maimoon
Thank you mom maimoon ta fada cikin ladabi
Ammm maimoon kina jina?mom ta fada bayan shiru daya shiga tsakaninsu
Yes mom ina jinki
Great!maimoon gobe Mr london ze dawo nigeria saboda dad dinsa ya takura sai ya dawo wajensa please inaso zaki min wani taimakone maimoon mom ta fada jikinta sanyaye
Wow Mr london ze dawo nigeria gobe?what a suprise mom gaskiya naji dadi sosai amma wanne irin taimako zanyi miki mom?maimoon ta fada a takaice
Maimoon iqbaal ba kamar sauran mutanen da kika sani bane iqbaal ya fita daban saboda gaba daya rayuwarsa ta mutanen london yake yi sam iqbaal besan wani abu waishi damuwa ba kuma be yarda da kalmar enemy ba balle har ya yarda cewar akwai makiya a duniya maimoon basai na bata bakina ba kinsan gidan Alhaji sayeed sosai sannan kinsan kalar rayuwar da akeyi kowa burinsa ya debi dukiya shiyasa suka tsani iqbaal saboda shine mallakin duk wani abu na Alhaji sayeed...a takaice maimoon inaso ki bawa iqbaal tsaro da kulawa a rayuwarsa ta nigeria
Cike da zumudi maimoon tace second mom wannan ai is not a big deal kinfi kowa sanin daddy na shine major general idan bodyguards dari kikeso toh shirye nake zan bayar saboda su kula da rayuwar Mr london
Shiru mom tayi sannan tace maimoon iqbaal yana da guards masu kula dashi baya bukatar karin wasu ke kadai nakeso ki zama mai kula da rayuwarsa ta musamman inaso ki zama kece bodyguard din iqbaal
A tsorace maimoon tace bodyguard?female bodyguard?how?mom kina ganin zan iya?kuma meyasa kika zabeni matsayin mace ace na zama bodyguard din iqbaal
Dariya mom tayi tace zaki iya maimoon saboda ke kadaice kike azabtuwa da irin kalar rayuwar da iqbaal ze shiga saboda haka na rokeki maimoon ga amanar iqbaal ...sun dade suna waya kafin maimoon ta amince da maganar mom sedai babu yanda zatayi saboda tana matukar respecting mom sosai
Bayan mom ta gama magana da maimoon ne tayiwa iqbaal bayanin cewar idan yaje nigeria akwai maimoon itace zatayi accompany dinsa
Airport
Cikin farin ciki iqbaal ya bude idonsa sassanyar iska ya shigeshi yace home sweet home i am so excited to meet my family,checking counter ya tsaya bayan anyi checking an miko mishi passport murmushi yayi sannan yace let me see who's here to pick me up
Cikin sauri maimoon keyin komai saboda ta tabbatar sun isa airport kafin iqbaal ya karaso,guards 2 sai ita suka tafi airport dauko iqbaal duk da ita kadai ta shiga sauran guards din a parking lot ta barsu su jirasu anan
Oh my god!what a beautiful iqbaal ya fada bayan ya sauke idonsa akan maimoon
Tsaki tayi tace omg na manta board din a mota kuma bansan ya kamanninsa suke ba taya zan ganeshi oh shit ta fada bayan ta dora hannunta akanta
Ammm excuse me please,actually i am lost can i have some directions?ya fada idonsa cikin nata
Kallonsa takeyi tana sake kallon irin kyan da Allah yayi masa cike da mamaki tace directions?i mean directions to where?
Wink yayi da idonsa yace directions to your heart
Damn stupidity ta fada a ranta sedai a zahiri kallonsa tayi bayan ta daure fuska tace sorry i am not here to make some fun nazo daukan boss dinane daga tafiya,tana gama fadan haka ta juya ta fita don dauko board dinda ta manta a mota wanda yake rubuce da sunan iqbaal saboda bata taba ganin iqbaal ba balle tasan ya kamaninsa suke,bata dade ba ta dawo hannunta rike da board wanda aka rubuta "Mr London" jiki
Cike da mamaki yake sake kallon board din dake hannun maimoon kenan wannan yarinyar da tayi disgracing dinsa yanzu itace yarinyar da aka aiko ta daukeshi?who is she and how dare her? Shine abinda iqbaal ya fada cike da murmushin mugunta yace that's good "miss 9ja" i will definitely mess up with you
Cigaba da daga board din tayi inda zuciyarta take tunanin ya kamanin iqbaal yake
Murmushi yayi wanda ya bawa kyawunsa sake fitowa sosai sannan ya karaso inda maimoon take tsaye yace hey i am iqbaal sayeed and why are you fucking holding a board with my name written?
Cikin tsananin mamaki ta zaro ido muryarta na rawa tace ohh sorry sir you are highly welcome
Kallonta yayi a wulakance sannan ya janyo travelling bag dinsa ya ajiye a gabanta yace first of all who are you?sannan meyasa zaa turomin mace tazo ta daukeni instead of guards what's the meaning of this shit ya karasa magana ransa a bace
Aaahhh i am also your guard sir ta fada a tsorace
Female bodyguard heck no way ya fada yana dariya cike da rainin hankali
Ji tayi ranta ya fara baci ganin yanda iqbaal ya mayar da ita kamar mahaukaciya tsaye yana yi mata dariya da kyar ta daga lips dinta da suka yi mata nauyi tace sir can we go please bata jira ya bata amsaba ta fara jan travelling bag dinsa shima bece komai ba ya fara bin ta a baya cike da tsananin mamaki who's she?sannan meyasa ta zabi ta zama bodyguard?sam maimoon batayi kama da mutanen da suke cikin wahala ba toh meyasa ta zabi ta zama bodyguard,da wannan kalar tunanin suka karasa mota da sauri aka budewa iqbaal mota ya shiga itama maimoon ta shiga sannan sauran bodyguards suka shiga dayan motan suka fara tafiya,sosai iqbaal ke kallon nigeria rabonsa da 9ja tun yana 4 years hakan yana nufin baze iya tuna komaiba ko kuma besan komaiba a 9ja
Tafiya kadan suka yi iqbaal ya zaro kwalin cigarette daga aljihunsa ya kunna ya fara sha cike da nishadi inda idonsa ke kallon window,da sauri maimoon ta kalli iqbaal cike da mamaki cikin takaici tace tab wannan mr london din sam besan kanshiba tun kafin aje ko ina har ya fara nuna halinsa tirr
Dukansu tsaye suke inka cire Alhaji sayeed dake zaune kan wheel chair dinsa da alama kowa ya kagu yaga iqbaal tun bayan hango parking din motansu
A hankali ya sauke kafarsa daga cikin motan ya shaqi fresh air sannan yace wow bayan ya daga kansa yana cigaba da kallon hadadden mansion din nasu,tabbas gidansu iqbaal ya tsaru fiye da imaginations,maimoon ce ta shige gaba iqbaal na biye da ita a baya har suka karasa babban main parlour din gidan da sauri iqbaal ya karasa gaban dad cike da soyayya yace hey dad i miss you so much bayan yayi hugging dinsa kamar wani karamin yaro,hangosu walida da balkissa tsaye yasa iqbaal saurin karasawa yayi hugging din walida yace hey darling sis sannan ya bata peck a cheeks daga nan ya koma yayiwa balkissa,cike da mamaki kowa ke zaro ido yana kallon iqbaal inda su walida sukayi suman tsaye,cike da tashin hankali maimoon tace ya salam mr london me yakeyi haka kuma ta fada a zuciyarta sannnan taci gaba da kallonsu hajiya laila da irin kallon tsanar da kowa keyi masa a wajen
Cike da soyayya Alhaji sayeed ya kalli maimoon yace aje a nuna masa apartment dinsa yana bukatar hutu kafin ya fito yaci abinci,murmushi tayi tace ok dad sannan ta kalli iqbaal tace let's go,kwalin cigarette dinne ya fado daga aljihun iqbaal cike da kunya maimoon ta tsuguna ta dauke cikin tsananin mamaki su hajiya laila suka rike baki cike da mamaki inda kowacce cikinsu ke girgiza kai tab lallai kowaccensu ke fada cike da murmushi hajiya laila tace barka da shigowa makabartarka iqbaal
Yana shiga dakin ya fada kan gadonsa dakin ya tsaru sosai don ko rayuwarsa a london sai wanda ya isa zaa gansa a irin dakin da aka tsara masa anan,jikin closet maimoon ta ajiye masa travelling bag dinsa sannan ta kalleshi tace am sorry sir nigeria fa ba london bace rayuwarmu da aladunmu da addinin mu is different abinda kayi yanzu a palour be daceba ba hugging dinsu ya kamata kayiba tunda cikinsu akwai wayanda ba muharramankaba zasu iya yi maka wani kallon abun daban kamata yayi ace kun fara gaisawa
Will you shut up please?who the hell do you think you are?haba miss 9ja don't you dare try to interfere yourself in my family issues tunda aka haifeni iyayena suke kashemin kudi a kalar makarantu dayawa wanda har ki mutu bazaki taba sanya kafafuwanki cikiba saboda haka karki kuskura kicemin banida tarbiya stay in your limits don't you ever cross it and finally will you get out from my room?
Tuni jikin maimoon ya fara rawa cikin tsananin tashin hankali take kallon iqbaal yanda lokaci daya yake faman masifa kamar wanda aka yiwa wani abu
Miss 9ja i said get out ya sake fada a takaice yana nuna mata hanyar fita
I'm sorry Mr london idan har wannan maganar da nayi ce ta bata maka rai kuma yanzu zan fita daga dakinka akwai number wayata jikin littafin chan duk sanda kake bukatar wani abu you can call me and i am always ready for you sir,tana gama fadan haka ta fita daga dakin zuciyarta a bace
Tare da duk mutanen gidan iqbaal yaci abinci cikin farin ciki da nishadi sam be ga alamar tsana ko wani rashin soyayya a tare dasu ba kenan mom itama bata tabbatar da abinda take fada masa ba,sai karfe 8 iqbaal ya tashi ya koma apartment dinsa yana shiga kiran wayar mom ya gani cike da kewarta ya daga wayar yace hey mom
Hey Mr london i hope you arrived safely tun dazu nake ta tunaninka ko ka sauka lafiya i have already missed you
Murmushi yayi yace i missed you too mom and we arrived safely i hope daga yau zaki dena treating dina kamar karamin yaro because i am no more a kid now ya karasa magana cikin shagwaba
Dariya tayi tace well na yarda amma idan har kanaso na dena daukanka baby boy dole sai ka kula da kanka sosai,sun dade suna hira kafin iqbaal ya ajiye waya sannan ya kalli agogo karfe 8:30pm wayarsa ya dauko ya kira maimoon cikin 5 minutes ta karaso sanye da abaya cikin ladabi tace how can i help you sir?
I need some refreshments inaso ki kaini the most biggest and expensive club da yake garin nan yanzu ya karasa magana yana mikewa tsaye
What?gabanta ne ya fadi muryarta na rawa tace club?amma ban taba zuwa club ba sir ta fada cikin tsananin rikicewa da tsoro
Murmushi yayi yace google it
Hannunta na rawa ta fara browsing a wayarta cikin 1 minute ta samu result "Millionaires paradise" shine club din da yafi kowanne kyau tsada da tsaruwa hannunta na rawa ta mikawa iqbaal wayar murmushi yayi yace wow "Millionaires paradise" what a nice name
Vote
Share
Comment
Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro