chapter 7
Hello guys,i am really sorry for this much late in update,Actually i was little bit busy in studies..but insha Allah i will try to update regularly....mark my words guys i said i will try hahaha
"Tana shiga daki ta zauna kan gado zuciyarta na bugawa da karfin gaske,da sauri ta dafe kanta ta kalli mudubin dake gefen gadon,kallon kanta take a hankali hawaye suka fara gangarowa daga idonta,ita kanta tasan tana da matukar kyau to menene aibun ta da moha yake wulakantata haka?
"Towel ta dauka ta shiga bathroom ta watsa ruwa jikinta sannan ta daura alwalar sallar magriba,tana kokarin kwanciya don tsananin ciwon da kanta yakeyi taji ana knocking kofar dakin,wani sanyi taji a ranta tasan babu wanda zai buga mata kofa a wannan lokacin sai moha don tasan daga ita sai shi a gidan...sai data sake kallon mirror tukunna ta bude dakin
"A take murmushinta ya koma fushi ganin wani bature tsaye a gabanta yana mata murmushi cike da girmamawa,da sauri ta janyo hijab tasaka sannan ta karasa fitowa tana kallonsa
"Good evening mrs moha,i am johny legend can i help you?
"Nice to meet you johny,but i dont need any help yet see you later...
"Ok maam tare da juyawa yai ficewarsa
"Tsaki tayi sannan ta dafe kanta da yake faman sarawa ta fada kan gado zuciyarta na faman jinjina cewar da gaske mijinta shine zai turo wanda zai tayata hira lallai moha sam bai damu da ita ba ya zama dole itama ta watsar da duk wata soyayyarsa da take kokarin shiga zuciyarta ba tare data shiryaba
"Yau weekend rahma bata tashi da wuriba don tsananin zazaabin data tashi dashi jikinta tamkar anyi mata dukan tsiya,ganin har 12 na rana babu wanda yasan halin da take ciki yasata mikewa da kyar ta janyo waya ta kira johny ta sanar dashi zazzabin da yake damunta...johny bai wuce 5 minutes ba ya karaso kai tsaye yake knocking kofar
"Doguwan riga abaya tasa,ta fito tana layi saurin kai hannu yayi zai tallafeta,da sauri ta dakatar dashi cike da murmushi tace thank you johny
"Moha ne ya fito sanyi cikin suit tare da kyakkyawan kamshi da yake tashi daga jikinsa,yayi kyau sosai babu marabar sa da bature,a wulakance ya kallesu daga ita har johny sannan ya maida kallonsa wajen wayar da yake dannawa
"Da sauri johny ya fita waje ya kunna mota yana jiran rahma ta fito ya kaita asibiti
"Ganin moha da gaske yake zai fita ba tare dayace mata komaiba yasa rahma kallonsa tace banida lafiya
"And then so what?ya karasa maganar a fusace kamar zai rufeta da duka
"Kasa magana tayi ta zuba mishi idanuwanta tana kallonsa cike da tsoro
"Meye kika zuba min ido kina kallo,nifa i hate this your stupid attitudes,banason munafinci irin naku na mata......wayansa ne ya fara ringing da sauri ya dauka cike da murmushina fuskarsa yace hello mom
"Sun dade suna hira da mom,fuskarsa hade ya mikawa rahma waya
"Hello rahma dafatan duk kuna lafiya
"Cike da karfin hali tace lafiya lau mom
"Ya naji muryanki haka rahma kamar kina cikin damuwa
"Hawayene suka zubo a fuskarta muryarta na rawa tace mom bani da lafiyane shiyasa
"A firgice mom tace bashi wayar
"Mika mishi wayar tayi jikinta a matukar sanyaye
"Haba mom munjeje asibiti kullum sai na kaita asibiti,yanzu haka ina fama da itane zan kaita asibiti wai ita batason allura,kuma mom jikinta duk yayi weak don haka bari yanzu zan dauketa in kaita mota we will talk later my regards to yusrah da mahmud....yana gama fadin haka ya kashe wayar sannan ya dubi rahma data zuba mishi ido cike da mamaki taji sai zubawa mom karya yakeyi
"What happened!wai ke ga munafuka zaki hadani fada da mom ko har da yin kuka kina ce mata baki da lafiya ko...i have already told you duk wani matsalanki idan ya tashi ki samu johny ki fada mishi but you refuse kullum burinki ki shiga rayuwana...
"Ai ba zaman johny nakeyi a gidan ba don haka kai zan fadawa ta karasa maganar cikin kuka
"Murmushi yayi sannan yace well......Allah ya baki sa'a yai ficewarsa
"Kifa kanta tayi a kujera tana ta kuka mai ban tausayi,johny taji yana yi mata magana,a firgice ta mike ta kalleshi
"Cikin tausayi yace sorry please ma,boss is always heartless ...kar ki damu kanki everything will be okay
"Mikewa tai har suka shiga mota bata sake cewa komaiba sai kukan da takeyi,bayan an bata magunguna da allurai suka koma gida,komawa tai ta kwanta ranta a matukar bace
"Yau kwana 3 kenan da zazzabin rahma amma tun ranar farko basu sake koda haduwa da moha ba balle har ya shigo inda take yayi mata sannu
"Karar message taji ya shigo mata,jikinta sanyaye ta bude whatsapp dun,sabuwar number ta gani ance mata "hey"
"Hello ta mayarwa da mai number din tare da scrolling ta duba sunan wanda ke magana *Mr moh* ta gani rubuce dasauri ta shiga kan display picture (DP) dinshi taga wani hotonsa zaune a office dinsa yasa suit ash colour...yayi kyau sosai a jikin hoton sedai fuskar nan tana nan babu alamar murmushi amma hakan bai hanashi yin kyau ba
"Tsaki yai mai sauti a zuciyarsa yace what am i doing,saurin yin block dinta yayi sannan ya jefar da wayar zuciyarsa na matukar jin haushin yin maganar da yayi mata
"Rahma na cikin kallon hoton cike da birgewa taga yayi blocking dinta murmushi tayi a hankali tace kuma dai but i really love you G-man (Gentleman)
"Cike da gadara yake knocking din door din daga wani bangaren kuma zuciyarsa na raya masa kamar ya koma kawai,jin bata da niyyar bude kofar yasa shi murda kofar dakin ya shiga cike da fushi,kwance ya tarar da ita ta lullube da bargo amma duk da haka rawar sanyi takeyi
"Bargon ya yaye tare da dora hannunsa akan wuyanta,zafi sosai yaji a jikinta,kallonta yaci gaba dayi na 2 minutes ta rame sosai duk da ba wani jikine da itaba amma ta rame akan yanda tazo gidan
"Juyar da kanta tai ganin yanda ya zuba mata ido yana kallo
"Cikin kaukashiyar muryarshi yace tashi mu tafi asibiti
"Girgiza kanta tayi cike da bacin rai tace thank you amma babu inda zani
"Ok kawai yace sannan yai ficewarsa ba tare daya sake cewa komaiba........
Masu yimin messages sorry please bazan iya duba messages dinkuba nan da 7 days,amma idan na gama komai duk zakuga reply dinku....love you all
*Mrs Abideen*
Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro