Chapter 15
*HALWA*
Wattpad:MaimunaAbdallah
Maman hanan
*Unedited*
Banyi edit ba idan kunga any mistake just manage it
15
"Tura kofar yayi fuskarsa babu alamar tsoro ya tsaya gabanta yana kallon yanda ta kifa kanta tana kuka
"Oh shitt ya fada a hankali a zuciyarsa yana tantamar anya rahma zata karbi zancensa kuwa,murmushi yayi har yana sake gyara tsayuwarsa ya cire hannunta daga fuskarta yaci gaba da kallonta da zafafan idanuwansa
"Ture hannunsa tayi da karfi,wani mugun ciwo yaji a zuciyarsa ganin yarinyar da bai damu da itaba balle wani nata amma har tana iya ture masa hannu,sake kama hannun nata yayi ya rike da karfin gaske,wannan karon bata ce mishi komaiba sai sunkuyar da kanta tayi kasa
"Am sorry please ya fada a hankali
"Shiru tayi zuciyarta na mugun bugawa,anya mr arrogant shine ya tsaya gabanta har yana bata hakuri
"Sake rike hannun nata yai ya sake matsowa sosai har suna iya jiyo numfashin junansu yace sorry idan har baso kike na tsuguna gabankiba you have to say something
"Saurin kallonsa tai a zuciyarta tace tsugunawa kuma?saurin girgiza mishi kai tayi tace no
"Kin hakura yace cikin muryarsa ta yaudara
"Daga kanta tai alamar eh
"Murmushi yayi sannan yace thank you ya juya kamar zai fita sai kuma ya juyo kamar wanda yayi mantuwa yace ohh sorry anjima kadan freinds dina zasuzo idan bazaki damuba zaki iya dafa musu some traditional foods koda kala 2 ne haka?
"Gabanta ne ya fadi ganin itama ba wata gwana bace gurin girki balle wani abincin gargajiya
"Ganin ta dade bata bashi amsaba yace any problem?
"No...no..no problem zanyi i will try ta fada cikin i'ina
"Murmushi yai ganin ta amince yace well akwai komai a kitchen you can manage it,idan kuma kina bukatar wani abu kiyiwa johny magana
"Daga mishi kai tayi cikin tsananin mamaki take kallonsa ashe haka yake da sakin fuska da saukin kai
"Murmushi ya sakeyi mata cikin yaudara yace thank you and finally ki shirya gobe zamu wuce 9ja our tickets is ready,yana gama fadar haka ya fice
"Yana fita ta doka tsalle hade da murna ta dauki waya ta kira anna inda ta koya mata yanda zatayi wainar shinkafa da miyar dakakkiyar kaza sai burabusko da miyan kayan ciki
"Sunzo sunci abinci kowa yanata santi hatta moha sai daya take cikinsa tsaf sannan sukayi sallama kowa ya tafi
"Tun dare rahma ta shirya komai nata don moha ya fada mata morning flight zasu bi,karfe 3 jirgin su moha ya sauka,dama driver na jiransu suna sauka suka shiga mota
"Bangaren mom dasu yusrah sun gama shirye-shiryensu an gyara komai tare da abinci kala -kala
"Driver na parking rahma ta bude kofa don jinta takeyi kamar akan dutse jinta tare da moha,tana kokarin zira kafarta waje moha ya janyo hannunta tare dasa mata wani envelope cikin murmushinsa na yaudara yace muje
"A hankali suka karasa cikin gidan sai dai lokaci zuwa lokaci zuciyarta na bugawa da kaguwar shin menene moha ya bata haka
"Suna shiga su mom suka rungumesu cike da murna da farin ciki,cikin dabara rahma ta zame jiki ta shige daki ta bude takardar daya bata
"Takardar saki ce,da sauri ta dafe kanta da yake juyawa,zuciyarta na dukan goma-goma,inda gumi ke zubowa tamkar ruwan sama,innalillahi wa inna ilaihir rajiun,Allahumma lah sahla illa maja'altahu sahla wa anta tajalul hazna iza shi'ita sahla shine addu'ar da rahma ke maimaitawa fashewa tai da kuka mai karfi ta fara bubbuga kanta jikin pillow
"Jin kuka yasa mom da yusra saurin turo kofar dakin da gudu suka karasa gabanta tare da fadin lafiya?saurin tura takardar tai karkashin pillow sannan ta fara goge hawaye tare dayin murmushi tace bakomai mom
"Mom ce tasa hannu ta janyo takardar tare da budewa,itama a firgice ta mike tsaye tace subhanallah saki kuma?
*Mrs Abideen*
Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro