Chào các bạn! Vì nhiều lý do từ nay Truyen2U chính thức đổi tên là Truyen247.Pro. Mong các bạn tiếp tục ủng hộ truy cập tên miền mới này nhé! Mãi yêu... ♥

BIYU

*HATSABIBIYAR TAFIYA

*BIYU

*XINNIE_SMART
*===========
Har misalin karfe biyun dare suhaima bata daina kuka ba, tana zaune a cikin dakin da aka ajiye su,TANI tana tare da ita. Gaba daya cikin yanayin tashin hankali da kokarin kwantar mata da hankali kuma gashi jamil yana kwance har yanzu bai farfado ba, gaba daya cikin yanayin tashin hankali suke.
Malam mai kaji yana tsaye a cikin dakin shima yana kallonsu yanayinsa cike da alhini da kuma rashin nutsuwa, inna tana zaune dirshan a cikin dakin,  al’amarin ya kasalar da ita. Suna cikin wannan halin malam mai kaji ya sauke numfashi
“innalillahi wa inna ilaihirraji’un… wannan Kalmar ita kadai ta rage mana, itace kadai tunani yake bamu ikon sarrafata a wannan yanayin da ake ciki”
“baba kaga iftila’in daya fada mana ko?”
“Na kasa magana suhaima, bansan me zance ba, bansan da wace fuska zan kalli yaron nan ba, bansan me zamu fada masa ba, bansan me zamu kira wannan tafiya taku ba”
“Tafiyar kaddara…” inna ta fada, daga ina take zaune da take kokarin danne kukan da yake so ya cuso kansa ya fito waje.  “wannan al’amarin dole mu dora shi a mizanin kaddara.”
Tani ta sauke numfashi muryarta akwai tsoro da rawa alamun tana gab da fara kuka itama “to yanzu yaya zamu yi? Wannan abun da ya faru yaya zamu kalle shi?”
Malam mai kaji ya girgiza kai
“shine tunanin da muka kasa samu”
“malam” inji inna “kar mu kuskura mu fadawa yaron nan maganar nan, bashi bama, kar mu fadawa kowa”
malam mai kaji ya dan yi jim sannan ya kalle ta
“idan kika ce kar mu fadawa kowa, kinyi gaskiya saboda hakan ne zai rufe asirin tozarcin da suka yiwa wannan yarinyar, duk da ba a wannan kauyen zata rayu ba, amma gudun kada hakan ya hana zuri’ar ta ziyarta wannan garin dole mu rufe.. amma kamar da wuya boyewa shi yaron”
“Malam ita fa sanda naci da dagiya ke sa ta mikewa ba nuna karfi ba, mu daure mu cije mu  boye wannan al’amarin, sumar da yayi kamar taimako ne da Allah ya lamunce mana ta hanya daban”
“me kike tsoro akan hakan da bakya so a sanar dashi?” Tani ta kalli babansu a raunane
“yanzu baba sai ace masa anyiwa suhaima fyade? Yaya zaiji? Wane irin zaman aure zasu yi?”
Malam mai kaji ya ajiye zuciya da karfi, irin bashi da amsar nan.
“kawai shawarar inna zamu bi, mu boye, kamar hakan zaifi daraja martabar suhaima a wurinsa”
suhaima ta sauke numfashi sai yanzu ta dago ta kalle su duk maganganun da suke yi
“babu yadda zamu yi mu boyewa jamil wannan al’amarin da ya faru”
Tani da Inna suka kalle ta a sukwane.
“Kinsan me kike fada kuwa suhaima? Wannan wace irin dagiya ce? Ki bari ki nemi daraja da mutumcin ki da Allah ya rufe tunda wannan bakin al’amarin ya faru”
hawaye suka zo mata
“idan yanzu an boye masa ta yaya zamu fuskance shi idan ya gane? Idan mun boye masa Allah fa? Kuna ganin bamu shiga hakkinsa ba? Bamu cutar da jamil ba? Al’amarin aure lamari ne da yake bukatar gaskiya, rikon amana. Me yasa zamu boye masa abinda dole sai ya sani?”
Tani ta runtse idanu sannan ta taba ta ta matso kusa da ita
“kina ‘yar birni amma kina so ki yi halin irin mu yan karkara… ni bazan yi haka ba bai kamata kema kiyi ba… ki bari ko daga baya ne ya gane akwai nauyin rabuwa ko daukar mataki a lokacin sama da yanzu da babu wani abu tsakanin ku”
“soyayyar mu da jamil tana da tasirin da zai fahimce ni, soyayyar mu tana da ikon da zata bashi haske da fahimtar cewa ba yin kaina bane, na tabbata zuciyarsa zata kyautata min kamar yadda nayi fatan mu sanar dashi gaskiya, domin ramin karya ne ke kurewa, amma na gaskiya baya kurewa….”
Inna ta yi tsaki
“Ke kinga…!!”
malam mai kaji ya dakatar dasu.
“Ban yarda cewa Suhaima kina da hankali kuma kina amfani da ilimin ki ba sai yau, abune mai wuya wannan al’amarin bai rikita rayuwarki ba, amma gashi kin iya juriyar zabar gaskiya akan karya… wallahi Allah bazai barki a tabe ba, kuma zai shiga al’anarin ki , ku kuma da kuke zaton boyewa shine abunda ya dace kunyi kuskure.. maganarta gaskiya ce”
“yanzu ka yarda wannan yarinya ta rasa daraja, ta rasa mutumci da kima a idanun wanda zata rayu dashi?” inna ta fada cike da kokwanto da damuwa da kuma alhini. Ya girgiza kai
“yanzu fatan mu wannan yaron ya samu lafiya, ya farfado, na tabbata yadda ta bashi amana, shima haka zai bata amana, baisan anyi ba, amma zai tabbatar da saboda shi ta bada kanta, kunga kuwa shine abinda zai dogara dashi ya rama mata aniyarta, rama aniya kuma shine yi mata adalci ya amshi kaddarar abinda ya faru a matsayin kaddara.”
Tani ta sauke numfashi a tsorace
“ni dai tsoro nake ji.. nasan wannan shine abinda ya dace, amma wallahi tsoro nake ji, baba kana ganin irin yadda ka yiwa mijina gata, gona da duk abinda uba kewa yaronsa, saboda wata ya ci mutumcina, maza basu da tabbas.. bai kamata mu bashi wannan amanar ba”
“bamu da tabbas nake zaune da mahaifiyar ki, har muka same ki?”
ta dukar da kai
“kayi hakuri, baku duka nake nufi ba”
suhaima ta jefa kallonta wurin jamil da yake bacci. Bai farka ba
“fatana dai ya farfado, ya samu lafiya, mu koma gida, ina jin tsoron wani dalili yasa lafiya tayi masa gardama a dalilin wannan tafiyar”
“ina tsoron kada a birni a ji cewa shi kadai aka yiwa haka mu kuma fa”  mai kaji yayi murmushi
“Tani ai rufe mana daki suka yi, da kwado kuma wannan itace dabi’ar wadanda suka zo sata ko aikata barna iriin haka suke yi”
“haka ne, kaddara ce kawai”
Gaba daya suka koma rarrashinta. Domin sun yarda da abinda ta fada
***
Sai misalin karfe tara na safe jamil ya samu kansa, suka tabbatar da ya dawo hayyacinsa. An boye al’amarin ne saboda ana fada a kauyen kowa zai ji labarin, kuma irin wannan lamarin ana boye shine,
Jamil ya samu cikakken labari, ta hanyar mai kaji, yanzu suna zaune a tsakar gida, inda aka shimfida tabarma jamil yana zaune akai, a gefen kansa akwai bandeji da likitan kauyen yazo ya sa masa.  Mai kaji yaci gaba da Magana
“Wannan al’amari ka amshe shi yadda muka amshe shi, kamar yadda ubangiji ke cewa a cikin alqur’ani mai falala. Zamu rayu a wadanda zai rika jarrabawa da kaddara daban daban… wannan yarinya anyi kokarin a boye maka komai, amma ta takura cewa sai an sanar da kai, domin kuwa bata bukatar wata hanyar rashin gaskiya ta bullo a tsakanin ku… kaga kuwa ba wai dan ‘ya take a wurina ba, tayi namijin kokarin da ya dace a jinjina mata, a bata sunan ‘yar halak”
a sanyaye inna ta kalle shi
“dukan mu nan jikin mu a sanyaye, mun kasa yarda ko jurewa cewa zaka kalle ta da daraja shi yasa muka so boyewa ba wai da wata manufa ba”
jamil ya dago a hankali yana kallonsu, duk wadda ya hada idanu da ita sais u dukar da kai. Suhaima ma bata iya kallonsa ba.
“suhaima” ya kira sunanta, ta dago a hankali, da hawaye a fuskarta. Yayi murmushi
“Na godewa Allah daya sa kika zama kece zaki zama matata… nagode masa da ya kasance dake zan rayu, saboda tsananin gaskiyar ki dana sani wani dalili ya kasa sauya ta. Wallahi kin cika ‘yar halak!”
gaba daya suka kalle shi, suka kalli juna a rude. Tani ta matso kusa da shi
“kana nufin… wai kana nufin ka yafe?”
“to laifi tayi? Ai sai anyi laifi ake yafewa ko?”
“kuma baka ji haushin komai a rank aba?”
“naji haushi, amma ba haushin suhaima ba, haushin yan taaddan da suka yi mana illa da cin mutumcin mu”
inna ta daga hannu sama
“Alhamdulillah, lallai ka cika jarumi, ka cika masoyi na hakika”
mai kaji ya kalle shi
“Tabbas Allah ne abin godiya, saboda shine yake tsara rayuwar masu fahimta haka a tare da junansu… wannan dabi’a taka ta tabbatar min da kai sirikine na gaske, ko a tsakiyar daji da kuraye zaka iya rike mana yarinyar mu, lallai Allah shine kawai abin godiya”
jamil yayi murmushi
“yana daga cikin cikon imani  YARDA DA KADDARA.. mai kyau ko sabaninta, ya kamata na tabbata daga cikin wadanda zasu samu wannan ladan, kuma dai suhaima tayi hakanne dan kada na rasa rain a, da bata bada fansar jikinta ba, da watakila yanzu bani da rai, ko bana numfashi… wannan abu da ta nuna ma, dabi’ace ta matar kwarai, zata iya rike min sirri da rufamin asiri a kowanne yanayi ko hali. Na tabbata nayi dace”
“muma mun dace siriki. Allah ya barku tare, ya kuma kade dukkan wasu fitinun.”
Inna ta sauke numfashi da murna sosai a tare da ita
“kai ku barni nayi guda dan Allah”
ta rangada guda da karfi.
“ke baki san kin girma bane?”
“a’a malam barni na nuna murna ta ta samun yaron kirki”
***
tsuntsaye suna ta gudanar da kukansu, ruwa na wucewa da sauti mai dadi. Hasken rana ya dan rage saboda la’asar ta wuce.
Suhaima da jamil suna zaune a karkashin wata karamar itaciya da take daf da wani dutse da suke kansa, karkashin dutsen wata korama ce karama da ruwa ke wucewa cike da salo mai birgewa saboda yana zagaye wani farin karamin dutse a ciki.
Jamil ya dago ya kalli suhaima da take takure a gefe guda kusa da shi. Kanta na kasa, yayi murmushi
“me yasa kike min rowar idanun ki my one?”
suhaima ta sauke numfashi
“yaya jamil”
“na’am masoyiya ta”
“me yasa ka lamunce da yanayin da nake ciki?”
“me yasa kika sadaukar da rayuwar ki a kaina?”
ta dago ta kalle shi
“saboda idan babu kai da wa zan rayu? Ta yaya zan iya kallon duniya a matsayin wadda ta rasa ka? Menen amfani na bayan tare muka shirya zamu rayu? Menene makomata?”
ya yi murmushin jin dadi
“kalaman ki suna kama da wadda take so tace ba zata iya barina na mutu ba ko?”
“da ina da hali, mutuwa ko kusa da kai ba zata zo ba, da ina da dalilin kare ka, ko a ina yake zan je na nemo”
“ki daina damuwa kinji”
ta miko hannuwanta ta rike hannunsa, wani shauki ya shiga jikinsu, suka kalli juna, sun kai minti day aba tare da sun iya cewa komai ba, ta sauke numfashi. Sannan ta lumshe idanu
“wata rana ba zaka tuna da wannan daren ba?”
“har’abada na manta da wannan tafiyar, har abada na shaafa da wannan daren, har gaba da abada na manta da abinda ya faru.. har da’iman na manta bani bane farko a wurin ki”
kuka suka zo mata, bata iya hana daukar hannayensa ta dora a gefen fuskarta da hawaye ke zuba ba
“dan Allah wata rana kada ka tuna wannan lokacin, dan Allah koda na yi maka laifi, kada ka tuno ko kada ka furta min wannan ranar, dan Allah duk abinda ya faru tsakanin mu kada wannan ranar ta sake zo mana.
“suhaima”
“na’am yaya jamil”
“kina sona?”
“fiye da tunanin ka”
“kar ki sake min maganar”
ta kalle shi
“da gaske nake, idan baki min ba nima babu yadda zanyi na tuna”
ta lumshe idanu.. wayarsa tayi kara, ya dauka
“kazoo… gamu nan zuwa”
ya kashe ya kalli suhaima
“direba yazo… mu tashi mu tafi…”
suka mike suka tafi

*SAIDAI WANNAN TAFIYAR DA ZASU YI DAWOWA GIDA.. TA SAUYA ABUBUWA DA DAMA*

Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro